Editor

9513 Posts
Siyasar Kwankwasiyya: Bayan tiya akwai wata cacar

Siyasar Kwankwasiyya: Bayan tiya akwai wata cacar

Daga RAHMA ABDULMAJID A ranar da na yi sharhi a kan Atiku da Tinubu 'yan kwankwasiya masu zuciya a hannu sun far min har da saƙonni cewa ban sanya madugu a sharhi na ba. Abinda na saba yi shi na yi, wato ƙyaƙyata dariya. Saboda ganin rashin adalci ƙarara da rashin tuna baya. A 2019 na kasa haƙuri wajen nuna goyon bayan Kwankwaso ne ba don mutanensa ko shi ba sai don na yi na'am da ƙudirorinsa har ana min Laƙabi da 'yar kwankwasiya. Kuma har yau da ni za a bai wa zaɓin Shugaban Nijeriya, Kwankwaso zan baiwa babu…
Read More
Tinubu: Tsakanin takara da Musulunci

Tinubu: Tsakanin takara da Musulunci

Daga FATUHU MUSTAFA Baya ga batun rashin lafiyar ɗan takarar shugabancin Nijeriya na APC, Bola Ahmed Tinubu, yanzu kuma an kawo batun wai a matsayinsa na musulmi, bai taɓa gina masallaci ba, kuma ma wai 'ya'yansa dukkansu kiristoci ne, saboda uwargidansa kirista ce.  A saboda haka, na ga akwai buƙatar mu warware zare da abawa a kan wannan batu da ya taso. Na farko dai, ba ma batun auren bakitabiya a musulunci ba, wanda kowa ya san halal ne. Ba a Yarbawa ba ne kawai ake samu musulmi ya auri kirista har ma acikinmu yan Arewa. Misali, Alhaji Baba Danbappa…
Read More
Ta hanyar biyayyar miji mace za ta samu duk abinda ta ke so – Halima Ben Umar

Ta hanyar biyayyar miji mace za ta samu duk abinda ta ke so – Halima Ben Umar

"Mata na fuskantar matsaloli yayin aiki tare da maza" Daga AISHA ASAS Yawaitar ƙalubale ga mata a yayin da suke aiki tare ko a ƙarƙashin maza ya jima yana kasancewa cikin al'ummar Hausa, wanda ya cancanci ya zama wutar da za ta cinye ilahirin burin mata na ɓangaren aiki. Da yawa daga cikin mata ƙalubalen na yin tasiri sosai a mafarkin zuciyarsu ta fuskar aiki, inda suke ajiye makaman yaƙi, su haƙura da burinsu. Duk da haka, akan samu jajirtattu daga cikin mata da suke iya jure wannan ƙalubale da ma wasu don tabbatar da ba su hana su isa…
Read More
Ƙalubalen iyaye kan ’ya’ya mata masu shaye-shaye

Ƙalubalen iyaye kan ’ya’ya mata masu shaye-shaye

ABBA ABUBAKAR YAKUBU Matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ba baƙon abu ba ne, musamman ma ga 'ya'ya maza, inda ya ke da mamaki da ɗaukar hankali shi ne a ga ’ya mace budurwa, bazawara ko matar aure tana bulayi cikin maye ko a ga tana ɗaga kwalba ana shewa da ita, babu ma dai kamar yarinya ’yar musulma kuma bahaushiya ko ’yar Arewa, da ake kyautata mata zaton ta taso a gidan tarbiyya, kunya da ƙyamatar irin waɗannan halaye marasa kyau. Ba lallai ya zama abin kunya ga matan bariki ko masu zaman kansu da aka fi sani…
Read More
Rabuwar aure: Shin kun shirya tunkarar ƙalubalensa?

