Editor

9513 Posts
Bayan naɗa sabon Akanta-Janar Anamekwe, an gano EFCC na bincikensa

Bayan naɗa sabon Akanta-Janar Anamekwe, an gano EFCC na bincikensa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon Akanta-Janar na riƙon ƙwarya a Nijeriya yana cikin tuhume-tuhumen Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) Ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta naɗa Anamekwe Nwabuoku a matsayin Akanta-Janar na Nijeriya na riƙon ƙwarya, bayan samun Ahmed Idris da Hukumar EFCC ta yi da zargin karkatar da kuɗaɗe ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi, wanda ta zarge shi da karkatar da Naira biliyan 80. To sai dai shi ma sabon da aka naɗa, Anamekwe Nwabuoku, akwai zarge-zarge na cin hanci da rashawa a kansa, inda tuntuni…
Read More
Ba za a sake amfani da jirgin ƙasa da titin Abuja zuwa Kaduna ba – Sharaɗin ’yan bindiga ga gwamnati

Ba za a sake amfani da jirgin ƙasa da titin Abuja zuwa Kaduna ba – Sharaɗin ’yan bindiga ga gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar hana amfanin da titin Kaduna zuwa Abuja gabaɗaya idan Gwamnatin Tarayya ba ta saki yan'uwansu ba. Shugaban 'yan ta'addan, Abu Barrah, ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridar Desert Herald. Abu Barrah ya qara da cewa saboda su Gwamnatin Tarayya ta ɗage ranar dawo da amfani da jirgin ƙasan. Ya ce: "Za mu saki sauran fasinjojin idan aka saki wasu kwamandojinmu dake hannun gwamnati. "Idan gwamnati ta ƙi amsa buqatunmu. Muna gargaɗin 'yan Nijeriya musamman masu hawa…
Read More
Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Nasarawa ta tara Naira biliyan 40 ta sabon tsarin tara kuɗin shigarta

Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Nasarawa ta tara Naira biliyan 40 ta sabon tsarin tara kuɗin shigarta

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga na cikin gida wato Nasarawa State Internal Revenue Services, Ahmed Muhammad, ya bayyana cewa hukumar a ‘yan kwanakin baya ta taro kuɗaɗen shiga da sun kai kimanin Naira biliyan 40 sakamakon ƙirƙiro da sabon tsarin tattaro kuɗaɗen shiga da ta yi kwanakin baya wato na yin amfani da mashinan zamani don samun sauƙin karɓan kuɗaɗen haraji a jihar. Ahmed Muhammed ya sanar da haka ne a lokacin da yake zanta da wakilin mu dangane da harkokin hukumar a ofishin sa dake Lafiya babbar birnin jihar ranar Litinin 23 ga…
Read More
Hukumar NUDB ta yi gargaɗin a riƙa bin ƙa’idojin mallakar filaye da gine-gine a biranen Jihar Nasarawa

Hukumar NUDB ta yi gargaɗin a riƙa bin ƙa’idojin mallakar filaye da gine-gine a biranen Jihar Nasarawa

•Ta ce za ta cigaba da rushe gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar Tsara Manyan Birane na Gwamnatin Jihar Nasarawa, wato Nasarawa State Urban Development Board (NUDB) a turance, ta gargaɗi al’ummar jihar baki ɗaya dangane da mallakar filaye ko yin gine-gine ba bisa ƙa’ida ba a manyan biranen jihar. Manajan daraktan hukumar, Injiniya Idris Wada ne yayi wannan gargaɗi a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a ofishin sa dake babbar hedikwatar hukumar a Lafiya babban birnin jihar ranar Litinin 23 ga watan Mayun shekarar 2022 da ake ciki.…
Read More
Kuskure ne saka sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya, inji Sarkin Dutse

Kuskure ne saka sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya, inji Sarkin Dutse

