‘Sanadin Kenan’ (3)

Daga FATIMA IBRAHIM GARBA DAN-BORNO

Yau asabar ya yi daidai da ranar da aka ɗibarwa Sulaiman a matsayin ranar da zai mallaki matarsa Asma’u. Ya fito yana walwali ya ji alamun numfarfashi. Har zai wuce ya dawo. A bakin ƙofar ɗakin mai kama da bukkan wasan yara ya tsaya ya ce, “Menene haka kike yi kamar mai shirin haihuwa?”

Muryarta bata fita sosai ta ce,
“Kaina ciwo yake yi mini, ka taimaka min da magani. Ina jin wani abu kamar allura yana tsikarina.”

Nan da nan zuciyar Sulaiman ta sanar da shi tsabar kishi ne ke ɗawainiya da ita, take so dole sai ta ɓata masa biki.

“Sai ki jirani sai na kammala abubuwan da nake yi. Salima don Allah kada ki ɓata mini biki don Allah. Bana so masu kawo amarya su san kina cikin gidan nan. Kamar yadda kika rufawa kanki asiri kika yi shiru har aka gama danki, haka nake so ki yi har a kawo amarya a tafi. Idan kuwa kika ƙi ji, ke ce za a fita duniya ana yi maki dariya ana cewa mai yoyon fitsari.”

Ita dai Salima ba fahimtarsa take yi sosai ba. Tana riqe da kanta da hannu bibbiyu da take ji yana juya mata. A duk lokacin da ciwon kan ya matsa mata tana shiga wani hali. Sai dai har ciwon ya gaji ya daina babu wanda ya taɓa bata ko magani, bare akai ga zancen binciken dalilin irin ciwon kan.

Wataran har zabura take yi idan ya tsikareta. Sulaiman bai jira komai ba ya sa kai ya fice abinsa.

Mus’ab ya samu da ƙyar ya je ɗaurin auren, bai jira komai ba ya wuce gida. Abokai suka yi ta cigiyarsa. Bayan an kai amarya anwatse ne, Sulaiman ya zo har gida ya matsawa Mus’ab akan dole sai sun je sun kaishi gurin amarya.

Dole Mus’ab ya tashi suka tafi. Tun daga bakin qofar gidan yake baza idanu. Ya rasa dalilin faɗiwar gaban da yake fama da ita, tun shigowarsa gidan.

Sai dai har suka gama gaisawa da amaryar babu Salima babu dalilinta. Yana son tambayar in da take, amma kalaman Ummansa suna yi masa yawo a tsakiyar kansa.

Sulaiman ya tashi domin yi masu rakiya, a lokacin idanun Mus’ab ya hasko masa wani qaramin ɗaki da baisan da shi ba.

“Sulaiman me zaka yi da qaramin ɗaki haka kai ba yara ba, bare in ce ka yi masu wurin wasa ne.”

Mus’ab ya yi tambayar yana ci gaba da kallon ɗakin kamar mai ƙoƙarin gano abin da aka ɓoye a ciki. Hantar cikin Sulaiman ya karta da ƙarfi. Sai da ya daidaita natsuwarsa sannan ya ce,
“Kai kasan ko na fara tanadin zuwansu ne?” Sauran abokan suka yi dariya suna yi masa shaƙiyanci. Shi dai Mus’ab bai motsa daga wurin ba. Wata zuciyar tana sanar da shi ya leƙa ya ga menene a ciki.

Sulaiman ya sake daburcewa. A lokacin kuma ɗaya daga cikin abokan ya ce, “Ahaf! Mun yi babban mantuwa kuwa. Ina Uwargida?”

Ambatar uwargida da Musa ya yi ya sa Mus’ab juyowa gaba ɗaya ya zubawa Sulaiman idanu ta cikin hasken lantarkin gidan. Sulaiman ya waske da cewa,
“Ta gaya mini kanta yana ciwo shiyasa ban kirawota ba.”

Mus’ab ya saki ajiyar zuciya, sannan duk suka yi waje. Da sauri ya rufe gidansa yana ajiyar zuciya. Bai san dalilin da yasa yake tsananin shakkar Mus’ab akan Salima ba.