Editor

9513 Posts
Zaɓen PDP: Wike ya fice daga zauren taro bayan da aka bayyana Atiku a matsayin wanda ya yi nasara

Zaɓen PDP: Wike ya fice daga zauren taro bayan da aka bayyana Atiku a matsayin wanda ya yi nasara

Daga WAKILINMU Ɗan takarar Shugaban Kasa ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Gwamna Nyesom Wike, ya fice daga zuren da PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani a daidai lokacin da Alhaji Atiku Abubakar ke gabatar a jawabin amincewar nasarar da ya samu. Alamu sun nuna Wike ya fice daga wajen zaɓen ne saboda rashin jin daɗin sakamakon zaɓen wanda Atiku ya samu nasara a kansa. A ranar Asabar da ta gabata Jam'iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani a Babban Dilin Wasannin Motsa Jiki da ke Abuja don tsayar da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023. Da yake jawabi…
Read More
ASUP ta janye yajin aikinta, ta buƙaci malamai da su dawo bakin aiki

ASUP ta janye yajin aikinta, ta buƙaci malamai da su dawo bakin aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Ƙasa (ASUP) ta janye yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta yi, inda ta buƙaci ɗaukacin malaman da su koma ranar 30 ga Mayu, 2022. Hakan ya fito ne daga bakin sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa, Abdullahi Yalwa. A cewarsa, ƙungiyar na buƙatar mambobin ƙungiyar da su dawo bakin aiki daga ranar 30 ga watan Mayu, 2022, tare da fatan gwamnati za ta yi amfani da damar da aka ba ta don magance abubuwa biyar da ake neman a wajenta. A ranar 16 ga Mayu, 2022, ƙungiyar ta fara…
Read More
Tinubu ya taya Atiku murna

Tinubu ya taya Atiku murna

Daga SANI AHMAD GIWA Jagoran Jam’iyyar APC mai mulki kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Atiku Abubakar murnar nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na PDP babbar jam’iyyar hamayya. Tinubu kuma ya bayyana fatansa na kasancewa abokin hamayyar Atiku a zaɓen 2023. A ranar Asabar PDP ta zaɓi Atiku a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa. Atiku shi ya fafata da Buhari a zaɓen 2019. Tinubu, duk da ya yaba da yadda jam’iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fitar da gwaninta a ranar Asabar, amma ya ce jam’iyyar na da ƙalubale a gabanta domin har yanzu…
Read More
Zaɓen fidda gwanin PDP: Yadda kowane daliget ya tashi da Dala 50,000

Zaɓen fidda gwanin PDP: Yadda kowane daliget ya tashi da Dala 50,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An ruwaito cewa wakilan Jam'iyyar PDP wato daliget masu zaɓen fidda gwanin ɗan takarar Shugaban Ƙasa a babban taron da ya gudana ranar Asabar a filin wasa na Mashood Abiola da ke Abuja, kowane daliget ya cika aljihunsa da kimanin Naira miliyan 29,900,000, kwatankwacin dala 50,000 wanda 'yan takarar suka yi masu yayyafinsu a matsayin la'ada ko saye ƙuri'arsu. Kafin nan, an ji cewa ɗaya daga cikin masu neman jam'iyyar ta tsayarsu, Mohammed Hayatu-Deen ya janye takararsa, inda ya ce zai cigaba da bai wa jam'iyyar tasu goyon baya don kai ga nasara a…
Read More
Mai sha’awar takarar gwamnan Sakkwato a PDP ya fice daga jam’iyyar

Mai sha’awar takarar gwamnan Sakkwato a PDP ya fice daga jam’iyyar

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗaya daga cikin waɗanda suka so tsayawa jam'iyyar PDP takarar Gwamna a Sakkwato, Barrister Mukhtari Shehu Shagari ya sanar da ficewa daga jam'iyyar a cikin wani bayani da ya fitar wa manema labarai a Sakkwato, yana mai cewar jam'iyyar ta mutu murus a Sakkwato. A cewar sa ɗaukar matakin ya biyo bayan irin salon takun jam'iyyar da ya yi hannun riga da tanadin dimukuraɗiyya, duk kuwa da cewa ya shafe lokaci yana hidimta wa jam'iyyar tun a shekarar 1998, a cewarsa. Muhtari wanda ya nuna damuwarsa kan yadda Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya…
Read More
Dokar zaɓe na cigaba da kaɗa hantar gwamnoni

