Editor

9513 Posts
Wasu matan ne suke kashe wa kansu aure

Wasu matan ne suke kashe wa kansu aure

Daga AMINA YUSUF ALI Barkarnmu da haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun jaridar Blueprint Manhaja, mai farin jini. Hausawa sun ce: 'Idan an bi ta ɓarawo, sai a bi ta ma bi sawu'. Kusan koyaushe a ƙasar Hausa muna magana a kan yawaitar mutuwar aure a ƙasar Hausa. Ni kaina na sha rubutu a kan hakan, kuma na sha ƙorafi daga 'yanuwa maza masu kiran waya. Musamman masu ganin ina ɗaukar laifin rabuwar aure ina ɗora musu kacokan.   Duk da dai masu bibiyar shafin nan sun shaida cewa, kowanne lokaci mukan yi ƙoƙarin ganin mun taɓo kowanne ɓangare,…
Read More
2023: Ƙungiyoyin Arewa sun yi fatali da shugabancin Ibo

2023: Ƙungiyoyin Arewa sun yi fatali da shugabancin Ibo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa (CNG), ta caccaki ’ya’yan Ƙungiyar Dattawan Ibo (IECF) da sauran ƙungiyoyin da ke fafutukar ganin an tsayar da shugaban ƙasa a yankin Kudu Maso Gabas, inda suka ce suna tada hankalinsu ta hanyar da ba ta dace ba. Ƙungiyar ta CNG ta yi zargin cewa, dattawan ƙabilar Ibo sun zama babbar barazana ga tsaro a ƙasar, inda ta ƙara da cewa, gargaɗin da suka yi a baya-bayan nan cewa duk wani yunƙuri na kaucewa shiyyar Kudu Maso Gabas na tsayar da shugaban ƙasa a 2023 zai ruguza kasuwancin Nijeriya. Don haka ƙungiyar haɗin…
Read More
Alamomin da ke nuna fata bata karɓi kayan kwalliyar da ake amfani da su ba (2)

Alamomin da ke nuna fata bata karɓi kayan kwalliyar da ake amfani da su ba (2)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun fara bayyanin yadda kayan kwalliya ke tasiri wurin lalacewar fata da kuma janyo mata matsalolin da ka iya zama wani ciwon na daban. Har muka fara zayyano wasu daga cikin alamomin da idan an gansu a fata to alamu ne na bata aminta da kayan kwalliyar ba. A wannan sati zamu ci gaba ne da kawo wasu daga cikin alamomin har zuwa inda ruwan alƙalamin wannan satin zai tsaya. Bar-ni-da-mugu:Da yawa suna ganin matsalar cizon kwari ko tava wani abu da fatar bata amsa na daga dabbobi ko tsiro ne kawai…
Read More
Ƙungiyar matasa ta nemi haɗin kan al’umma kan daƙile shayin miyagun ƙwayoyi

Ƙungiyar matasa ta nemi haɗin kan al’umma kan daƙile shayin miyagun ƙwayoyi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dangane da muguwar yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, Ƙungiyar Matasa ta Ƙasa (NYCN) da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA) na neman haɗin kan al’ummomi da ƙungiyoyi wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya. Dangane da rahoton ƙwayoyi na duniya na 2021, wanda Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ya fitar, kusan mutane miliyan 275 ne ke amfani da ƙwayoyi a duk duniya, yayin da sama da mutane miliyan 36 ke fama da matsalar shan muggan ƙwayoyi. Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 ya…
Read More
2023: Ya kamata matasa su guje wa shiga bangar siyasa – Ƙungiyar Ushaƙun

2023: Ya kamata matasa su guje wa shiga bangar siyasa – Ƙungiyar Ushaƙun

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Ganin yadda babban zaɓe ya ke ƙara ƙaratowa kuma ’yan siyasa kan yi amfani da matasa wajen aika-aika irin na bangar siyasa, ƙungiyar Ushaqun Nabiyi Rasulul a'azam ta yi kira ga iyayen yara da su kula da 'ya'yan su. Kiran hakan ya fito ne ta bakin shugaban ƙungiyar ta Ushaqun Nabiyi na ƙasa Sherif Auwal Siddi Bolari, a lokacin da ƙungiyar ta gudanar da babban taron ta a Gombe. Ushagun Nabiyi ƙungiya ce ta mawaƙan ƙasidun Hausa ta Nijeriya ƙarƙashin jagoranci Shugabanta na ƙasa, Sheriff Auwal Siddi Bolari, inda ya ce, matasa su hanu…
Read More
Kamfanonin Amurka sun ci riba yayin da ake fama da wahalar hauhawar farashin abinci

Kamfanonin Amurka sun ci riba yayin da ake fama da wahalar hauhawar farashin abinci

Daga CMG HAUSA Abokaina, a wajenku, farashin kayayyakin abinci ya karu? Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, da takunkuman da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba wa Rasha, sun dakatar da cinikin takin zamanin da ake samarwa a ƙasashen Rasha da Belarus, lamarin da ya sa kuɗin da ake kashewa a aikin gona ya ƙaru. Baya ga wannan batu, yadda Ukraine da Rasha suka dakatar da aikin fitar da alkama da masara zuwa ƙasashen waje, sun sa farashin kayayyakin abinci na ƙasashe daban daban ya ƙaru sosai. Yanzu a ƙasar Masar, farashin burodi ya karu da kashi 50%. Yayin da…
Read More
Wang Yi ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo

Wang Yi ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo

Daga CMG HAUSA Yau ne, mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na hukumar tattalin arziki da zaman takewar al’umma ta yankin Asiya da tekun Pacifik ta MƊD wato ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo a birnin Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong dake kudancin ƙasar Sin, inda ya gabatar da jawabi. Cikin jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, ya dace a hada kai domin gina kyakkyawar makomar ƙasashen yankin Asiya da tekun Pacifik, ta hanyar ɗaukar matakai uku, na farko, nacewa kan manufar kiyaye zaman lafiya da…
Read More
Sin ta himmatu wajen tabbatar da kafuwar yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific

Sin ta himmatu wajen tabbatar da kafuwar yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific

Daga CMG HAUSA Ministan maaikatar cinikiyya ta ƙasar Sin Wang Wentao, ya ce ƙasar sa za ta yi aiki tukuru, wajen tabbatar da nasarar kafa yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific, cikakke kuma bisa matsayin koli. Minista Wang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, yayin taro na 28 na ministocin ƙungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific ko APEC, wanda ya gudana a ƙarshen mako. Wang ya ce kamata ya yi dukkanin ƙasashe mambobin APEC su jajirce, wajen gina alumma mai makomar bai daya a matsayin tushensu, su kuma ingiza haɗin gwiwa…
Read More
Sabbin gwamnonin Kastina da Neja

Sabbin gwamnonin Kastina da Neja

An ce sanin gaibu sai Allah. Don haka ban ce jihohin Katsina da Neja dukka an gama zaɓe ba. Amma a fili ta ke jama'a kan bayyana wanda ya yi ficce kuma ake rinjayar da samun nasararsa. Katsina dai zakara ya kunno kai, tabbas ko mutane dubu mutum guda ne wanda zai zamo ya yi nasara sauran kuma su ɗauki ƙaddara tare da haƙura amma sai idan an kwatamta adalci za a yi zaɓen sauran su amince. Jihar Neja ga dukkan alamu fitaccen marubucin nan mai kamfanin jaridu na Blueprint wacce ke fitar da jarida Manhaja, Alhaji Muhammad Idris Malagi,…
Read More