Editor

9513 Posts
Zaɓen fidda gwani: APC ta ɗage zaɓen ‘yan takarar Shugaban Ƙasa, PDP ta shiga ruɗani

Zaɓen fidda gwani: APC ta ɗage zaɓen ‘yan takarar Shugaban Ƙasa, PDP ta shiga ruɗani

Daga BASHIR ISAH Jam’iyyar APC ta ɗage zaɓen fidda gwanin na ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da ta shirya gudanarwa a ranar Litinin, 23 ga Mayun 2022, tare da cewa za ta sanar da sabon lokaci nan gaba. Duk da dai jam’iyyar ba ta ba da dalilin ɗage zaɓen ba, amma ba wannan ne karon farko da APC ta sauya jadawalin zaɓen fidda gwanin nata ba dangane da shirye-shiryen zaɓen 2023. Sanarwar da ta nuna ɗage zaɓen ta ce, “An ɗage shirin tantace ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin,  23 ga Mayun 2022. “Za a sanar…
Read More
Zagin addinin wani: laifin iyaye ko ‘ya’ya (1)

Zagin addinin wani: laifin iyaye ko ‘ya’ya (1)

Daga AISHA ASAS A duk lokacin da aka tava wani mai muhimmanci da zuciya take so da mutunta shi, zuciya kan girgiza yayin da hankali kan gushe, a daidai lokacin komai zai iya faruwa. Wannan ne yasa duk faɗan da kaga ya ƙazanta to tabata akwai sakin layi a furucin na su. A ƙasa irin Nijeriya da take da mutane masu mabanbantan ra’ayi da addini, kuma ake so mu zauna lafiya ba tare da wani ya ci zarafin wani ba, to wajibi ne a riƙa sawa baki linzami yayin faɗar magana da ta shafi addini. Addini a arewacin Nijeriya wani…
Read More
Har yanzu ta’addanci na ƙara zama barazana a Nijeriya

Har yanzu ta’addanci na ƙara zama barazana a Nijeriya

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kawo ƙarshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a ranar 3 ga Mayu, 2022 tare da ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa. Ya ziyarci waɗanda ta’addanci ya shafa kamar, sansanoni ’yan gudun hijira a Jihar Borno, waɗanda rikicin ta’addancin Boko Haram ya kora daga muhallan su. Guterres ya bayyana fatansa na cewa, Nijeriya na daf da samun nasara a yaƙin Boko Haram. Ya yabawa gwamnatin Buhari bisa dabarunta da suka ƙarfafawa mayaƙan Boka Haram aqalla 37,000 kwarin gwiwar miƙa wuya tare da kai su wuraren halin gyaran hali.…
Read More
Ɗangote na neman rancen Naira biliyan 638 kafin 2023

Ɗangote na neman rancen Naira biliyan 638 kafin 2023

Daga AMINA YUSUF ALI Mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote yana buƙatar rancen Naira biliyan 638 don ƙarasa ginin matatar man wacce yake so ya kammala kafin nan kafin shekarar 2023. Kamar yadda jaridar Ingilishi ta News Business News ta rawaito.  A wani sakamakon rahoto da kamfanin Fitch wanda ya yi fice wajen bincike a Duniya ya yi hasashen cewa, mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Ɗangote dole zai buƙaci rancen Naira biliyan 638 don kammala matatar man da ya fara ginawa wacce ake sa ran za ta lamushe har Dalar Amurka biliyan…
Read More
Almundahana: Gwamnati ta naɗa muƙaddashin Akanta-Janar

Almundahana: Gwamnati ta naɗa muƙaddashin Akanta-Janar

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta amince da naɗinMr. Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku a matsayin wanda zai ci gaba da riƙon ofishin Akanta-Janar na Tarayya biyo bayan binciken da EFCC ke kan gudanarwa kan Akanta-Janar, Ahmed Idris bisa zargin almundahana. Hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Sakataren Ma'aikatar Kuɗi da Tsare-tsare na Tarayya, Aliyu Ahmed ya sanya hannu mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Mayu, 2022. Wasiƙar ta ce naɗin zai yi aiki ne ya zuwa lokacin da bikin zai kammala. Kafin wannan lokaci, Nwabuoku darakta ne a Ofishin Akanta-Janar, inda yanzu ya zama mai kula da ofishin na…
Read More
’Yan Nijeriya na shanye barasa da lemon kwalba na Naira biliyan 246 a wata uku – Rahoto

’Yan Nijeriya na shanye barasa da lemon kwalba na Naira biliyan 246 a wata uku – Rahoto