Dokar zaɓe na cigaba da kaɗa hantar gwamnoni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ganin rashin amincewa da gyaran sashe na 84 (8) na dokar zaɓe da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi, gwamnonin Nijeriya sun shiga ruɗu a ƙoƙarinsu na ganin sun samar da waɗanda za su gaje su da kuma isar da jihohinsu ga masu son tsayawa takarar shugaban ƙasa. Rahotanni sun nuna cewa, wasu gwamnonin na ƙorafin rashin halartar zaɓukan fidda gwani savanin a baya. Akwai kuma fargabar cewa gwamnonin na iya rasa ikonsu a kan wakilan jam’iyyu na jihohi, musamman a lokacin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa. A halin yang dai ’yan takarar…
Read More
Zaɓen fidda gwani: Za mu kwatanta adalci a APC – Adamu

Zaɓen fidda gwani: Za mu kwatanta adalci a APC – Adamu

*Shugaban APC ya yi magana kan ɗan takarar masalaha da karɓa-karɓa*Dokar zaɓe na cigaba da kaɗa hantar gwamnoni*Yadda ta kaya a zaɓen fidda gwanin PDP a Borno da Yobe*Kada ku mayar da zaɓen fidda gwani na a-mutu-ko-a-yi-rai, inji Gwamna Masari Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yayin da jam’iyyun Nijeriya za su ƙarƙare gudanar da zaven fitar da gwani na masu neman kujerar Shugaban Ƙasa a ƙarshen makon nan, Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce, jam’iyyar za ta yanke shawara kan batun shiyya-shiyya bayan ta tantance masu neman shugabancin ƙasar a 2023, ya na mai cewa, shugabannin…
Read More
Jirigin ƙasan Abuja-Kaduna: A gaggauta sako mana ’yan uwanmu, inji dangin waɗanda aka sace

Jirigin ƙasan Abuja-Kaduna: A gaggauta sako mana ’yan uwanmu, inji dangin waɗanda aka sace

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Iyalai da dangin waɗanda ’yan bindiga su ka sace a hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun bayyana damuwarsu akan irin halin da ’yan uwansu ke ciki a hannun masu garkuwar, inda suka ce a gaggauta a sako su. Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da suka fitar cikin makon nan. Sanarwar ta ce, “a jiya, mun sami labari mai firgitarwa daga waɗanda suka sace fasinjojin jirgin Ak9 da suka taso daga Abuja ranar 28 ga Maris, 2022 da qarfe 6:10 na yamma zuwa Kaduna amma ba su kai ga inda aka nufa ba.”…
Read More
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da Janar Gowon

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da Janar Gowon

Daga CMG HAUSA Jakadan ƙasar Sin a tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya gana da tsohon shugaban gwamnatin sojan ƙasar Yakubu Gowon, wanda ya taba ba da gagarumar gudummowa ga ci gaban huldar diplomasiyyar tsakanin ƙasashen biyu. Jakada Cui ya bayyana cewa, a halin yanzu, hulɗar dake tsakanin Sin da Najeriya tana gudana yadda ya kamata ƙarƙashin ƙoƙarin da gwamnatoci da al’ummomin sassan biyu suke yi, kana ƙasashen biyu suna goyon bayan juna a fannin siyasa, kuma suna taimakawa juna wajen ci gaban tattalin arziki da cinikayya. Ya ce a nan gaba, ƙasar Sin tana son hada hannu da Najeriya domin…
Read More
Rundunar sojin Sin ta kira taro kan yanayin tsaroa gaɓar tekun Guinea

Rundunar sojin Sin ta kira taro kan yanayin tsaroa gaɓar tekun Guinea

Daga CMG HAUSA Shugaban sashen watsa labarai na ma’aikatar tsaron ƙasar Sin kuma kakakin ma’aikatar Wu Qian, ya ce rundunar sojin ƙasar Sin ta kira taron ƙara wa juna sani ta kafar bidiyo, kan yanayin tsaron gaɓar tekun Guinea, domin tabbatar da shawarar tsaron duniya da tunanin kafa kyakkyawar makoma a kan teku, da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Tare kuma da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakanin rundunar sojin Sin da na ƙasashen dake gaɓar tekun Guinea, kan tabbatar da tsaro a kan teku. Taken taron shi ne, “tabbatar da tsaro a gabar tekun Guinea, ta hanyar…
Read More