Editor

9513 Posts
Kotu ta tsare Okorocha bisa zargin almundahanar biliyan 2.9

Kotu ta tsare Okorocha bisa zargin almundahanar biliyan 2.9

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Abuja ta ba da umarnin a tsare tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, karkashin kulawar hukumar EFCC a bisa zargin badaƙalar biliyan N2.9. Alƙalin kotun, Inyang Ekwo ne ya ba da umarnin hakan a ranar Litinin a Abuja. EFCC ta gurfanar da Okorocha da Chinenye tare da wasu kamfanoni me bisa tuhumar laifuffuka 17 masu alaƙa da almundahanar biliyan 2.9. Aƙali Ekwo ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata inda kotun za ta saurari buƙatar belin da Okorocha da Chinenye suka gabatar. Kamfanonin da lamarin ya shafa sun haɗa da: Naphtali International Limited da…
Read More
2023: Ba za ka taɓa zama shugaban Nijeriya ba, Ƙungiyar Ibo ga Atiku

2023: Ba za ka taɓa zama shugaban Nijeriya ba, Ƙungiyar Ibo ga Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar ƙungiyar siyasa da zamantakewar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta ce ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba zai taɓa zama shugaban Nijeriya ba. Ohanaeze ta bayyana hakan ne a lokacin da take yin tir da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP wanda ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar. Ƙungiyar ta bayyana zaɓen a matsayin wani tsari na rashin gaskiya da almundahana wanda ’yan Arewa marasa kishin ƙasa suka sa ido a kan Kudancin ƙasar nan. Sakatare Janar na ƙungiyar Ohanaeze, Mazi Okechukwu…
Read More
CAN ga hukumomin tsaro: Dole ku kamo masu hannu a kashe Musulma a Anambara

CAN ga hukumomin tsaro: Dole ku kamo masu hannu a kashe Musulma a Anambara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN, ta buƙaci ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da su kamo masu hannu a kisan wata Musulma mai juna biyu da aka bayyana sunanta da Fatima da ’ya’yanta huɗu a jihar Anambra. Ƙungiyar kiristocin ta bayyana mutuwarsu a matsayin abin da ba za a amince da ita ba kwata-kwata, rashin gaskiya kuma abin zargi ne, ta kuma buqaci gwamnati da ta ɗauki matakin hukunta masu laifin. Shugaban CAN, Rabaran Dr Samson Ayokunle, a wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa…
Read More
Sanatan APC a Legas ya lashe tikitin tsayawa takarar Sanatan Ogun

Sanatan APC a Legas ya lashe tikitin tsayawa takarar Sanatan Ogun

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, Sanata Solomon Adeola wanda aka fi sani da Yayi ya lashe tikitin jam’iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Jihar Ogun ta Yamma bayan ya yi wani gagarumin yunƙuri daga Jihar Legas zuwa Jihar Ogun. Sanata Adeola ya samu tikitin tsayawa takarar jam’iyyar APC ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata a wajen zaɓen fidda gwani da jami’an jam’iyyar suka gudanar a ɗakin taro na Orona da ke Ilaro, hedikwatar ƙaramar hukumar Yewa ta Kudu a jihar. A cewar jami’in zaɓen fidda gwani, Dapo Adekoya, Sanata Adeola ya samu ƙuri’u…
Read More
Yadda wata babbar dillaliyar miyagun ƙwayoyi a Delta ta shiga hannu

Yadda wata babbar dillaliyar miyagun ƙwayoyi a Delta ta shiga hannu

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta yi nasarar cafke wata mata mai shekaru 59, wadda aka tabbatar ita ce shugabar dillalan muggan ƙwayoyi a Jihar Delta da maƙwabtanta. Premium Times ta rawaito cewa: Matar mai suna Bridget Emeka, an fi sanin ta da suna Mama. An kama ta ne a ranar Lahadi, a wani danƙareren gidanta da ke garin Warri a jihar Delta. Kakakin yaɗa labaran NDLEA, Femi Babafemi ne ya sanar da haka a ranar Talata a Abuja. NDELA sun zargi Mama da riƙa yin amfani da kantamemen gidanta dake kan Titin…
Read More
Yadda tsananta haraji ga kamfanonin sadarwa ya jawo matsalar sabis ɗin layukan waya a Nijeriya

