31
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai ya nemi a yi watsi da ƙudirin da ke neman kafa dokar haramta sana’ar acaba a faɗin ƙasar nan. Yayin zamanta na ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar Jigawa a Jam’iyyar APC, Abubakar Yallemen ne ya gabatar da ƙudurin, inda ya buƙaci su yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin da take yi na haramta sana’ar acaɓa a faɗin ƙasar nan. Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa, ɗan majalisar ya buƙaci a tabbatar da an samar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen rage wa ‘yan qasa raɗaɗin haramta…
