Tsakanin Mahukunta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da gwamnati wai waye ba ya tausayin talaka?

Daga FAUZIYYA D. SULAIMAN

Asibitin Malam Aminu Kano, yana ɗaya daga cikin mafakar da talaka ke samu ya fake idan ciwo ya yi tsanani, domin daga asibitin Murtala da Asibitin Nasarawa kai da duk wani asbiti a kano har da asibitocin kuɗi nan ne ƙarshen gurin da za a tura mara lafiya, daga nan kuwa sai dai mutuwa, sai dai idan kana da hali ka fita ƙasar waje.

A ƙarƙashin ƙungiyarmu ta ‘creative helping needy foundation’ , nan ne asibitin da kai tsaye muke iya kai marasa lafiyarmu a duba su cikin kwanciyar hankali da kuma gaggawa. Don haka, kaso kusa 70% na marasa lafiyarmu nan asibitin muke kai su.

Amma yanzu abun takaici komai na asibitin ya ninka farashinsu sau biyu har zuwa kashi huɗu. Misali, a baya kuɗin ganin likita Naira ɗari shida muke biya, yanzu ya koma dubu biyu da ɗari ɗaya. Kuɗin buɗe fayal daga 500, ya koma 1000. Kuɗin gado kwanaki biyar daga dubu ashirin ya koma dubu arba’in. Kuɗin tiyata idan mace za ta haihu daga dubu saba’in da biyar ya koma dubu ɗari biyu da hamsin har ma fiye da hakan wani lokacin. Yanzu wata ƙanwata a satin nan da naƙuda ta kama ta mai haɗari aka ce aiki za a yi mata an kashe kuɗi kusan dubu ɗari uku da wani abu. Ya Ilahi, ta ina talaka zai iya biyan wannan kuɗin?

Babban tashin hankalin kuma duk sauran asibitocin irin su Murtala da Nassarawa da Kuroda da sauransu, an musu taron dangin da za ka iya zuwa sau goma a ce maka babu gado. Don ƙanwar tawa haka aka dinga yawo da ita cikin naƙuda kusan asibiti biyar ana cewa babu gado, ƙarshe aka ga za ta iya rasa ranta aka tafi asibitin Malam Aminu Kano. Ana zuwa suka ce sai an bayar da dubu arba’in na gado, sannan kuɗin aiki, dubu ɗari biyu da sittin. Babu zaɓi, domin idan ba a yi aikin ba, za ta iya mutuwa. Don haka, dole suka yadda a yi aikin a haka.

Yanzu ta kai kusan wata guda ana ta turo min marasa lafiya ina gani na kasa wallafawa a shafukan yanar gizo, saboda ga rashin kuɗi a hannun mutane, ga tsadar asibiti. Wallahi marasa lafiyar da ke roƙo na yanzu ko saƙonsu bana iya buɗewa. Shekaranjiya wata zagi na ta dinga yi a saƙon kar-ta-kwana wai ana kirana na ƙi ɗagawa, ina wulaƙanta su, ni ɗin banza? Sai haƙuri na ba ta domin na san tana cikin damuwar rashin lafiyar ɗan’uwanta ne.

Yanzu idan ka je asibitin Malam za ka ga babu mutane domin da yawa ba za su iya biya ba. Wani ɗan yayata kwanaki da ya yi haɗari, kwanansa biyar a Asibitin suka nemi sallama. Ba don ya warke ba, domin ba za su iya biyan kuɗin ba, komai nasu ya ƙare.

Amma bayan bincike da muka yi na dalilin wannan tashi da komai ya yi, sai aka sanar da ni wai asibitin sun ƙara kuɗaɗen ne saboda ba a samun wutar Lantarki sai Diesel suke siya. Kuma kusan kullum wai sai sun sayi na miliyan guda ko ma fiye da haka kafin su iya ayyukansu. Don haka, ba su da zaɓin da ya wuce su ƙara kuɗaɗen a kan talaka.

Yanzu marasa lafiyarmu da ke biniyarmu, irin su Zakiyya (Mai ciwon nono); da Iyami mai shekaru uku da sauransu, sama da marasa lafiya guda ashirin duk abunda muka ajiye nasu ya ƙare. Ga wasu kuma a kan layi, mun rasa yaya za mu yi da su. Wasu sai mutuwa suke yi kafin ma a ce mun yi wallafa a shafin yanar gizo.

Ban san wacce irin ƙasa muke ba da babu abunda ya damu shugabanninmu da mu ba, domin babu wanda na tava ji ya yi magana a kan wannan matsalar. Da mu rayu, da mu mutu, duk uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya a gurinsu.

Don haka, muna kira da babbar murya ga waɗanda abin ya shafa, musamman shugabanni. Ku duba halin da asibitin Malam Aminu ke ciki ku kawo mana ɗauki, don Allah don Annabi. Domin idan ba a ɗauki mataki ba, mutane za su ci gaba da mutuwa kullum, saboda babu yadda za su iya biyan waɗancan kuɗaɗe. Wani a kan dubu biyu da zai ga likitan kawai sai a rasa ransa, mutanen da kuɗin motar da za su zo asibitin ba su da shi?

Ina kuma kira ga masu turo marasa lafiya da su yi haƙuri. Wallahi babu yadda zan yi ne, ni na fi son a ce kullum na yi fostin mara lafiya ya samu sauƙi, Allah ka kawo ɗauki amin.

Fauziyya D. Sulaiman arubuciya ce, kuma shugaban qungiyar Tallafa wa gajiyayyu a Kano.