Editor

9513 Posts
Nijeriya ta zama koma baya da matsayin ƙasa mafi samar da man fetur a Afirka

Nijeriya ta zama koma baya da matsayin ƙasa mafi samar da man fetur a Afirka

Daga AMINA YUSUF ALI A cikin watan Agustan bana ne dai ƙasar Nijeriya ta koma samar da abinda bai wuce ganga 972,000 ta man fetur a kowacce rana. A yayin da ƙasashen Angola da Libya suka yi mata zarra ta hanyar samar da adadin da ya wuce wanda take samarwar kamar yadda ƙungiyar ƙasashen masu samar da man fetur (OPE) ta rawaito. OPEC ta saki waɗannan alƙalumman ne wannan watan Satumbar shekarar 2022 da muke ciki. Ita kuma ta samu wannan rahoto daga hukumar daidaita farashin mai ta Nijeriya. Dama tun a a makon da ya gabata ne dai jaridar…
Read More
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano ya nemi haɗin kan Hukumar Kwastam da SSS a jihar

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano ya nemi haɗin kan Hukumar Kwastam da SSS a jihar

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano A ranar Larabar wannan makon ne Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawal ya kai wa takwarorinsa na hukumar hana fasa ƙwauri mai kula da shiyyar Kano da Jigawa da kuma hukumar farin kaya wato SSS ziyarar aiki, kamar yadda jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Jihar Kano SP Haruna Abdullah Kiyawa ya fitar ga manema labarai. Da yake jawabi yayin ganawa da shugabannin hukumomin biyu, CP Abubakar Lawal Daura ya ce ya ziyarci vangarorin guda biyu ne don gabatar da kansa tare da neman goyon bayan wannan hukumomi don samun…
Read More
Gwamnatin Katsina ta fara bada horo ga ‘yan bijilanti don tunkarar ‘yan bindiga

Gwamnatin Katsina ta fara bada horo ga ‘yan bijilanti don tunkarar ‘yan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta fara horar da 'yan bijilanti 600 daga cikin mutane 3000 da gwamnatin ta yi alƙawarin ɗauka da kuma ba su horo domin su taimaka wa sauran jami'an tsaron dake jihar wajen yaƙar 'yan ta'adda. A madadin Gwamna Masari, mai bai wa gwamnan jihar shawara akan harkar tsaro Ibrahim Katsina ne ya ƙaddamar da shirin fara bada horon a sansanin horar da jami’an Civil Defence dake cikin birnin Katsina jiya Alhamis. Da yake jawabi Ibrahim Katsina ya bayyana cewa bayar da horon wani mataki ne da…
Read More
‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-14 sun kammala ayyuka a wajen ɗakin gwaji na Wentian

‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-14 sun kammala ayyuka a wajen ɗakin gwaji na Wentian

Daga CMG HAUSA ‘Yan sama jannatin ƙasar Sin 3 da suka tashi da kumbon Shenzhou-14, sun kammala ayyuka a wajen ɗakin gwaji na Wentian cikin nasara, kamar dai yadda hukumar lura da ayyukan sama jannati ta ƙasar CMSA ta bayyana a jiya Asabar. CMSA ta ce ya zuwa ƙarfe 1:35 na jiya bisa agogon birnin Beijing, dan sama jannati Cai Xuzhe ya buɗe ƙofar dakin gwaji na Wentian, kana da misalin ƙarfe 3:33, shi da abokin aikin sa Chen Dong, dukkansu sun fita wajen ɗakin gwajin. Ma’aikatan su biyu, sun koma cikin ɗakin gwajin da misalin ƙarfe 6 saura mintuna…
Read More
Yaushe ƙasashen Yamma za su iya ɗaukar nauyin da ke bisa wuyansu

Yaushe ƙasashen Yamma za su iya ɗaukar nauyin da ke bisa wuyansu

Daga LUBABATU LEI Kwanan baya, an gudanar da taron ƙolin ƙasashen Afirka game da daidaita matsalar sauyin yanayi a birnin Rotterdam na ƙasar Netherlands, inda shugabannin ƙasashen Afirka guda shida suka hallara, a yayin da firaministan ƙasar Netherland shi kaɗai ya halarci taron, ba tare da shugabannin sauran ƙasashen Yamma da aka ba su goron gayyata ba, ciki har da Faransa da Norway da Canada da sauransu. Hakan ya baƙanta ran shugabannin ƙasashen Afirka. Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall, wanda kuma shi ne shugaban karɓa-karɓa karba na ƙungiyar tarayyar Afirka, ya furta a wajen bikin buɗe taron cewa, “Abin baƙin…
Read More
Sin da Rasha za su gudanar da taron tattaunawa game da aikin tsaro

