06
Aug
Daga CMG HAUSA Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta ƙasar Sin, ta ce ƙasar zata gudanar da atisayen harba makamai daga yau 6 ga wata zuwa 15 ga wata, a yankin kudancin Rawayen teku dake gabashin ƙasar. Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce kazalika a yau Asabar, ana gudanar da atisayen soji a ɓangaren arewacin tekun Bohai, duk a gabashin ƙasar Sin. Fassarawar Fa’iza Mustapha
