DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

Daga BASHIR ISAH

Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Malam Tukur Mamu a Bababban Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano.

Tun farko Mnahaja ta rawaito yadda jami’an tsaro suka tsare Mamu a birnin Alƙahira, babban birnin ƙasar Masar, inda daga nan aka dawo da shi Nijeriya.

Mamu ya ce shi da iyalansa suna kan hanyarsu ta zuwa Ƙasar Saudiyya ne inda aka tsare su na tsawon awa 24 a Alƙahira.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, jirgin da ya dawo da su Tukur Mamu ya sauka filin jirgin saman Kano ne da misalin ƙarfe 1:55 na rana, ranar Laraba.

Bayanai sun nuna an girke jami’an DSS a filin jirgin sama na Kano tun kafin isowar Mamu.

Wani ɗan uwan Tukur Mamu ya tabbatar wa majiyarmu cewa lallai jami’an DSS sun tsare Mamu da iyalansa, kuma sun kwashe su zuwa Abuja.

Tukur Mamu shi ne mawallafin jaridar nan ta Desert Herald, wanda kuma ya taka rawa wajen shiga tsakani don tattaunawa wajen kuɓutar da wasu da dama daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Da ma dai Mamu ya yi zargin cewa, gwamnatin Nijeriya ya yi wa rayuwarsa barazana.