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun bayyana cewa, a cikin kowanne watanni uku 'yan Nijeriya sukan kwankwaɗe barasa da lemunan kwalaba na wuri na gugar wuri har na sama da biliyan Naira 245.61. Sakamakon wani rahoto mai taken Q1 2022 da aka gudanar a kan manyan rukunin kamfanonin samar da ababen sha guda uku wato, kamfanonin gida Nijeriya, kamfanonin wajen ƙasar nan da kuma kamfanin Guinness Nigeria ya bayyana cewa, yadda yawan masu yi wa kamfanonin ciniki yake ƙaruwa ya tilasta kamfanonin ƙara zagewa wajen ganin ababen shan ba su yanke wa masu saye ba.  Wannan ba makawa shi ya…
Read More
Abinda ke jawo yawaitar ficewar kamfanonin mai na ƙasar waje daga Nijeriya (2) – Sani Ɓaɓura

Abinda ke jawo yawaitar ficewar kamfanonin mai na ƙasar waje daga Nijeriya (2) – Sani Ɓaɓura

Daga AMINA YUSUF ALI Komai na tafiya daidai wajen haqo mai a Nijeriya har wajen ƙarshan 1980 zuwa farkon 1990 lokachin da guraren haƙar man suka fara fuskantar matsaloli kamar haka: Guraren ƙauyuka ne futuk, babu ruwan sha mai tsafta, ba wutar lantarki, gidajensu na bukka ne a kan ruwa suke kwana, suke bahaya, makarantun 'ya'yansu ginin ƙasa ne, rufin ciyayi; kuma duk lokacin da bututun dake ɗauke da mai ya fashe, sana'arsu ta kamun kifi da noma ta  shiga uku. Hakazalika, sai sun yi tafiya a kwale-kwale mai nisa kafin su sami ruwan da za su sha. Ƙauyukan kuwa…
Read More
Ƙungiyar 13×13 Movement ta raba buhunhunan shinkafa da masara

Ƙungiyar 13×13 Movement ta raba buhunhunan shinkafa da masara

Daga AMINA YUSUF ALI a KANO Shugaban ƙungiyar 13x13 Movement na ƙasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya jagoranci raba kayan abinci: Buhunhunan shinkafa da buhunhunan masara wanda ƙungiyar (Buhari For All) ta bai wa ƙungiyar 13x13 Movement kyautar su. Shi kuma shugaban ƙungiyar, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ne ya jagoranci rabawa. An ba wa kowanne mutum ɗaya buhunan shinkafa uku-uku da buhunhunan masara guda hur-huɗu. Sannan aka ɗora masa kuɗi Naira 20,000 ga kowanne mamba da ke cikin ƙungiyar ta 13x13 Movement. Mambobin ƙungiyar 13x13 Movement sun yi wa ƙungiyar Buhari For All godiya tare da…
Read More
Da gaske ba zaratan sojoji a Nijeriya?

Da gaske ba zaratan sojoji a Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Bayan samun ’yancin Nijeriya a 1960, an samu gwamnatin farar hula ne, wato Jamhuriya ta Farko, da marigayi, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ya jagorantar a matsayin Firaminista yayin da Marigayi Nnamdi Azikwe ke matsayin Shugaban Ƙasa, da hakan ya faru gabanin ɗaukar tsarin shugaba ɗaya mai wuƙa da nama irin na Amurka da a ka yi amfani da shi a jamhuriya ta biyu daga 1979. A wancan lokacin an yi amanna aikin soja shi ne yaƙi don kare ƙasa ba wai riƙe madafun mulki na gwamnati ba. Hasalima ai sojojin Nijeriya na cikin sojojin da su…
Read More
Sharhi: Kafofi na wai masu ‘yanci

Sharhi: Kafofi na wai masu ‘yanci

Daga LUBABATU LEI Kwanan nan, Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu na Najeriya Lai Mohammed, ya ja kunnen kamfanoni mamallaka dandalolin sada zumunta, da su daina bai wa ƙungiyar nan ta IPOB, ta ‘yan aware dake kudancin Najeriya, damar yaɗa bayanai na rura wutar rikici da ƙabilanci a kan shafukansu. Lai Mohammed ya yi wannan gargaɗi ne a yayin wata tattaunawa da tawagar kamfanin Facebook. Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Najeriya za ta sanya ido sosai kan shafukan Facebook da sauran dandaloli makamantan sa a kwanaki masu zuwa, domin tabbatar da ko facebook ɗin ya kiyaye wannan jan hankali, yayin…
Read More