Xi ya yi bayani game da matsayi da fifikon dangantakar dake tsakanin Sin da Kazakhstan

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Kazakhstan Tokayev a birnin Nur-Sultan, fadar mulkin ƙasar ta Kazakhstan.

Xi Jinping ya bayyana cewa, ya yi matukar farin cikin sake ganawa da takwaransa na Kazakhstan.

Yana mai cewa, wannan ita ce ziyararsa ta farko zuwa ƙasashen waje, tun bayan ɓarkewar annobar COVID-19, kuma ya zabi zuwa ƙasar Kazakhstan, wadda ta nuna babban matsayi na daban kan alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Ƙasar Sin za ta ci gaba da zama aminiyar kawa kuma abokiyar hulɗar Kazakhstan.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *