29
May
Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi (COEASU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni shida kan ta cika alƙawarin da ta ɗauka ko kuma su tafi yajin aikin sai baba ta gani. Mataimakin shugaban ƙungiyar ta ƙasa kuma kodinetan ƙungiyar na yankin Arewa maso Yamma, Dr. Shehu Jabaka Muhammad ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kwalejin fasaha ta tarayya ta Gusau da ke Jihar Zamfara. Ya ci gaba da cewa, akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi taro na zagaye na biyu domin…
