16
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ambaliyar ruwa ta tayar da garuruwa da ƙauyuka fiye da 100 a Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya, a cewar hukumomi. Kazalika ambaliyar ta haddasa asarar gidaje da dabbobi da kayan amfanin gona da dama a yankin ƙaramar hukumar Zaki ta jihar. Mutanen da abin ya shafa sun ce an kai masu ɗaukin kwale-kwale na haya, da ke kwashe su daga wuraren da ruwan ya mamaye, amma kuma babu wani tallafi na kayan abinci da magunguna da dai sauransu da suka samu har yanzu. Wani mutum da ambaliyar ruwan ta shafa, wanda…
