Editor

9513 Posts
Yunƙurin tsige Buhari ɓata wa kanku lokaci ne – Garba Shehu ga sanatoci

Yunƙurin tsige Buhari ɓata wa kanku lokaci ne – Garba Shehu ga sanatoci

Daga AISHA ASAS  Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta maida martani ga sanatocin jam’iyyar hamayya ta PDP da suke yi wa Shugaba Muhammadu Buhari barazanar tumɓuke shi.  Blueprint ta ce, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi a ranar Alhamis a matsayin martani.  Garba Shehu ya kuma yabi shugaban majalisar dattawa wanda ya takawa sanatocin burki, inda Garba Shehu ya bayyana cewa, Ahmad Lawan ya yi abin da ya kamata.  A jawabin da ya fitar, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ce, sanatocin PDP da suka fice daga majalisa saboda maganar, sun nuna…
Read More
Tsaleliyar budurwa ta yi wuf da Sarkin Daura bayan soyayyar mako guda

Tsaleliyar budurwa ta yi wuf da Sarkin Daura bayan soyayyar mako guda

Daga AISHA ASAS a Abuja Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya auri wata tsaleliyar budurwa ’yar shekara 22 mai suna Aisha Yahuza Gona mako guda bayan fara soyayyarsu. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an ɗaura auren ne a garin Safana da ke Jihar Katsina a cikin yanayi na rashin tara ɗimbin jama’a a wajen shagalin, duk da cewa, amaryar ɗiya ce ga tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Safana, Alhaji Yahuza Gona. An bayar da rahoton cewa, Mar Martaba Sarkin, wanda a farkon shekarar nan ya yi bikin cikarsa shekara 15 a gadon sarauta, ya auri ’yar shekara…
Read More
Yaushe Ganduje zai zartar da hukunci kan makashin Hanifa? …Bayan kotun Kano ta yanke wa makashin Hanifa hukuncin rataya

Yaushe Ganduje zai zartar da hukunci kan makashin Hanifa? …Bayan kotun Kano ta yanke wa makashin Hanifa hukuncin rataya

*Lokacin da gwamna ke da ikon saka hannu kan hukuncin – Lauya Daga MAHDI M. MUHAMMAD A jiya ne Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 6 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako da ke Birnin Kano a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na’abba ta yanke wa malamin makarantar nan da aka kama da aikata laifin kisan ɗalibarsa, Hanifa Abubakar, wato Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da laifin yin garkuwa da ita da kuma kisan ta. Haka kuma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyar, saboda samun sa da laifin haɗa baki da kuma…
Read More
Kasuwanci ɓangaren da ba na masana’antun ƙira ba a Sin ya ci gaba da farfaɗowa a watan Yuli

Kasuwanci ɓangaren da ba na masana’antun ƙira ba a Sin ya ci gaba da farfaɗowa a watan Yuli

Daga CMG HAUSA Haɗaɗɗiyar ƙungiyar jigilar kayayyaki da ta masu sayayya ta ƙasar Sin da cibiyar binciken ayyukan hidima ta hukumar ƙididdiga ta ƙasar, sun sanar a yau Lahadi da cewa, alƙaluman harkokin kasuwanci da ba na masana’antun kira ba, sun kai kaso 53.8 bisa ɗari a watan Yuli, adadin ya ƙaru da kaso 0.5 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin a bara, wato ya kai sama da matsakaicin matsayin rabin farkon bana. Alƙaluma game da ma’aikatan harkokin kasuwancin ba ta sauya sosai ba, kuma ayyukan hidima na ci gaba da farfaɗowa. A taƙaice dai, ana…
Read More
An buɗe rumbun adana wallafe-wallafe da al’adun gargajiya na Ƙasar Sin

An buɗe rumbun adana wallafe-wallafe da al’adun gargajiya na Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA An ƙaddamar da ginin rumbun adana wallafe-wallafe da al’adun gargajiya na ƙasar Sin a jiya a Asabar. Ginin wata muhimmiyar alama ce ta al’adun gargajiya a sabon zamani, haka kuma cibiyar adana al’adun gargajiya ta ƙasar Sin. Bayan buɗewar, zai gudanar da ayyukan wallafa da adana muhimman kayayyaki da al’adun gargajiya da aka yi gado. Babban ɗaki mai lamba 1 na ginin, ya ƙaddamar da jerin nune-nune na musammam bisa taken raya tarihin Sinawa da ci gaban wayewarsu. Haka kuma yana haska sauye-sauyen tarihi da shaida nasarorin da aka cimma. Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
Read More
Ƙungiyar NAF ta yi martani ga matasan Arewa masu yekuwar a tsige Janar Monguno

Ƙungiyar NAF ta yi martani ga matasan Arewa masu yekuwar a tsige Janar Monguno

Daga WAKILINMU Ƙungiyar Arewa Ina Mafita ta yi kakkausan martani ga wata ƙungiyar matasan Arewa mai suna ‘Arewa Youth Assembly bisa kira da suka yi na murabus din mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsrao, Janar Babagana Mongonu. Rahotanni sun ruwaito kakakin ƙungiyar, Mohammed Danlami ne ya yi wannan kira a wata takardar sanarwar manema labarai da ya rattaba wa hannu a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda ƙungiyar tasu ta nemi Janar Monguno da ya yi ritaya ko Shugaba Buhari ya tsige shi. Sai dai a yayin mayar da martani ga wannan matsaya ta Ƙungiyar Matasan, Kungiyar…
Read More
Rundunar sojin saman Ƙasar Sin ta lashi takobin kare cikakken ‘yanci da yankunan ƙasar

Rundunar sojin saman Ƙasar Sin ta lashi takobin kare cikakken ‘yanci da yankunan ƙasar

Daga CMG HAUSA Rundunar sojin saman ƙasar Sin, ta ce haƙƙi ne kan kowanne sojan samar ƙasar, ya kare yankuna da ikon ƙasarsa. Kakakin rundunar Shen Jinke ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da aka yi yau Lahadi. A cewarsa, ƙudurin rundunar ne kare cikakken ‘yanci da yankunan ƙasar Sin, bisa jajircewa da dogaro da kai. Fassarawar Fa’iza Mustapha
Read More
Tsadar fulawa da kayan haɗi: Gidajen burodi sun sanar da sabon farashinsu

Tsadar fulawa da kayan haɗi: Gidajen burodi sun sanar da sabon farashinsu

Daga AMINA YUSUF ALI Masu gidajen burodi a Nijeriya sun bayyana yadda farashin biredi zai tashi nan gaba. Sabon farashin ana sa ran zai fara daga ranar Litinin ɗin da ta gabata wato 25 ga Yuli, 2022. Rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu haka ma farashin biredin ya jima da tashi a wasu jihohin saboda abinda suka alaƙanta da tsadar fulawa da kayan haɗin burodin a Nijeriya. Rahotanni daga jihar Kogi sun bayyana cewa, tuni masu gidajen burodin suka ƙara farashin biredin da ƙarin kaso 20% a kan tsohon farashinsa. Wannan ƙarin farashin ya biyo bayan yakin aikin ƙasa bakiɗayan…
Read More
Batun haramta babura da haƙar ma’adanai a faɗin Nijeriya

Batun haramta babura da haƙar ma’adanai a faɗin Nijeriya

A wani yunƙuri na shawo kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar, gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na sanya dokar hana amfani da babura da ma’adanai a faɗin tarayyar ƙasar nan. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyana hakan kwanan nan. A cewarsa, irin wannan matakin zai kawar da hanyoyin samun kuɗaɗe ga 'yan ta'adda da kuma 'yan fashin daji a Nijeriya da ke amfani da kuɗaɗen da ake samu daga waɗannan kafofin wajen ƙarfafa ayyukansu na aikata laifuka. Malami ya ci gaba da cewa, waɗannan kayan aikin da ’yan ta’addan ke…
Read More
Gwamna Ganduje ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamna Ganduje ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar 1 ga watan Augusta shekara ta 2022 a matsayin ranar hutun domin murnar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445 bayan hijrah. Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bada wannan umarnin cikin sanarwar da Kwamishinan Ma'aikatar Yaɗa Labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya rattaɓawa hannu, don haka,  sai ya taya al'ummar Musulmin Jihar Kano murna bisa muhimmancin wannan rana tare da buƙatar yi wa kai hisabi. Ya kuma buƙace su da su yi amfani da wannan hutu wajen neman gafarar Allah, tare da roƙon Allah ya…
Read More