Editor

9513 Posts
Ba a sauya wa tuwo suna

Ba a sauya wa tuwo suna

Daga IBRAHIM YAYA Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin, ita ce kaɗai halastacciyar gwamnati dake wakiltar ƙasar Sin. Haka kuma kasancewar ƙasar Sin ɗaya tilo a duniya, ita ce babbar manufar da ƙasashen duniya suka amince da ita, kana tushen siyasa na raya hulɗa tsakanin Sin da duƙ ƙasashen da suka ƙulla ko ma suke son ƙulla alaƙa da ƙasar Sin. Yanzu haka akwai ƙasashe 180 a duniya, waɗanda suka amince tare da goyon bayan manufar ƙasar Sin ɗaya tilo a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta zahiri…
Read More
Ƙungiyar ’yan Tifa ta tallafa wa marayu a Kano

Ƙungiyar ’yan Tifa ta tallafa wa marayu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar ’yan Tifa ta Jihar Kano ta raba kayayyakin abinci, har da ma tufafi ga ’ya’yan ’yan ƙungiyar da su ka rasu sama da guda 100 a ranar Litinin da ta gabata a ofishinta na jiha. Hakimin Ƙaramar Hukumar Garinmallam, wanda ya samu wakilcin Wazirin Garin Malam Sheik Abubakar Rabo Abdulkarim, shi ne ya jagoranci rabon kayan. Sheikh Abdulkarim ya ce, sanya farin ciki a zukatan marayu da taimaka wa rayuwarsu abu ne wanda zai inganta rayuwar su, tare da kawar musu da tunanin rashin iyayen su. Ya bayyana cewa, halin da marayu da iyayen…
Read More
2023: Mu guji ra’ayin ƙabilanci da addini, inji Ƙungiyar Nijeriya Ɗaya

2023: Mu guji ra’ayin ƙabilanci da addini, inji Ƙungiyar Nijeriya Ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Ƙungiyar Nijeriya Ɗaya (ONG), wata ƙungiya mai zaman kanta ta ‘One Nigeria Group’, ta yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji ra’ayin ƙabilanci da addini, su zaɓi ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Saleh-Hassan, ne ya yi wannan roƙo a wata sanarwa da ya fitar a Abuja cikin makon nan. Saleh-Hassan ya buƙaci ’yan Nijeriya da su zaɓi shugaban ƙasa wanda ya kamata ya zama shugaban ƙasa ba tare da la’akari da ko wane yanki na ƙasar ya fito ba. Ya buƙaci ’yan Nijeriya…
Read More
Akwai masifu da dama fiye da rashin yin zaɓe – Martani ga Ɗansadau

Akwai masifu da dama fiye da rashin yin zaɓe – Martani ga Ɗansadau

DAGA ABDULWAHAB SULAIMAN A wata sabuwar tattaunawar Sanata Ɗansadau ya sake yi da BBC Hausa game da korar Digital Iman din da suka yi daga Limancin Masallacin rukunin gidajen 'yan Majalisa dake Apo Legislative Quaters, Abuja. A hirar tasu ya bayyana cewa, wai mutane ba su san masifar rashin yin zaɓe ba. Akwai masifar da ta kai, 'yan  bindiga su shiga gari su kashe mutane, su sace musu dabbobi, su sace Yara, kuma su yi wa mata fyaɗe. Akwai wani bidiyo da na gani na wata tsohuwa 'yar kusan shekara 70 tana kuka tana cewa wani yaro ɗan bindiga ya yi…
Read More
Idan malamai ba su faɗa wa shugabanni gaskiya a kan mumbari ba, a ina za su faɗa?

Idan malamai ba su faɗa wa shugabanni gaskiya a kan mumbari ba, a ina za su faɗa?

