Editor

9513 Posts
Wakilin musamman na Xi zai halarci jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu

Wakilin musamman na Xi zai halarci jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta sanar a yau Asabar cewa, bisa gayyatar da gwamnatin ƙasar Birtaniya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban ƙasar Wang Qishan, zai halarci jana'izar sarauniya Elizabeth ta biyu da za a yi a birnin Landan a ranar Litinin 19 ga watan Satumba. Fassarawar Ibrahim
Read More
Wang Yi ya yi tsokaci kan sakamakon Ziyarar Xi

Wang Yi ya yi tsokaci kan sakamakon Ziyarar Xi

By CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya halarci taron majalisar shugabannin ƙasashen mambobin ƙungiyar haɗin gwiwar Shanghai karo na 22 a birnin Samarkand, tare da kai ziyarar aiki a ƙasashen Kazakhstan da Uzbekistan bisa gayyatar da aka yi masa, tsakanin ranakun 14 zuwa 16 ga wannan wata. Mamban majalisar gudanarwar ƙasar kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya yi bayani kan ziyarar shugaban ga manema labarai. Yana mai cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya yi, ita ce ziyara ta farko da ya kai zuwa ƙetare, tun bayan ɓarkewar annobar cutar COVID-19, don haka tana da ma’ana…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Kano ta baje kolin masu laifuka daban-daban 331

Rundunar ‘yan sandan Kano ta baje kolin masu laifuka daban-daban 331

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Kimanin mutum 331 ne rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta yi nasarar yin awon gaba da su kan laifuffuka mabambanta a jihar Kano cikin makonni huɗu. Hakan ya biyo bayan lokacin da sabon kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawal Daura lokacin da yake gabatar wa da manema labarai masu laifin karo na farko bayan shafe makonni biyu da zuwansa matsayin Kwamishinan 'Yan Sandan jihar. CP Abubakar Lawal ya ce cikin ikon Allah ana cigaba da samun nasara daga batun samar da zaman lafiya a Jihar Kano ta ƙoƙarin gwamnati jihar, kwamitocin unguwanninsu…
Read More
Ba siyasar jahilci muke yi ba – Ogan Ɓoye

Ba siyasar jahilci muke yi ba – Ogan Ɓoye

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Hon. Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Ɓoye, ya bayyana cewa su ba sa siyasar jahilci, kuma bai yin siyasar gaba ko nunin yatsa, a cewarsa yana siyasa ne ta mutunci da mutunta juna. Ogan Ɓoye wanda jigo ne a tafiyar NNPP ta Kwankwasiyya, kana makusanci ga Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, rahotanni sun bayyana cewa magoya bayansa sun nuna fushinsu da cire wasu hotuna, kan rashin bashi takarar Sanatan Kano ta Tsakiya wanda Sanata Rufai Sani Hanga ya samu takarar bayan ficewar Malam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano daga Jam'iyyar NNPP. Ogan Ɓoye…
Read More
Sarkin Kano ne uban gidauniyar ELS ta taimaka wa marayu – Adosuwa Ogechi

Sarkin Kano ne uban gidauniyar ELS ta taimaka wa marayu – Adosuwa Ogechi

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugabar gidauniyar tallafa wa iyayen marayu, mata, da sauran masu rauni mabuƙata da ake kira ELS Empowerment Foundation, Misis Adosuwa Ogechi Udo, ta bayyana Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin uban gidauniyar, saboda kasancewarsa mutum mai tausayin marayu da gajiyayyu. Ohechi ta ce babban aikin gidauniyar tasu shi ne koyar da mata iyayen marayu da makamantansu sana'o'in da su ka shafi girke-girke, ɗinke-ɗinke saƙa da sauran sana'o'i na dogaro da kai, musamman ga mata waɗanda mazajensu suka rasu ko kuma waɗanda suka rabu da mazajen su sakamakon matsaloli na rayuwa da…
Read More
Ambaliyar ruwa ta rushe gidaje sama da 200 a Zariya

