Editor

9513 Posts
Illar rashin fahimtar juna a zamantakewar aure

Illar rashin fahimtar juna a zamantakewar aure

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Manhaja. A wannan mako muna tafe da bayani a game da yadda ma'aurata za su buɗe ƙofar fahimtar juna a tsakaninsu. Wannan matsala ta rashin fahimtar juna duk da yadda ake raina ta, idan ta yi kaka-gida a zaman aure, tana samar da babbar matsala har ma da rabuwa. Ba lallai ne mai karatu ya yarda da ni ba idan na ce matsalar rashin fahimta tana daga cikin manyan dalilan da ake samun matsaloli bayan aure ba. Sai ka ga an ƙulla aure irin…
Read More
Yanzu matan Kannywood za su iya harkar fim ba tare da an ga fuskarsu ba – Halima Ben Umar

Yanzu matan Kannywood za su iya harkar fim ba tare da an ga fuskarsu ba – Halima Ben Umar

Daga AISHA ASAS Labarin yunƙurin da mata ke yi, don kafa tarihi a masana'antar finafinai ta Kannywood ta hanyar shirya fim ɗin da mata zalla suka yi aikinsa, tuni ya karaɗe kunnuwan dubunnan al'ummar Hausa, kai ma har da wasu ɓangarori na wannan qasa tamu mai albarka. Da yawa sun tofa albarkacin bakinsu da bayyana ra'ayinsu. Wasu na ganin abin a matsayin cigaba, yayin da wasu ke ganin sa a matsayin hurimin da su matan bai kamata su shiga ba, sannan wasu kuma na  ganin abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Da wannan ne shafin Nishaɗi na…
Read More
Eavans zai shafe shekaru 21 a gidan yari

Eavans zai shafe shekaru 21 a gidan yari

Daga BASHIR ISAH Yaznu dai ya tabbata cewa, ƙasurgumin mai garkuwa da mutanen nan, Chukwudumeme Onwuamadike da ake yi wa laƙabi da Evans, zai shafe shekaru 21 a kurkuku bayan da kotu ta kama shi da laifin yin garkuwa da wani mai suna Sylvanus Hafia. Evans zai yi zaman kason ne tare da wani abokin cin mushensa Victor Aduba. A ranar Litinin Kotun Laifuka na Musamman mai zamanta a Ikeja, Jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Oluwatoyin Taiwo ta yanke wa waɗanda lamarin ya shafa hukuncin bayan da ta same su da laifin haɗin baki da yin garkuwa da Sylvanus…
Read More
An kammala aikin girbin hatsi a gonakin fiye da kadada 11,333,333 na Ƙasar Sin a wannan lokacin kaka

An kammala aikin girbin hatsi a gonakin fiye da kadada 11,333,333 na Ƙasar Sin a wannan lokacin kaka

Daga CMG HAUSA Ma'aikatar aikin gona da ƙauyuka ta ƙasar Sin ta sanar a kwanan baya cewa, an riga an kammala aikin girbin hatsi a gonaki fiye da kadada 11,333,333 a ƙasar Sin, jamillar da ta kai kashi 13.3% na ɗaukacin gonakin ƙasar da ake noman hatsi a ciki, a wannan lokacin kaka. Ban da wannan kuma, wakilin CMG ya lura da muhimmiyar rawar da inshorar aikin gona ke takawa a fannin tabbatar da samun girbi mai armashi, inda kamfanonin inshora suke ba da tallafi ga manoma wajen tinkarar bala'i daga indallahi. Sa'an nan a lokacin da manoma suka samu…
Read More
Kalaman John Kerry sun nuna girman kai na ƙasashen Yamma

Kalaman John Kerry sun nuna girman kai na ƙasashen Yamma

Daga BELLO WANG Kalaman da manzon musamman na shugaban ƙasar Amurka mai kula da aikin tinkarar sauyawar yanayi John Kerry ya furta, a taron ministocin ƙasashen Afirka kan aikin kare muhalli, wanda ya gudana a ƙasar Senegal a kwanan baya, sun ba ni mamaki sosai. Saboda a gaban wakilan dukkan ƙasashen Afirka, mista Kerry ya ce ƙasashe masu sukuni, ba su da wani nauyi na tarihi game da batun sauyawar yanayin duniya. A ganinsa, aikace-aikace na ɗaukacin dan Adam ne ke sa ake samun matsalar dumamar yanayi, saboda haka, ko da wata ƙasa dake fama da koma bayan tattalin arziki…
Read More
Shugaba Xi ya aike da wasiƙar taya murnar buɗe taron dandalin ƙasa da ƙasa a fannin samar da kayayyakin masana’antu

Shugaba Xi ya aike da wasiƙar taya murnar buɗe taron dandalin ƙasa da ƙasa a fannin samar da kayayyakin masana’antu

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murnar bude taron dandalin ƙasa da ƙasa a fannin tabbatar da juriya da ɗorewar tsarin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni. Xi Jinping ya aike da wasiƙar ne a Litinin din nan, ga mahalarta taron dandalin da aka buɗe a birnin Hangzhou, fadar mulkin lardin Zhejiang na ƙasar Sin. Cikin wasiƙar tasa, shugaba Xi ya ce wanzar da juriya da daidaito a fannin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, hanya ce ta tabbatar da ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, tare da biyan…
Read More
Osinbajo ya isa London don halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth ll

Osinbajo ya isa London don halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth ll

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya isa birnin London a ranar Lahadi domin halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth ll. A ranar Asabar Osinbajo ya bar Abuja zuwa Birtaniya inda zai wakilci Nijeriya wajen wasu muhimman ayyuka, ciki har da jana’izar Marigayiya Sarauniya Elizabeth. Hadimin Osinbajo kan harkokin yaɗa labarai, Laolu Akande, ya ce bayan da mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa London a ranar Lahadin, ya ziyarci inda aka ajiye gawar marigayiyar a Westminster. Kazalika, ya ce, Osinbajo ya sanya hannu a littafin da mahalarta jana’izar kan rubuta sunayensu. Kana ya ce, “Nijeriya ta shiga sahun ƙasashe renon…
Read More
Abin damuwa ne irin halin ƙuncin da zawarawa ke ciki — Sayyida Aisha Abubakar

Abin damuwa ne irin halin ƙuncin da zawarawa ke ciki — Sayyida Aisha Abubakar

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Masu hikimar magana na cewa, ciwon 'ya mace na ’ya mace ne. Kuma abu namu maganin a kwaɓe mu. Wannan duk maganganu ne na azanci da ake jingina su ga mata. Duk kuwa da cewa da ake yi mata ba su cika son junansu ba, ko nuna goyon gaba da tausayawa 'yan uwansu mata ba. Amma wannan zargin bai cika zama gaskiya ba, domin kuwa ana samun mata da ke nuna tsananin tausayawa da tallafawa ga 'yan uwan su, sakamakon wata jarabawar rayuwa da suke fuskanta. Hajiya Aishatu Abubakar Abdullahi da aka fi sani da Sayyida…
Read More
Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (1)

Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (1)

Daga AISHA ASAS Matsalar kogon haƙora ko in ce ramin haƙora matsala ce da ta zama ruwan dare a tsakanin mutane, kasancewar akan same ta a wurin manya da yara kai har ma a tsofaffi. Matsalar dai ta zama wata wutar daji da ke saurin tsananta ba tare da mai ita ya ankara ba, kasancewar saurin tsananta da ta ke yi. Sai dai abin da ba mu sani shine, matsalar na ta’azzara ne albarkacin wasu ababen da muke yi da ke taimaka wa cutar wurin yaɗuwa, kamar yawan barin baki a bushe, rashin sinadarin fluorine (sanadari ne da ke hana…
Read More
Duniyar Ƙirifto Karansi: Yaushe pi za ta fashe ne? (2)

Duniyar Ƙirifto Karansi: Yaushe pi za ta fashe ne? (2)

Daga DANLADI Z. HARUNA Tun a farkon shekara ta 2020 ake ta hasashen za a soma aiki da Pi a matsayin kuɗin intanet, wannan ta sa wasu ɗaliban Malam Nikolas musamman na ƙasashen Asiya, suka yi awon gaba suke ta buɗe kantuna da sunan 'Pi Mall', inda aka ce suna saye da sayarwa ta amfani da kuɗin Pi. Da alama wannan abu yayi wa malamin daɗi, don haka ya ja wasu da dama cikin tsarin ta hanyar da ake kira 'Hackathon'. Sai dai ƙila hakan bai yi wa ɗaya daga waɗanda suka soma aikin daɗi ba. A watan Fabrairu na…
Read More