27
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mayaƙan Boko Haram sun kashe farar hula 40 a Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno a Arewa maso gabashin Nijeriya. Ƙungiyar Boko Haram su na ci gaba da ta'asa jifa-jifa duk da kassara ta da hukumomin Nijeriya suka ce sun yi. Rahotanni sun ce ɗimbin ‘yan ta’adda ne suka yi wa farar hula da ba su ɗauke da makami ƙawanya, inda suka yi ta yi musu yankan rago a ranar Lahadi. ‘Yar majalisar wakilai ta Tarayyar Nijeriya da ke wakiltar mazaɓar, Zainab Gimba ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labari. Wata majiya…
