Editor

9513 Posts
Nijeriya na fuskantar tsadar abinci mafi muni cikin shekaru 17 – Rahoto

Nijeriya na fuskantar tsadar abinci mafi muni cikin shekaru 17 – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A halin yanzu, Nijeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 17 yayin da farashin kayayyaki da ayyuka ya qaru da kashi 20.52 cikin ɗari a cikin watan Agustan 2022 daga kashi 19.64 cikin ɗari da aka samu a watan da ya gabata. Wannan yana ƙunshe ne a cikin rahoton ƙididdigar farashin kayan masarufi (CPI) na watan Agusta 2022, wanda aka fitar a ranar Alhamis, 15 ga Satumba, 2022. A cewar NBS, adadin ya kai kashi 3.52 sama da kashi 17.01 da aka rubuta a watan Agustan 2021. Rahoton ya kuma nuna cewa hauhawar…
Read More
Sarauniya Elizabeth, mutuwa ƙarshen dukkan talikai

Sarauniya Elizabeth, mutuwa ƙarshen dukkan talikai

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kowace rai lalle wata rana sai ta ɗanɗani ɗacin mutuwa domin mutuwa tamkar gadon dukkan talikai ne. Ba ma sai mutum ya yi wani dogon nazari ba, zai amince cewa dukkan mu za mu mutu yau ne ko gobe ko jibi ko ma shekarar baɗi ko shekaru da dama. Misalai na da yawa da za mu iya fahimtar haka. Ba wanda ya ke raye a yanzu da wani na sa a yanzu ko a da can bai mutu ba. Ga shi ma ko sakwannin yanar gizo ka zo dubawa zai yi wuya ba ka ga labarin…
Read More
Gwamnati ce babbar matsalar Nijeriya (2)

Gwamnati ce babbar matsalar Nijeriya (2)

A cigaba da rubutu da na ɗauko game da matsaloli da muke ta fuskanta a ƙasar nan, na yi bayani yadda gwamnatin ta ke nuna gazawa harkokin tattalin arziki da kuma fannin ilimi. A makon jiya, na tsaya ne akan cewa zamu yi bayani akan taɓarɓarewar rashin tsaro. Harjar tsaro, wani yanayi ne da ke ɓata tattalin arzikin ƙasa. Wanda ba iya nan ba, zamu iya cewa tuk abinda babu kwanciyar hankali ciki to babu cigaba. Kuɗi na tafi saboda harkar tsaro, kuma dukiya na salwanta ga uwa uba kuma rashin muhalli da kuma walwala da al'umma ke ciki. Haƙiƙa…
Read More
Nijeriya da ƙasar Poland za su sabunta alaƙar kasuwanci tsakaninsu

Nijeriya da ƙasar Poland za su sabunta alaƙar kasuwanci tsakaninsu

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban ƙasar Nijeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya bayyana cewa, akwai buƙatar a ƙara ɗabbaƙa alaƙar cinikayya dake tsakanin ƙasar Poland da Nijeriya. Domin a cewar sa, duk da dai da ma alaƙarsa tana nan tsahon shekaru 60 da ƙulluwa, akwai buqatar ƙara ƙarfafa ta saboda sanyi da ya ce yana ganin ta yi. "Za mu so mu ga an samu haɓakar kasuwanci tsakanin ƙasashen guda biyu, domin a halin yanzu hulɗar kasuwanci ta yi ƙasa sosai tsakanin ƙasashen biyu duk da tsahon lokacin da aka ɗauka ana hada-hada tsakanin ƙasashen guda biyu". Buhari ne…
Read More
2023: Tikitin Musulmi da Musulmi tsantsar yaudara ce, inji Sheikh Gumi

2023: Tikitin Musulmi da Musulmi tsantsar yaudara ce, inji Sheikh Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi ko Musulmi da Musulma a matsayin yaudara, yana mai cewa abin da ƙasa ke buƙata a 2023 gogaggen shugaba ne da zai iya haɗa kan al’umma. Kamar yadda Vanguard ta ruwaito. Ya ce Nijeriya ba ta buqatar ƙaramin ɗan siyasa a matsayin shugaban ƙasa, sai dai gogaggen ɗan siyasa da zai jagoranci ta a zaɓen 2023 mai zuwa.Ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya su kawar da siyasar ƙabilanci a wannan karni na 21, kuma su haɗa kai a matsayin…
Read More
Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda, Muslihu Smith, ya yi murabus

Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda, Muslihu Smith, ya yi murabus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Sandan Nijeriya (PSC), Musilihu Smith ya yi murabus daga kan muƙaminsa. Wannan matakin dai na zuwa ne bayan rashin jituwa da kai ruwa rana da aka yi ta samu a tsakanin hukumar da Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali, dangane da batun ɗaukar sabbin ‘yan sanda, ƙarin girma wa jami’ai, ɗaukar kwansitabul da wasu jami’ai. Lamarin har ta kai Majalisar Ƙoli na hukumar ta buƙaci Smith da ya yi murabus cikin ruwan sanyi kuma ya amince da yin haka. Smith, wanda tsohon Sufeto Janar na ‘yan…
Read More
Taron MƊD: Yau Buhari zai tafi Amurka

Taron MƊD: Yau Buhari zai tafi Amurka

Daga BASHIR ISAH Yau Lahadi ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Amurka don halartar taron Malajisar Ɗinkin Duniya karo na 77 (UNGA77). Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar. A cewar Adesina, Buhari zai bayyana bayanan ƙasa ga taron Majalisar a ranar Laraba, 21 ga Satumba, 2022. Kazalika, ana sa ran Buhari ya gudanar da wasu ayyuka tsakani da wasu hukumomi yayin ziyarar kana kafin ya komo Nijeriya ranar Litinin, 26 ga Satumba, 26, 2022. Sanarwar ta ce,…
Read More
Kusantowar yaƙin neman zaɓen 2023

Kusantowar yaƙin neman zaɓen 2023

Nan da kwanaki kaɗan za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a hukumance. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), wacce ke da hurumin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe, ta sanya ranar 28 ga watan Satumba domin fara gudanar da ayyukan. Zaven 2023 na da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar dimokaraɗiyyarmu da ƙasa baki ɗaya. Tuni dai yanayin siyasa ya tashi yayin da 'yan takarar shugaban ƙasa ke yin alƙawura da yawa. Ƙasar na cikin tsaka mai wuya saboda ɗimbin ƙalubalen da ta ke ci gaba da fuskanta. Saboda ƙaruwar rashin tsaro, talauci da rashin aikin yi, an…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta cafke sojan bogi

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta cafke sojan bogi

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kama wani sojan bogi mai suna Zainu Lawal da ke bayyana kansa a matsayin jami’in sojan Nijeriya. Kakakin rundunar, Sp. Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu ‘yan ta’adda a hedikwatar rundunar da ke Gusau ya bayyana hakan yau Asabar. Sp. Shehu ya bayana cewar kayayyakin laifin da aka gano daga gare shi sun haɗa da, bindigu ƙirar revolver, 4 Cartridge, I D Card din soja na bogi da kuma kakin soja ɗaya.…
Read More
Ɗaliban Ghana 140 ne suka samu guraben ƙaro karatu na Jakadan Ƙasar Sin

Ɗaliban Ghana 140 ne suka samu guraben ƙaro karatu na Jakadan Ƙasar Sin

daga CMG HAUSA Ɗaliban ƙasar Ghana 140 ne suka samu guraben ƙaro karatu na jakadan ƙasar Sin dake ƙasar, saboda ƙwazon da suka nuna a fannin nazarin harshen Sinanci, a yayin wani biki da aka shirya a jami'ar Cape Coast (UCC) . Da yake jawabi a yayin bikin jiya Jumma’a, jakadan ƙasar Sin dake ƙasar Ghana Lu Kun, ya bayyana fatan samun tallafin karatun, zai taimaka wa ɗaliban Ghana a dukkan matakai wajen yin fice a fannin nazarin harshen Sinanci. Jakada Lu Kun ya bayyana cewa, yayin da ƙasar Sin ta zama ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a…
Read More