Tambaya ga ‘yan siyasa: Cin amana ko Khiyana?

Daga ABDULLAHI I. MAHUTA

So da yawa, bayan kammala zaɓuɓɓuka, za ka ji ‘yan siyasa, musamman ma waɗanda Allah ya hukunta ba su ke da nasara ba, su na amfani da kalmar “an ci amana ta” wajen ba da dalilin da ya sa ba su samu nasara ba. A maimakon yin tawakkali ta hanyar rungumar hukuncin da Allah ya hukunta musu.

Abin tambaya a nan shi ne: shin menene ma’anar wannan kalma ta AMANA da ‘yan siyasa suke yawan ambato? Wadda ita ce kuma suke yawan zargi a dalilin rashin samun nasararsu.

Amana dai kalma ce ta Larabci. Hakanan kuma kalma ce ta addinin musulunci. Saboda haka, bari mu gano ma’anar wannan kalma ta AMANA luggatan da kuma Istilahan. Watau ma’anar ta a larabci da kuma a shari’ance.

A Larabce, kalmar AMANA ta samo asali ne daga kalmar ‘Al-amnu’. Ita kuma wannan kalma ta ‘Al-amnu’, tana nufin samun natsuwa, kwanciyar hankali ko rashin tsoro. Watau mutun ya samu natsuwa, kwanciyar hankali ko aminci daga wani nau’i na zalunci, yaudara, ha’inci ko cutarwa daga arzikin mai arziki, zaluncin azzalumi, yaudarar mayaudari, wayon mai wayo ko fin ƙarfin mai ƙarfi.

Idan kuma muka koma ta shari’a, wannan kalma ta AMANA, tana nufin badawa, saukewa ko kiyaye dukkan wani nauyi, haƙƙi ko wata ƙa’ida ko doka dake kan mutum. Saboda haka, tun da mun fahimci ma’anar AMANA a luggatan da kuma a shari’ance, to bari mu kuma kalli abinda mu ‘yan siyasa ke kira da “cin amana”

Mulkin dimokiraɗiyya ko siyasa, an gina shi ne bisa tsarin cewa al’umma ko talakawa, su ne za su zabar wa kansu shugabannin da za su jagorance su ba tare da tursasawa ba. A dalilin haka ne doka ta tanadi cewa idan zaɓen ya matso, mutanen kowace jamiyya su je su zavi wakilansu waɗanda za su wakilce su a lokacin gudanar da zaɓen fidda gwani. Idan kuma an je wajen zaɓen fidda gwani, kowane daliget ya zabi ɗan takarar da ya gamsu da aƙidunsa tsakaninsa da Allah ba tare da tursasawar wasu manya ba ko kuma amsar cin hanci ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko a bisa irin wannan tsari siyasar ƙasarmu take gudana?

A Nijeriya kowa ya san cewa da farko dai su waɗannan daliget-daliget ɗin ba zaɓar su ake yi ba. Wasu manya ne ke zama su rubuta sunan wasu yaransu da nufin su ba su umurnin yin abinda su manyan suke so. Na biyu kuma, idan an je wurin zaven fidda gwani, akan zauna ne a wata mavoya ta sirri, a yi yarjejeniya da su a kan yawan kuɗin da za a ba su domin zavar shi wanda ya ba su kuɗin. To saɓa wa irin wannan yarjejeniya, musamman idan aka samu wani ɗan takara da ya ba da kuɗin da suka fi na farko, shi ‘yan siyasar mu ke kira da ‘cin Amana’.

Tambaya ta biyu ita ce, a shari’a ta Musulunci, a iya kiran irin wannan yarjejeniya da ake ƙullawa a tsakanin yan takara da daliget ko wasu dayawa jam’iyya a matsayin an ƙulla AMANA wadda Allah (swt)i ya aminta da ita? Shin ko saɓa wa irin wannan yarjejeniya zai iya zama cin amana, wadda Allah na iya hukunci a kan wanda ya saɓa wa wannan yarjejeniyar?

A musulunci, ba a ƙulla amana domin aikata haram. Irin wannan yarjejeniya da mutane ke kullawa domin aikata haram ko ƙoƙarin kauce wa, ko saɓa wa wata ƙa’ida da aka yarda da ita a musulunci sunan ta KHIYANA. Abinda ake ce wa KHIYANA kuwa, shi ne HA’INCI.

Abdullahi I. Mahuta, ɗan siyasa ne, kuma mai sharhin kan al’amuran siyasa da mulki. Ya rubuto daga Malumfashi, jihar Katsina.