Chelsea ta kori kocinta, Thomas Tuchel

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta kori kocinta Thomas Tuchel sakamakon rashin nasarar da ta yi a daren Talatar da ta gabata a gasar Zakarun Turai.

Tuchel mai shekara 49 kuma tsohon kocin Borussia Dortmund da Paris St-Germain, ya bar Stamford Bridge bayan watanni 20.

Mamallakin ƙungiyar, Todd Boehly ya sanya Tuchel a kan riƙon wucin gadi har zuwa lokacin da za a samu wanda zai maye gurbinsa.

Cikin sanarwar da ta fitar ranar Talata, Chelsea ta ce ta yi ammanar yanzu ne lokacin da ya dace ƙungiyar ta samu sabon kocin da ci gaba da jan ragamarta.

A ranar 26 ga Janairun 2021 ne Chelsea ta ɗauki Tuchel a matsayin kocinta inda ta maye gurbin Frank Lampard da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *