Editor

9513 Posts
An yanke masa hukuncin shekara 2 a gidan yarin saboda harƙallar Kirifto Karansi a Legas

An yanke masa hukuncin shekara 2 a gidan yarin saboda harƙallar Kirifto Karansi a Legas

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai wata kotun laifuka na musamman dake Ikejan jihar Legas ta yanke hukuncin shekara biyu a gidan yarin ga wani ɗan kasuwar canji da aka kama da laifin harƙallar Kirifto Karansi wanda ya kai darajar Naira miliyan 20. A ranar Talatar da ta gabata ne dai Alƙalin kotun Mai shari'a, Oluwatoyin Taiwo ya yanke wa wani ɗan canji mai suna Shola Henry hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyu bayan saninsa da Laifuka iri-iri har guda biyu da kotun take tuhumasa da su. Hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin…
Read More
Yaushe Amurka za ta cika alƙawarin da ta yiwa ƙasar Sin?

Yaushe Amurka za ta cika alƙawarin da ta yiwa ƙasar Sin?

Daga CMG HAUSA Mamban hukumar siyasar kwamitin ƙolin JKS kuma darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin Yang Jiechi ya gana da mai taimakawa shugaban ƙasar Amurka kan tsaron ƙasa Jake Sullivan a Luxembourg a Litinin da ta gabata har na tsawon awoyi huɗu, inda suka yi tattaunawa mai zurfi, tare kuma da amincewa da tabbatar da matsaya guda da shugabannin ƙasashen biyu wato Sin da Amurka suka cimma. Yanzu hulɗar dake tsakanin sassan biyu ta gamu da matsala, sakamakon ƙasa tabbatar da matsayar da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma, duk da cewa, ƙasar Sin ta nuna sahihanci…
Read More
Xi Jinping ya tattauna da Putin ta wayar tarho

Xi Jinping ya tattauna da Putin ta wayar tarho

Daga CMG HAUSA A yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin na son hada kai tare da ƙasar Rasha, wajen inganta hadin gwiwarsu ta hanyar da ta dace. Ƙasar Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga ƙasar Rasha kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, da manyan batutuwan da suka shafi harkokin ikon mulkin ƙasa, da tsaro, da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin ƙasashen biyu, da ƙarfafa tattaunawa da yin haɗin gwiwa…
Read More
Shiru-shiru ba tsoro ba ne…

Shiru-shiru ba tsoro ba ne…

Daga IBRAHIM YAYA A duk lokacin da aka kira taruka kama daga na tattalin arziki, al’adu, ko wasanni ko Ilimi ko kare muhalli ko harkar tsaro, walau a mataki na ƙasa ko shiyya ko ƙasa da ƙasa, muhimman abubuwan da mahalarta tarukan ke tattaunawa, su ne matsaloli da nasarori da aka cimma a waɗannan fannoni, gami da sabbin dabaru ko matakai da aka bijiro da su don inganta su, wadda daga ƙarshe za su taimaka wajen haifar da kyakkyawan sakamako da ma burin da ake fatan cimmawa, wanda zai amfani duniya baki ɗaya. Sai dai wani abin mamaki shi ne,…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari zai ziyarci Kano gobe

Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari zai ziyarci Kano gobe

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyara Jihar Kano a gobe Alhamis, 16 ga watan Yuni, 2022. Hakan na cikin saƙon da mai taimaka wa Shugaban Ƙasar kan sabbin kafafen sadarwa, Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Laraba. Bashir Ahmad ya ce, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai je Jihar Kano ne domin halartar taron bikin yaye sabbabbin jami’an 'yan sanda a Kwalejin Horas da 'Yan Sandan da ke garin Wudil a jihar.
Read More
Tambaya ga ‘yan siyasa: Cin amana ko Khiyana?

Tambaya ga ‘yan siyasa: Cin amana ko Khiyana?

Daga ABDULLAHI I. MAHUTA So da yawa, bayan kammala zaɓuɓɓuka, za ka ji 'yan siyasa, musamman ma waɗanda Allah ya hukunta ba su ke da nasara ba, su na amfani da kalmar "an ci amana ta" wajen ba da dalilin da ya sa ba su samu nasara ba. A maimakon yin tawakkali ta hanyar rungumar hukuncin da Allah ya hukunta musu. Abin tambaya a nan shi ne: shin menene ma'anar wannan kalma ta AMANA da 'yan siyasa suke yawan ambato? Wadda ita ce kuma suke yawan zargi a dalilin rashin samun nasararsu. Amana dai kalma ce ta Larabci. Hakanan kuma…
Read More
Tsakanin Mahukunta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da gwamnati wai waye ba ya tausayin talaka?

