26
May
Daga AMINA YUSUF ALI Muhammad Abacha ɗa a gurin marigayi Sani Abacha, tsohon shugaban ƙasar Nijeriya na mulkin soja ya samu nasarar lashe zaɓen fid ga gwani na Gwamnan Kano a jam'iyyarsa ta PDP. Jami'ar sanar da sakamakon zaɓen, Barista Amina Garba, ita ta bayyana Muhamad Abacha a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu ƙuri'u 736 ya kayar da ɗan takarar da yake bin bayansa a yawan ƙuri'u, Jafar Sani Bello, wanda shi kuma ya samu ƙuri'u 710. Shugaban kwamitin zaɓe, Mohammed Jamu, ya bayyana cewa, an gudanar da zaɓen bisa bin dokoki sannan an yi zaɓen tare…
