A taimaka wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A cikin wannan mako mai ƙarewa jihohi da dama na arewacin ƙasar nan sun samu mamakon ruwan sama, wanda a dalilin haka aka fuskanci ambaliya mai tsananin gaske. Jihohi irin su Kano, Jigawa, Neja, da kuma Filato. A dalilin wannan ambaliya an samu asarar rayuka da dukiyoyi ciki kuwa har da amfanin gona da kayan abinci.

Tun kafin saukar damina, Hukumar Kula da Yanayin Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) ta fitar da rahoto kan yadda daminar bana za ta kasance, abin da ya tayar da hankalin jama’a da dama a ƙasar nan. Manazarta da masu hasashe kan muhalli sun yi ta jan hankalin ‘yan Nijeriya da hukumomi dangane da ƙalubalen da za a iya fuskanta na ambaliya, amma kamar yadda aka yi hasashe hukumomi a Nijeriya ba sa ɗaukar matakin rigakafi ko kariya don kiyaye afkuwar wani mummunan al’amari, sai abin ya faru ne sannan a fara neman yaya za a yi.

Bai wadatar ba a ce, Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, wato NEMA ta jira sai al’amura sun caɓe kafin a kai tallafi. Mai suka yi kafin afkuwar abin ta ɓangaren faɗakarwa da koyawa mutane dabarun yadda za su kare ƙauyukan su da muhallansu daga mamayar ambaliya? Waɗanne dabaru ne ya kamata ana amfani da su na kai ɗaukin gaggawa kafin hukumomi su kai jami’an ceto ko tallafi? Ina Hukumar Wayar Da Kan Jama’a ta NOA, wacce ke da rassa a dukkan jihohin ƙasar nan, mai ta yi wajen faɗakar da jama’a da nusar da su haɗarin da ke tafe?

Wannan al’amarin fa tuni an san da zai faru, ƙarfin da zai zo da shi, da ma wuraren da zai fi yi wa illa. Wannan hukuma ta yi nata aikin, yadda ya kamata. Mu ma a nan shafin AIKI DA HANKALI, mun yi iya irin namu faɗakarwar da gudunmawar a mun kuma ba da ‘yan shawarwarin da muke ganin za su yi amfani. Daga ciki idan za mu iya tunawa akwai batun, samar da matakan kariya kafin saukar ruwan sama. Sanya manyan buhuna masu cike da yashi ko ƙasa, don tare hanyoyin da ruwa zai iya bi ya shiga gidaje da unguwannin zaman jama’a. Gyara magudanun ruwa, yashe waɗanda suka cika da shara da datti, da gina sababbi a wuraren da babu su a baya.

Har wa yau mun yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su tashi tsaye wajen ganin an samar da wasu matakai na rigakafi, duk da ya ke dai a wasu jihohin damina ta fara sauka, manoma sun fara sharar gona. Shin yaya ake ciki game da batun samar da bishiyoyi da za su zama garkuwa a bakin gavar teku ko manyan rafuka, wanda bai yi tasirin da ake so ba? Wacce gudunmawa ya kamata ‘yan ƙasa su bayar don kare muhallansu da kewayensu?

Masana ilimin muhalli sun yi ta ƙorafi da bayyana damuwa kan yadda gwamnati ke jan ƙafa game da batun samar da kuɗaɗe a Asusun Kula da Gurɓacewar Muhalli, da aka tanada, domin magance irin waɗannan matsalolin da za su iya tasowa, kamar na yanzu da ake farkar da hukumomi haɗarin da ke tafe. A maimakon haka, kuɗaɗen da ake warewa suna zirarewa ne ta wasu wurare da ake ɓarnatar da su, ba don amfanin al’umma ba. Alhalin ya kamata a ce, an yi wani tanadi da za a yi amfani da shi a duk lokacin da wani mummunan al’amari ya faru ko yake daf da faruwa.

Ban manta ba mun bayyana buƙatar gwamnatin tarayya da ta jihohi da su himmatu wajen samar da matakan rigakafi, da wayar da kan jama’a ta kafafen watsa labarai da sauran hanyoyi na isar da saƙonni. Da kuma samar da muhallan da za a iya kwashe jama’a a ajiye su na wani lokaci, don kaucewa ɓarnar da ambaliyar za ta iya yi. Sannan har wa yau a samar da magunguna da ruwan sha mai tsafta, saboda kaucewa ɓarkewar annoba da yaɗuwar cututtuka. Gwamnati na buƙatar ƙara mayar da hankali kan tsare-tsaren ta na kare muhalli da yaƙi da gurɓacewar kewayen ɗan Adam, a gwamnatance.

Sai yanzu ne da mai faruwa ta kasance, aka fara ganin manyan jami’an gwamnati suna zavar dukiyar da tun a farko an yi amfani da ita wajen samar da kariya, suna kai ziyara da tallafin abin da ba zai iya zuwa ko’ina ba. Alhalin za a iya magance afkuwar sa ko rage kaifinsa.

Mun ji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana bayyana ɓacin ransa game da yadda aka bari abubuwa suka taɓarɓare har ambaliya ta yi wa mutane da dama illa. Ya bayyana cewa, kowacce jiha ana ware mata kuɗi don gudanar da ayyukan gaggawa, irin wannan wanda ya kamata shugabannin ƙananan hukumomi da gwamnoni su yi amfani da kuɗaɗen a shawo kan matsalar kafin ta wuce yadda za a iya tunkarar ta cikin sauƙi.

A yayin da muke jajentawa waɗanda bala’i ambaliyar ruwa ta shafa a dukkan sassan Nijeriya, muna kuma kira ga hukumomi da ƙungiyoyi su kai ɗaukin gaggawa, don sauƙaƙa halin da suke ciki. Da ɗaukar matakan rage illar da asarar da aka tafka ta amfanin gona za ta haifar ga ‘yan Nijeriya, a lokacin da ake kukan yunwa da rashin wadatar abinci a ƙasa.