16
Sep
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗan takarar majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Fagge a Jam'iyyar ADC, Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya jajentawa 'yan kasuwar Kantin Kwari bisa iftila'i da ya samesu na ambaliyar ruwa da ya janwo lalacewar dukiya mai tarin yawa. Wakili ya kuma yi irin wannan jaje ga 'yan kasuwar Bairut suma bisa matsalar da aka samu a kasuwar ta rushewar wani gini da ya janwo asarar rai da raunata mutane. Kwamared Haruna Wakili ya yi fatan waɗanda abin ya shafa Allah ya mayar musu da alheri ya kuma bunƙasa abinda aka rasa. Ɗan majalisar dai ya yi…
