Editor

9513 Posts
Ta yi garkuwa da mijinta kan rashin kwanciyar aure

Ta yi garkuwa da mijinta kan rashin kwanciyar aure

Wata matar aure da ta yi garkuwa da mijinta domin ta karɓi kuɗin fansa ta shiga hannun hukuma. Dubun matar ta cika ne bayan ta karɓi kuɗin fansa Naira miliyan biyu bayan ta yi garkuwa da mijin nata. Sai dai ta shaida wa ’yan sanda cewa, “Wanda ya yi garkuwa da shi ya karvi kuɗin fansa Naira miliyan biyu, amma bai ba ni kasona daga ciki ba, ko fasalin kuɗin ban gani ba.” Ta bayyana cewa, ta sa an yi garkuwa da shi ne saboda rashin kwanciyar aure da ita da kuma watsi da ’ya’yansu. Matar dai tana cikin mutum…
Read More
Malamin Islamiyya ya bayyana kashe iyayensa da ya yi a matsayin jihadi

Malamin Islamiyya ya bayyana kashe iyayensa da ya yi a matsayin jihadi

Wani matashi da ya rankwaɗa wa mahaifansa biyu taɓarya ya kashe su, ya yi ikirarin cewa Jihadi ne abin da ya aikata. Shi dai wannan matashi ya shaida wa ’yan sanda cewa, ya yi amfani da taɓarya wajen kashe mahaifan nasa ne saboda izgili da su ke masa idan yana yin ibada. A baya mun kawo rahoton wanann abin al’ajabi da matashin ya hallaka mahaifiyarsa Hauwa, mai shekara 60 da mahafinsa Ahmad Muhammad, mai shekara 70, wanda kuma shi ne Daggacin ƙauyen Zarada-Sabuwa a Ƙaramar Hukumar Gagarawa ta Jihar Jigawa. Bai tsaya a iya kansu ba, domin sai da ya…
Read More
Yadda ’yan bindiga suka kama ɓarawo, suka miƙa shi ga hukuma

Yadda ’yan bindiga suka kama ɓarawo, suka miƙa shi ga hukuma

Wani al'amari mai cike abin mamaki ya faru, inda wasu ’yan bindiga a Jihar Katsina suka kama wani ɗan jari-bola yana sace-sace a ƙauyen da mutanen garin suka gudu suka bari. Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake zargin, wanda matashi ne da ya ƙware wajen cire rodika da ƙarafa daga ginin mutane a wani ƙauye. Rahotannin sun rawaito cewa, ’yan bindigar sun kama matashin ne lokacin da suka fito sintiri a kan baburansu. A wani bidiyo da aka samu, an ga ’yan bindigar suna gabatar da shi tare da ƙarafan da ya sata a gaban wani shugaban al’umma na ƙauyen.…
Read More
Nancy Ajram: Sarauniyar Mawaƙan Larabawa

Nancy Ajram: Sarauniyar Mawaƙan Larabawa

Daga AISHA ASAS Kiɗa da waƙa wata daɗaɗɗiyar al'ada ce ko in ce ɗab'i da ba kasafai kake samun al'ummar da ba ta da irin nata da ta ke nishaɗanta da ita ba. Wannan ne ya sa duk inda ka ratsa za ka tarar da kiɗa da waƙa ya rigaka zuwa, sai dai ka tarar da ba irin wanda ka baro ne a inda ka fito ba. Za mu iya kiran waƙa a matsayin wasiƙu zuwa ga zukatan mutane, hakan zai sa da wahala ka rasa wadda aka yi domin taka zuciyar. Kazalika bincike ya tabbatar waƙa na kan gaba…
Read More
Yankin Zanzibar na Tanzaniya ya karrama tawagar likitocin Ƙasar Sin da lambar yabo saboda hidmar da suka bayar

Yankin Zanzibar na Tanzaniya ya karrama tawagar likitocin Ƙasar Sin da lambar yabo saboda hidmar da suka bayar

Daga CMG HAUSA Shugaban yankin Zanzibar na ƙasar Tanzania, Hussein Ali Mwinyi a ranar Asabar din da ta gabata ya karrama mambobi 21 na tawagar likitocin ƙasar Sin da lambar yabo, saboda hidimar aikin jinya da suka bayar na tsawon shekara ɗaya a tsibirin na Zanzibar. Mwinyi ya shaida wa tawagar likitocin na ƙasar Sin yayin da yake ban kwana da su a gidan gwamnatin Zanzibar cewa, ana da dalilai masu tarin yawa na miƙa godiya ga irin gagarumin aikin da likitocin ƙasar Sin suka yi na tabbatar da cewa, jama'ar Zanzibar sun samu hidimar ayyukan kiwon lafiya mafi kyau…
Read More
Rashin yarda da kai ya sa wasu ƙasashen Yamma ke neman ta da matsaloli