Yadda tsananta haraji ga kamfanonin sadarwa ya jawo matsalar sabis ɗin layukan waya a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun nuna cewa, tsananin yawan harajin da gwamnatin Nijeriya take tafka wa kamfanonin sadarwa shi ne ummul'aba'isin na rashin ƙarfin sabis ɗin layukan waya a ƙasar nan.  Wannan rahoto yana ƙunshe ne a wani rahoto da  SB Morgen suka  haɗa.  Rahoton ya bayyana cewa, kamfanonin sadarwar suna azabtuwa daga haraji da ya zarta ƙa'ida da gwamnatin Nijeriya take ta lafta musu. Rahoton ya bayyana cewa, a yanzu haka akwai haraji iri daban-daban har kala 40 wanda kamfanonin sadarwa suke biya a Nijeriya. Sai dai inda matsalar take a cewar rahoton, wannnan gingimemen haraji shi ya…
Read More
Almundahana: EFCC ta cafke Yari bisa zargin alaƙarsa da badaƙalar Akanta-Janar

Almundahana: EFCC ta cafke Yari bisa zargin alaƙarsa da badaƙalar Akanta-Janar

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa (EFCC), ta kama tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari bisa nasabarsa da binciken da hukumar ke kan gudanarwa a kna dakataccen Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris. EFCC ta cika hannu da Yari ɗin ne a ranar Lahadi a gidansa da ke Abuja bayan da ya lashe zaɓen fidda gwanin APC inda ya zama ɗan takarar sanata na jam'iyyar a Shiyyar Zamfara ta Yamma a zaɓe mai zuwa. Tun a ranar 16 ga Mayu Idris, ya faɗa a komar EFCC inda ake bincike a kansa kan zargin wawushe biliyan N80 daga aljihun…
Read More
Yadda Kwankwaso ya taya Gwamna Wike kiciniyar kayar da Atiku a zaɓen PDP – Rahoto

Yadda Kwankwaso ya taya Gwamna Wike kiciniyar kayar da Atiku a zaɓen PDP – Rahoto

Dagana AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamnan Kano, Gwamna Kwankwaso ya amshi kuɗaɗe daga Gwamnan jihar Ribas, Wike, don raba wa daliget na Kano a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP, inda SaharaReporters ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya amshi kimanin Dalar Amurka 15,000 ga kowanne daliget na Kano. Haka zalika, ya ɓoye daliget na Kano su 44 a wani otal, domin shirya wa nasarar ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a PDP, Wike a zaɓen fidda gwanin. Wata majiya ta bayyana wa Sahara Reporters cewa, Kwankwaso ya amsar wa kowanne daliget na Kano guda ɗaya Dalar Amurka…
Read More
Nasarar Atiku a zaɓen fidda gwani ta jefa APC cikin ruɗani – Urzo Kalu

Nasarar Atiku a zaɓen fidda gwani ta jefa APC cikin ruɗani – Urzo Kalu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu ya gargaɗi Jam’iyyar APC ta yi karatun ta natsu wajen zaɓen fidda ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar. Da yake miƙa saƙon taya Atiku murnar nasarar da ya yi a zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar PDP, Kalu ya ce kada APC ta kuskura ta tsaida wani ɗan Kudu ɗan takaran ta. ”Idan har ba ritayar dole APC take so ta tafi ba a siyasa, toh ta zaɓi ɗan Arewa ne ya yi mata takarar Shugaban Ƙasa tunda wuri. Kuma Ahmed Lawan ne ya fi dacewa. ”Dalili kuwa…
Read More
Ranar Yara: Ma’aikatar Mata ta sha alwashin samar da kyakkyawar Rayuwa ga Yara – Dr. Zahra’u

Ranar Yara: Ma’aikatar Mata ta sha alwashin samar da kyakkyawar Rayuwa ga Yara – Dr. Zahra’u

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A duk ranar 27 ga watan Mayun kowace shekara ne dai ake gabatar da ranar Yara ta Duniya wato World Children Day, taron na bana dai shi ne: “Samar da kyakkyawar makoma ga kowane Yaro”. Jihar Kano ma ba a barta a baya ba wajen aiwatar da wannan bikin, inda Gwamnatin jihar Kano tare da Ma’aikatar Mata da ci gaban al’umma ta gabatar a gidan Gwamnatin jihar, Kano. Tun da farko a jawabinta, Kwamishinar Mata da Cigaban Al’umma ta Jihar Kano, Dr. Zaharau Muhammad, ta bayyana muhimmancin wannan rana da kuma tasirin da ta ke…
Read More