Tsakanin Mahukunta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da gwamnati wai waye ba ya tausayin talaka?

Daga FAUZIYYA D. SULAIMAN Asibitin Malam Aminu Kano, yana ɗaya daga cikin mafakar da talaka ke samu ya fake idan ciwo ya yi tsanani, domin daga asibitin Murtala da Asibitin Nasarawa kai da duk wani asbiti a kano har da asibitocin kuɗi nan ne ƙarshen gurin da za a tura mara lafiya, daga nan kuwa sai dai mutuwa, sai dai idan kana da hali ka fita ƙasar waje. A ƙarƙashin ƙungiyarmu ta 'creative helping needy foundation' , nan ne asibitin da kai tsaye muke iya kai marasa lafiyarmu a duba su cikin kwanciyar hankali da kuma gaggawa. Don haka, kaso…
Read More
Ya kai ɗan Kwankwasiyya, bai kamata ka maimaita kuskure iri ɗaya sau biyu ba!

Ya kai ɗan Kwankwasiyya, bai kamata ka maimaita kuskure iri ɗaya sau biyu ba!

Daga ABDULAZIZ T. BAƘO Ya kai ɗan Kwankwasiyya, a shekarar 2019, Kwankwasiyya ta nuna maka ɗan takarar da za ka zaɓa a matakin shugaban ƙasa, da gwamna, da 'yan majalisu, da sanatoci, amma ka ƙeƙashe ƙasa ka ce kai ina! "Cancanta," bisa ra'ayin son zuciyarka da abinda ka ji mutanen gari suna faɗa, za ka zaɓa. Ina ga ko ban faɗa maka ba, ka san irin tozarci da cin mutuncin da wannan ra'ayin naka na bin abinda ka kira "cancanta" ya jawo wa Kwankwasiyya, wanda in dai kai ɗan kwankwasiyyar ne na gaske, to tabbas an yi abubuwa da yawa…
Read More
Lokaci ya yi da ya kamata mata su zama jagaba a al’amuran ƙasa-Honorabul Habiba Balarabe

Lokaci ya yi da ya kamata mata su zama jagaba a al’amuran ƙasa-Honorabul Habiba Balarabe

"Don samun damar ci gaba da agaza wa al’umma ne na shiga siyasa" Honorabul Habiba Balarabe Liman, gogaggiyar ‘yar siyasa a Jihar Nasarawa da ƙasa bakiɗaya. Ta taɓa fitowa takarar kujerar mamba mai wakiltar mazaɓar Keffi da Kokona da Karu a Majalisar Wakilai ta Tarayya. A yanzu ita ce mataimakiyar gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ta musamman. A zantawarta da wakilinmu, ta bayyana tarihin rayuwanta, inda ta kuma buƙaci ‘yan'uwanta mata a jihar da ƙasa bakiɗaya su yi amfani da yawansu wajen ƙwato 'yancinsu da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Daga JOHN D. WADA, Lafiya MANHAJA: Mu fara…
Read More
Siyasar kuɗi ba alheri ba ce ga Nijeriya

Siyasar kuɗi ba alheri ba ce ga Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Hada-hadar siyasa na cigaba da kankama gadan-gadan a Nijeriya. Kawo yanzu dai akasarin jam'iyyun siyasar ƙasar nan sun kammala gudanar da zavukan su na fitar da gwanayen ’yan takarar da za su tsaya ƙarƙashin tutar su, don neman muƙamai a matakai daban-daban, daga kan gwamnoni, majalisun dokoki na jihohi, zuwa Majalisar Ƙasa a ɓangaren Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Dattawa, da Shugaban Ƙasa. Manyan jam'iyyun APC da PDP dai har yanzu su ne suka fi jan hankalin jama'a, yayin da aka samu farfaɗowar wasu ƙananan jam'iyyun da jama'a suke kallon su a matsayin tudun talakawa,…
Read More