Editor

9513 Posts
Sabuwar manufar Amurka kan Sin ba ta canja tunaninta na yakin cacar baka da fin ƙarfi ba

Sabuwar manufar Amurka kan Sin ba ta canja tunaninta na yakin cacar baka da fin ƙarfi ba

Daga CMG HAUSA Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya gabatar da wani jawabi game da manufar ƙasarsa kan ƙasar Sin a jami’ar George Washington a ranar 26 ga wata, inda ya bayyana cewa, Amurka tana aiwatar da manufar “zuba jari da hada kai da yin takara” kan ƙasar Sin, amma kafin hakan, ya taba bayyana cewa, manufar ita ce: “takara da haɗin gwiwa da nuna ƙiyayya”. Duk da cewa, akwai bambanci kaɗan tsakaninsu, ainihin yanayin da Amurka ke ciki shi ne, ta gamu da cikas yayin da take matsawa ƙasar Sin lamba. Amurka ba ta sauya tunaninta na yakin…
Read More
Zaɓen fidda gwanin PDP: Tambuwal ya janye wa Atiku

Zaɓen fidda gwanin PDP: Tambuwal ya janye wa Atiku

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Sakkwato kuma ɗan takarar Shugaban Kasa a ƙarƙashin Jayyar PDP, Aminu Tambuwal, ya bayyana janyewarsa daga takarar shugabancin Nijeriya. Tambuwal ya bayyana janyewar tasa ne sa''ilin da yake bayani wajen taron zaɓen fidda gwani na Jam'iyyar PDP ranar Asabar a Abuja. Tambuwal ya bayyana dalilin janyewarsa da cewa, “Lokaci ya zo da za mu nuna sadaukarwa don cigaban jam'iyyarmu da kasarmu. Don haka, na yanke shawarar janye takararta." Bayan ɗaukar matakin janyewar, Tambuwal ya buƙaci duka daliget da ma magoya bayansa a haɗu a mara wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar baya.
Read More
Yari, Marafa da Sahabi sun lashe zaɓe ƙarƙashin APC

Yari, Marafa da Sahabi sun lashe zaɓe ƙarƙashin APC

Daga SANUSI MUHAMMAD aGusau. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, Sanata Kabiru Garba Marafa da kuma Sanata Sahabi Ya'u a yau sun lashe zaɓen zama yantakarar majalisar dattawa ƙarƙashin Jam'iyyar APC. Zaɓen da aka gudanar cikin lumana ya samu halartar Gwamna Bello Mohammed Matawalle. Tsohon gwamnan Abdulaziz Yari ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, India yasamu ƙuri'u 306 ƙuri'u daga cikin wakilai 310 da suka fito daga mazaɓu 62 a yankin. Hakazalika, zaɓen an gudanar da shi lokaci guda a adadin yankunan majalisar dattawa uku dake jihar. Bayan haka, shugaban majalisar dokoki jihar, Alhaji Nasiru Mu'azu Magarya…
Read More
APC ta ɗage zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa

APC ta ɗage zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta ɗage zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa zuwa ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni. An fara gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 29 da 30 ga Mayu. “Bayan ƙarin wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta yi na gabatar da sunayen ’yan takara daga jam’iyyun siyasa, jam’iyyar APC ta ɗage babban taronta na musamman na shugaban ƙasa daga ranar Lahadi 29 ga wata zuwa Litinin, 30 ga Mayu, 2022 zuwa Litinin, 6 ga Laraba, 8 ga Yuni, 2022," inji Kakakin jam'iyyar APC, Felix…
Read More
Zaɓen fidda gwani: Malagi ya taya Bago murna, ya roƙi magoya bayansa su kwantar da hankalinsu

Zaɓen fidda gwani: Malagi ya taya Bago murna, ya roƙi magoya bayansa su kwantar da hankalinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, kuma fitaccen ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Neja a ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Alhaji Mohammed Idris Malagi (Kaakaki Nupe), ya taya Hon. Mohammed Umar Bago murna yin nasara a zaɓen fidda gwani da ya gudana rana Alhamis ɗin nan. Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Minna, Malagi ya yi kira gare su da su kwantar da hankulansu kuma su cigaba da bai wa Jam'iyyar APC duk wata gudunmuwar da ta dace don ganin an kai ga nasara a babban zaven shekara mai zuwa. A cewarsa Malagi, "mun amince…
Read More
Zaɓen fidda gwani: INEC ta sahale wa jam’iyyu ƙarin kwanaki

Zaɓen fidda gwani: INEC ta sahale wa jam’iyyu ƙarin kwanaki

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta sahale wa jam'iyyun siyasa ƙarin kwanaki shida kan su kammala komai dangane da zaɓuɓɓukansu na fidda da gwani. INEC ta sahale wa jam'iyyun ranakun 4 zuwa 9 na Yunin 2022 kan su kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani tare da miƙa sunayen 'yan takararsu bayan da jam'iyyun suka roƙi INEC ɗin ƙarin lokaci. Hukumar zaɓen ta ce, da farko jam'iyyun sun buƙaci ƙarin lokaci amma ta hana saboda ba ta yarda da duk wani abun da zai jirkita mata jadawalinta ba. Ta ƙara da cewa, bayan da ta fahimci babu wani aiki tsakanin…
Read More
Tsoron Allah wajibi ne a sana’armu, inji Dakta Yunusa Wanzam

Tsoron Allah wajibi ne a sana’armu, inji Dakta Yunusa Wanzam

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Zannan Askan Sarkin Gombe kuma Sarkin Askan Bolari ta cikin garin Gombe, Dakta Yunusa Wanzam, ya yi iƙirarin cewa, duk wanda ba ya tsoron Allah to ba zai taɓa yin tasiri a tsakanin wanzamai ba. Ikirarin nasa ba ya rasa nasaba da yadda cikin 'yan kwanakin nan wasu ke fakewa da sunan masana a harkar maganin gargajiya amma kuma sam ba su da ilimi a kan harkar. A lokacin da yake hira da wakilanmu a harabar warakarsa a Bolari, Gombe, Dr. Yunusa Wanzam, ya ja hankalin irin waɗannan mutane da su ji tsoron Allah, saboda…
Read More
2023: Yari ya yi kira ga haɗin kai tsakanin mambobin APC a Zamfara

2023: Yari ya yi kira ga haɗin kai tsakanin mambobin APC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar ya yi kira ga mambobi da magoya bayan Jam'iyyar APC a jihar da su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya don samun nasarar jam'iyyar a zaɓen 2023. Yari ya yi kiran ne yayin da yake tsokaci kan sulhu tsakanin shi da Sanata Kabiru Garba Marafa da Gwamna Bello Matawallen Maradun a zantawa da manema labarai a gidansa. A cewar shi, kiran ya zama dole bisa la'akari da babban zaɓe da ke gabatowa. "Babu wani cigaban ƙasa da za a samu a kowace al'umma ko siyasa idan babu haɗin kai…
Read More
2023: Sarkin Damaturu, El-Kanemi, ya yi wa Osinbajo fatan nasara

2023: Sarkin Damaturu, El-Kanemi, ya yi wa Osinbajo fatan nasara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya ce masarautar za ta goyi bayan mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo tare da yin addu’a akan Allah Ya sa ya zama shugaban ƙasa a 2023. El-Kanemi ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin mataimakin shugaban ƙasar wanda ya kai ziyarar ban-girma a fadarsa ranar Litinin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. Osinbajo ya je Yobe ne a cigaba da tuntuɓar sa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar. Basaraken ya ce ziyarar da mataimakin shugaban ƙasar ya…
Read More