Rashin yarda da kai ya sa wasu ƙasashen Yamma ke neman ta da matsaloli

Daga BELLO WANG Ofishin babban kwamishina mai kula da aikin kare haƙƙin dan Adam na MƊD ya gabatar da wani rahoto dangane da jihar Xijiang ta ƙasar Sin a kwanan baya, wanda ya nuna al’adar ƙasar Amurka da wasu ƙawayenta ta neman yin amfani da batun haƙƙin dan Adam a matsayin wani makami. Me ya sa a ce haka?Saboda da farko dai, yadda aka tsara rahoton ya saba ka’idoji. A matsayinsa na daya daga cikin hukumomin MƊD, ya kamata ofishin babban kwamishina mai kula da haƙƙin ɗan Adam ya gudanar da duk wani aiki ne bisa iznin da majalisar kare…
Read More
Ministan Nijeriya ya yi maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a ƙasar

Ministan Nijeriya ya yi maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a ƙasar

Daga CMG HAUSA Tarayyar Najeniya, babbar kasuwa ce da ƙasar Sin take zuba jari, da gudanar da cinikayya, da fitar da kayayyaki, da kuma ayyukan gine-gine a nahiyar Afirka. Kwanan baya ministan masana’antu da cinikayya da zuba jari na tarayyar Najeriya Otunba Adebayo ya bayyana yayin da ya zanta da wakilin CMG cewa, Najeriya da Sin suna gudanar da hadin gwiwar ƙut-da-ƙut a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya, kuma Najeriya tana maraba da kamfanonin ƙasar Sin da su zuba jari tare kuma da kafa kamfanoni a ƙasar, kana tana fatan za ta yi…
Read More
Gwamnatin Masari a mizani

Gwamnatin Masari a mizani

A zahiri sai gwamnatin APC a Katsina ta ƙara azama wajen duba kura-kurai ta fuskar gyara ganin yadda gwamnatin Rt Hon His Exl. Alh Aminu Bello Masari ta ke daf da cika shekaru takwas tana mulki, inda wasu na yabo wasu na suka. An ce mutum ajizi ne. Kuma iya ma mutane sai Allah amma a ce a na da hurumi na zaɓe sau uku ai ko shakka ban yi wanda zai fito ya kawar da gwamna Masari ban hango shi ba. Amsa ta ita ce ba gwamna Masari ba ɗaukacin gwamnonin APC a Arewa da Kudu duka su na…
Read More
Uwar mulkin mallaka ta yi sabuwar firaminista

Uwar mulkin mallaka ta yi sabuwar firaminista

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Uwar ’yan mulkin mallaka ta duniya wato ƙasar Birtaniya ta yi sabuwar firaminista, Liz Truss bayan turka-turkar da ta kai ga kawar da firaministan ƙasar Boris Johnson. Tuni sarauniya Elizabeth ta tabbatar da wannan sabon juyi da ya kawo babbar jami’ar gwamnatin Johnson a matsayin jagorar ƙasar ta fuskar siyasa. Yadda a kan samu sauyin jagoranci a Birtaniya na da ban sha’awa don in ka duba nau’in laifukan da kan kai ga ƙin jinin firaminista ba za su zama wani abun damuwa a wasu ƙasashe masu tutiyar dimkoraɗiyya ba. Rashin da’a da taurin kai ko halin…
Read More
Gudunmawa da soyayyar Sarauniya Elizabeth II ga wasan ƙwallon ƙafa

Gudunmawa da soyayyar Sarauniya Elizabeth II ga wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta rasu tana da shekaru 96 a duniya, inda ta shafe shekaru 70 a kan karagar mulki, inda ta tavo dukkanin al'adun Birtaniya, ciki har da wasan ƙwallon ƙafa. Sarauniyar ta kasance jigo a wasu manyan lokuta a tarihin wasanni, musamman na ƙwallon ƙafa a Birtaniya. Daga gabatar da gasar kofin duniya na farko a Ingila ga Sir Bobby Moore a 1966, zuwa karrama ’yan wasa da dama waɗanda suka kasance fitattun jaruman ’yan wasa ne, zuwa kasancewarta jigo a wasan ƙarshe na kofin FA. Akwai ma jita-jitar cewa sarauniyar ya…
Read More