Rabuwar aure: Shin kun shirya tunkarar ƙalubalensa?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haɗuwa a wannan makon! Sannunku da jimirin karatun jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu yi magana a kan yadda wasu lokuta a rayuwar aure da zaman yake yin zafi ya ƙi daɗi, har ma su yanke shawarar su rabu da juna. Ko ɗaya ya dinga riyawa a zuciyarsa ba mafita illa ya rabu da ita ko ita ta dinga tunanin idan ba ta rabu da shi ba ba ta da sauran wani 'yanci. Eh haka ne, akwai wasu lokuta na rayuwar aure da suke zuwa ku ji sam ba kwa jin daɗin…
Read More
Firaministan Ƙasar Sin ya jaddada buƙatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki

Firaministan Ƙasar Sin ya jaddada buƙatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki

Daga CMG Hausa Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya jaddada buƙatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki, da farashin kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi. Li ya yi tsokacin ne yayin taron majalissar gudanarwar ƙasar Sin, bayan da ya saurari rahotanni daga tawagogin aikin daidaita sassan tattalin arziki guda 2. Ya ce daidaituwar tattalin arziki ya danganta da yanayin hada-hadar kasuwanni, don haka ya buƙaci a kara azama, wajen rage wahalhalun da sashen hada-hadar kasuwannin ke fuskanta, yayin da ake ƙara faɗaɗa harkokin zuba jari, har a kai ga samar da damammakin bunƙasa kasuwanni, da ƙarfafa ƙwarin gwiwarsu. Li…
Read More
Yanayin sufurin zamani a Ƙasar Sin

Yanayin sufurin zamani a Ƙasar Sin

Daga LAWAL SALE Sufuri dai abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan adam ta fannin zirga-zirga da dakon kaya daga wannan wuri zuwa wancan. Kafin zuwan zamanin kekuna, da motoci da layin dogo da jiragen sama, ana amfani ne da dabbobi kamar raƙuma da dawakai da jakuna domin tafiye-tafiye da dakon kaya na yau da kullum. A wancan lokacin, ƙasar Sin da ƙasashe da dama sun yi amfani da irin wannan nau’in sufurin a zirga-zirgar da aka fi sani da “silk road’’ wato hanyar siliki domin kasuwanci tsakaninsu. Daga nan dai aka fara samun ci gaba a yayin da…
Read More
Jakadan Ƙasar Sin a Najeriya ya ziyarci Lagos

Jakadan Ƙasar Sin a Najeriya ya ziyarci Lagos

Daga CMG Hausa Daga ranar 7 zuwa 9 ga watan nan, jakadan ƙasar Sin a Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya ziyarci jihar Lagos, inda ya gana da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu. Yayin ganawar tasu, Cui Jianchun ya ce, jihar Lagos tana kan gaba a Najeriya a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kasuwanci da masana’antu, kuma wuri ne da baƙi Sinawa suka fara zuwa a Najeriya domin yin ciniki da kasuwanci a ƙasar. Ya ce yankin yin ciniki cikin ‘yanci na Lekki, da masana’antar tace mai ta Dangote, da aikin tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki,…
Read More
Dandalin shawara

Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Salam. Asas barkan mu. Don Allah ni matsalar da na ke da irin kin gane ba Ina da suruka irin munafukan tsofaffin nan. A gaban mijina sai ta nuna tana so na amma idan ba idonshi sai ta yi ta cin zarafi na, ta yi ta kai ƙara na. Na yi ƙoƙarin fahimtar da shi amma kuma sai dai mu yi ta faɗa. Ki taimaka min da shawarar yadda zan kawo ƙarshen lamarin. AMSA: Da farko dai dole sai kin fara da canza irin kallon da kike yi wa uwar mijin taki matuƙar kina so ki…
Read More
Matan aure ku matso (2)

Matan aure ku matso (2)

Daga AISHA ASAS Shafin kwalliya na satin da ya gabata ya janyo hankalin matan aure kan kayan mata, inda ya miƙa wasu daga cikin tsarabar da ya yi wa masu karatun mu tare da alƙawarin ci gaba a wani makon. To Allah mai komi da kowa ya ba mu ikon cikawa. Idan uwar gida shirya, sai mu ce asha karatu lafiya: Nonon raƙumi idan ki ka haɗa shi da garin riɗi ki na sha zai ba ki fiye da tunanin ki a ni’ima. Sai dai fa yana buƙatar naci na ɗan lokaci kafin ya kama jikinki. Ɓawan mangoro da ƙodagon…
Read More