Sin da Rasha za su gudanar da taron tattaunawa game da aikin tsaro

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta sanar da yau Lahadi cewa, bisa gayyatar da bangaren ƙasar Sin ya yi, babban sakataren majalisar tsaro ta tarayyar Rasha, Patrushev Nikolai, zai ziyarci ƙasar Sin a yau Lahadi da gobe Litinin, don halartar taro na 17 na tattauna batun tsaron Sin da Rasha, gami da taro na 7, na tsarin haɗin gwiwa a ɓangaren aiwatar da doka tsakanin ƙasashen Sin da Rasha. Mai fassara: Bello Wang
Read More
Me ya sa takarar Sheikh Ibrahim Khalil ta zama barazana ga NNPP da APC a Kano?

Me ya sa takarar Sheikh Ibrahim Khalil ta zama barazana ga NNPP da APC a Kano?

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Ganin yadda zaɓen gama-gari na 2023 ke ƙara ƙaratowa, Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kuma ta fitar da ranar fara yaƙin neman zaɓe ga jam'iyyun siyasa 18 da suke da rajista, a yayin da 'yan takarkaru suka ɗaura ɗamara fita yaƙin neman zaɓen. Sai dai wannan dalilin ne ake ganin ya sa wata ƙungiya ta manyan masana a harkar aikin gwamnati da sauransu, da ake kira KJPF wato Kano Jigawa Professional Forum, inda ta kirawo ɗaukacin masu yin takara a kowace jam'iyya a Kano domin miqa wani kundi da ta wallafa domin…
Read More
Rodger Federer ya yi ritaya daga wasan Tennis

Rodger Federer ya yi ritaya daga wasan Tennis

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fitaccen ɗan wasan tennis ɗan ƙasar Switzerland, Roger Federer ya sanar da yin ritaya daga fagen wasan Tennis bayan da ya lashe kofuna sama da 103, da manyan wasanni 20 a cikin shekaru ashirin da huɗu na ganiyarsa a wasan ƙwallon Tennis. Federer ya fitar da sanarwa a shafinsa na Tiwuta, "wasan cin kofin Laver da za a yi a mako mai zuwa a Landan zai zama taron ATP na ƙarshe". Ɗan wasan mai shekaru 41, wanda ya lashe kofunan Grand Slam 20 bai taka leda ba tun bayan da ya yi rashin nasara a wasan…
Read More
A shirye muke mu janye yajin aiki – ASUU

A shirye muke mu janye yajin aiki – ASUU

…Amma idan an cimma matsaya, inji shugabanta*Ya ce, shigar da ƙungiyar ƙara ba mafita ba ce*Za mu cigaba da shiga tsakani don kawo ƙarshe, cewar wata ƙungiya Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sama da watanni bakwai kenan Ƙungiyar Malaman Jami'o'i a Nijeriya (ASUU) na cigaba da yajin aiki akan wasu buƙatu da suke neman gwamnati ta cika. Duk da zaman tattaunawa da ƙungiyar ta riƙa yi da Gwamnatin Tarayya akai-akai don sasantawa, amma ba a cimma wata matsaya ba, lamarin da ya haifar da kowanne vangare na zargin juna da nuna son zuciya, inda a gefe guda kuma ɗalibai…
Read More
Wayar salula ta taimaka wajen samar da sana’o’i ga matasa – Ashiru Yakasai

Wayar salula ta taimaka wajen samar da sana’o’i ga matasa – Ashiru Yakasai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana shigowar wayar hannu na tafi da gidanka a ƙasar nan ya taimaka sosai wajen samar wa ɗimbin matasa aikin yi da kuma haɓaka tattalin arziki. Jami'n hulɗa da jama'a na ƙungiyar kasuwar waya na titin Bairut kuma wanda shine jimi'in hulɗa da jama'a na biyu na ƙungiyar 'yan waya na Jihar Kano AMPAT, Ashiru Yusuf Yakasai shine ya bayyana hakan. Ya ce zuwan wayar hannu ya sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci ta yadda ake iya yin amfani da wayar wajen ƙulla hulɗa ta kasuwanci cikin sauƙi daga zaune za ka iya sayen duk…
Read More