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji (Dr.) Nuhu Muhammad Sunusi, ya ce kuskure ne sama wa sarakuna matsayi a cikin tsarin dokokin ƙasa kamar yadda majalisar ƙasa ta yi yunƙurin yi kwanan baya. Sarkin ya ce ya ji daɗin yadda ƙudirin ya faɗi bai kai ga samun nasara ba a Zaure Majalisar Nijeriya a lokacin da aka tafka mahawa akan lamarin. Sakin ya faɗi haka ne a lokacin da ya amshi baƙuncin shugaban majalisar dokoki ta Nijeriya Sanata Ahmed Lawan a fadarsa da ya kawo masa ziyarar bangirma tare da neman goyan bayansa akan buƙatarsa…
Read More
Matsalar tsaro: Sama da Katsinawa 13,000 suka yi hijira zuwa Nijar – Gwamna Masari

Matsalar tsaro: Sama da Katsinawa 13,000 suka yi hijira zuwa Nijar – Gwamna Masari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa al’ummar Jihar Katsina sun ga bala’in ‘yan bindiga, a cikin mummunan tashin hankalin da aka shiga matsananciyar wahala. Masari ya ce bala’i ya yi tsananin da an fatattaki mutane daga yankunansu, har ta kai sama da Katsinawa 13,000 sun yi gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar. Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da ‘yan bindiga suka hana zaman lafiya. Masari na magana ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, wanda ya je a matsayin sa na ɗaya daga cikin ‘yan takarar…
Read More
Sin ba ta da buƙatar adana abinci daga kasuwar ƙasa da ƙasa

Sin ba ta da buƙatar adana abinci daga kasuwar ƙasa da ƙasa

Daga CMG HAUSA Game da kalaman da wasu ƙasashen yamma suka yi wai ƙasar Sin tana adana abinci daga kasuwar ƙasa da ƙasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai cewa, ƙasar Sin tana da sharaɗi da ƙarfi da kuma imani wajen samar da isasshen abinci ga al’ummun ƙasarta, kuma babu buƙatar ta adana hatsi daga kasuwar ƙasa da ƙasa. Wang Wenbin ya ƙara da cewa, tun bayan ɓarkewar annobar cutar COVID-19, ƙasar Sin ta samar wa wasu ƙasashe tallafin abinci cikin gaggawa bisa shawarar MƊD da sauran ƙungiyoyin kasa da…
Read More
Sin Na fatan qarin qasashe za su shiga BRICS

Sin Na fatan qarin qasashe za su shiga BRICS

Daga CMG HAUSA Yau Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya yi tsokaci yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya cewa, a matsayinta na ƙasar dake shugabancin BRICS a bana, ƙasar Sin tana goyon bayan ƙasashen ƙungiyar, da su ƙara haɓaka mambobinsu, tare kuma da ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakaninsu da sauran ƙasashen duniya, tana kuma fatan ƙarin ƙasashe waɗanda ke da muradu iri ɗaya za su shiga kungiyar ta BRICS. A farkon bana, wasu ƙasashe kamar Argentina sun nuna fatansu na shiga BRICS, Wang Wenbin ya bayyana cewa, ƙungiyar BRICS, muhimmin tsarin gudanar da…
Read More
Ƙasar Sin ta ce Blinken ya yaɗa bayanan ƙarya a cikin jawabinsa

Ƙasar Sin ta ce Blinken ya yaɗa bayanan ƙarya a cikin jawabinsa

Daga CMG HAUSA Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fada Juma'ar nan cewa, jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi kan manufofin ƙasar Sin, ya yada labaran karya a cikinsa, ya kuma azuzuta wai "barazanar ƙasar Sin", da tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin da kuma bata sunan manufofin cikin gida da waje na ƙasar Sin. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, ƙasar Sin ta nuna rashin amincewarta da ma adawa da kakkausar murya kan wannan jawabi. Wang ya ƙara da cewa, sakatare Blinken…
Read More
Masu buƙata ta musamman sun yi barazanar kai ƙarar INEC kotu

Masu buƙata ta musamman sun yi barazanar kai ƙarar INEC kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu buƙata ta musamman a jihar Ekiti da ke Kudancin Nijeriya sun yi barazanar kai hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan ƙorafin ƙin tanadar abubuwan da suke buƙata domin shiga zaɓen gwamna da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Yuni. Jaridar Premium Times ta ambato shugaban ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen jihar Ekiti, David Anyaele yana shaida wa ‘yan jarida cewa matuƙar INEC ba ta yi abin da ya dace ba, za su shigar da ƙara kotu kan take haƙƙinsu, da dokokin Nijeriya suka ba su a…
Read More