Ambaliyar ruwa ta rushe gidaje sama da 200 a Zariya

Daga MOH'D BELO HABIB a Zariya Ambaliyar ruwa ya rushe gidaje sama da 200 a cikin garin Zariya dake ƙaramar hukumar Zariyan cikin jihar Kaduna. Wakilin Manhaja wanda ya zaga yankunan da abin ya shafa, ya ruwaito cewa gidajen da al'amari ya shafa galibansu gidajen talakawa nw kuma ambaliyar ruwan na da nasaba ne da ruwan da aka dinga sheƙawa yi akai akai har na tsawon kwanaki huɗu ko biyar a jere. Binciken da wakilin Manhajar ya gudunar a unguwannin da iftila'in ya shafa kamar Kusfa, Unguwar Malam Sule, Unguwar Danjinjiri, Kan Fage, Rimin Doko, Unguwar Nufawa da dai sauransu,…
Read More
Nijeriya ta fara raba kayayyakin kiwon lafiya ta hanyar jirgi mara matuƙi

Nijeriya ta fara raba kayayyakin kiwon lafiya ta hanyar jirgi mara matuƙi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Nijeriya ta kafa tarihi sakamakon bin sahun wa su ƙasashen duniya kamar Ghana da Rwanda da a cikin sauƙi suke rarraba kayayyakin kiwon lafiya, waɗanda suka haɗa da magunguna da jakakkunan jini ga wuraren da suke da wuyar ratsawa da jirage marasa matuƙa. Haka maganar take kamar yadda jirgi maras matuƙi mai gudanar da hidimomi na kamfanin, Zipline, ya fara rarraba kayayyakin kiwon lafiya ba tare da matuƙi ba wa cibiyoyin kiwon lafiya dake cikin Jihar Kaduna. Kamfanin ya bayyana cewar, kayayyakin kiwon lafiya, da ma wasu kayayyakin lodin farko da aka aza wa jirgin…
Read More
Sin ta yanke shawarar sanya takunkumai a kan shugabannin kamfanonin Amurka da ke da hannun sayar da makamai ga Taiwan

Sin ta yanke shawarar sanya takunkumai a kan shugabannin kamfanonin Amurka da ke da hannun sayar da makamai ga Taiwan

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta shaida wa taron manema labaru da aka saba yi Jumma’ar nan cewa, domin kare martabar ƙasar Sin da moriyar tsaron ƙasar, gwamnatin ƙasar Sin ta yanke shawarar ƙaƙaba takunkumai kan jagororin kamfanonin Raytheon Technologies da Boeing Defense na ƙasar, saboda hannun da suke da shi a makaman da Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na ƙasar Sin. Bayan da Amurka ta sanar da shirinta na sayar da makaman da darajarusu ta dalar Amurka biliyan 1.106 ga yankin Taiwan a ranar 2 ga watan Satumba, ƙasar Sin…
Read More
Kamfanonin Ƙasar Sin sun shirya taron horar da matasan Afrika

Kamfanonin Ƙasar Sin sun shirya taron horar da matasan Afrika

Daga CMG HAUSA An buɗe cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da ilimin zirga-zirgar jiragen ruwa ta farko, ƙarƙashin jagorancin kamfanonin ƙasar Sin, jiya Alhamis a birnin Djibouti City na ƙasar Djibouti. Taken cibiyar shi ne, ƙirƙire-ƙirƙire na zamani da cinikayya ta intanet tsakanin ƙasa da ƙasa. Kusan mutane 30 daga ƙasashen Djibouti da Habasha da Kenya da Uganda ne aka zaba domin su karɓi horon na kwanaki 8. Kuma yayin horon, matasan za su koyi darussan tafiyar da harkokin kamfani, kana za a gabatar da lokaci da tarukan ƙara wa juna sani daga masanan Sin da Afrika tare da ziyartar tashar jiragen ruwa…
Read More
Sin da Uganda na sa ran ƙarfafa haɗin gwiwarsu a fannin gina ababen more rayuwa Ga ƙirƙire-ƙirƙire

Sin da Uganda na sa ran ƙarfafa haɗin gwiwarsu a fannin gina ababen more rayuwa Ga ƙirƙire-ƙirƙire

Daga CMG HAUSA Jiya Alhamis ne aka gudanar da taron murnar cika shekaru 60, da kafuwar hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Uganda ta kafar bidiyo. A yayin taron, mataimakin shugaban ƙungiyar sada zumunci da ƙasashen waje ta ƙasar Sin Jiang Jiang, ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata ƙasar Sin da ƙasashen Afirka su haɗa kansu, wajen ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin gina ababen more rayuwa, da gudanar da ƙirƙire-ƙirƙire ta fuskar harkokin sadarwa, da neman bunƙasuwa ta hanyar kare muhalli, domin neman babban ci gaba. A nata ɓangaren, jakadar ƙasar Uganda dake ƙasar Sin Oliver Wonekha ta…
Read More