Daga SALISU ISMA'IL KABUGA Ita gaskiya, gaskiya ce indai gaskiyar ce. Yayin da aka tozarta gaskiya, ko kuma sai an zaɓi wanda za a gaya wa gaskiya. Ma'ana, sai masu rauni (Talakawa) za a gaya wa gaskiya, babu shakka an tozartar da gaskiya. Mecece gaskiya kuma a ina za a faɗi gaskiya?  A taƙaice gaskiya nasiha ce, wadda ake faɗa wa mutum/mutane cikin zance ko a wa'azance kamar yadda malamai suke yi idan za su warware zare da abawa a kan wani abu, yayin da suke kan munbarin khudba da ma a kowanne zarafi da suka samu na feɗe gaskiya.…
Read More
Bom ya halaka mutum 20 a mashayar Taraba

Bom ya halaka mutum 20 a mashayar Taraba

Daga BASHIR ISAH A ƙalla mutum ashirin ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon tashin bom a wata mashayar burkutu da ke ƙauyen Iwari cikin ƙaramar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba. Wani ganau ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa, wasu da dama sun jikkata sakamakon harin. "Sama da mutum ashirin ne aka kashe a wannan yammaci a wata mashayar burkutu bayan da wani matashi ya tashi wani abu mai fashewa a mashayar da ke yankin Iware cikin Ƙaramar Hukunar Ardokola a jihar. "Haka nan, fashewar ta jikkata wasu da dama wanda a yanzu haka ake yi musu magani a…
Read More
Farfagandar ƙyamar ƙasar Sin ba za ta yi kasuwa a tsibiran yankin Pacific ba

Farfagandar ƙyamar ƙasar Sin ba za ta yi kasuwa a tsibiran yankin Pacific ba

Daga CMG HAUSA A kwanan nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Amurka ya bayyana cewa, fadar White House ta Amurka ta shirya tura tawagar musamman ƙarƙashin jagorancin Mr. Kurt Campbell, jagoran tsare tsare na ayyukan da suka shafi yankunan tekun Indiya da Pacific a majalissar tsaron ƙasa, zuwa tsibiran dake yankin, ciki har da tsibirin Solomon. Kakakin ya ce tawagar Amurka na sa ran tattauna batutuwa da dama, ciki har da wadanda suka jibanci ƙasar Sin yayin wannan ziyara. A baya bayan nan, Sin da tsibirin Solomon sun sanya hannu, kan yarjejeniyar cudanya a hukumance, don gane da haɗin gwiwar…
Read More
Xi ya aike da saƙon jaje ga shugaban Afirka ta Kudu game da bala’in ambaliyar ruwa a Kwazulu-Natal

Xi ya aike da saƙon jaje ga shugaban Afirka ta Kudu game da bala’in ambaliyar ruwa a Kwazulu-Natal

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike saƙon jaje ga takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, don gane da bala’in ambaliyar ruwa da ta auku a yankin KwaZulu-Natal. Cikin saƙon na sa, Xi Jinping ya ce “Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka kwashe lokaci mai tsawo ana yi a KwaZulu-Natal na Afirka ta kudu ya haifar da ambaliya, da rasuwar mutane masu yawa, kana hakan ya haifar da asarar dukiyoyi da dama”. Ya ce “A madadin gwamnati da al’ummar ƙasar Sin, da ni kai na, ina amfani da wannan dama domin gabatar da sakon…
Read More
Ƙarin abokai sun shiga shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”

Ƙarin abokai sun shiga shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”

Daga CMG HAUSA Yau Talata, hukumar zurfafa gyare-gyare a gida da buɗe ƙofa ga waje ta ƙasar Sin, ta shirya wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar Meng Wei ta yi bayani cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta ƙulla yarjejeniyoyin haɗin kai fiye da 200 ƙarƙashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, tare da ƙasashe 149 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 32. Rahotanni na cewa, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, ƙasar Sin ta ƙulla yarjejeniyoyi da ƙasashen Nicaragua da Syria da Argentina da Malawi da sauransu, ƙarin abokai dake amincewa da shawarar. A farkon rubu’in bana, jiragen ƙasa sun…
Read More
Shugaban Jam’iyyar ADC ya soki lamirin gwamnati

Shugaban Jam’iyyar ADC ya soki lamirin gwamnati

BABANGIDA S. GORA a Kano An bayyana cewa da yawan shuwagabannin gwamnati a Jihar Kano ba su damu da matsalolin da suka shafi al'ummar jihar ba. Hakan ya fito daga bakin muƙaddashin shugaban jam'iyyar ADC na shiyyar Arewa maso Yamma kuma sabon shugaban jam'iyar a Jihar Kano Hon. Musa Sha'aibu Ungoggo. Ungoggo ya ce kasancewar Jihar Kano da take da yawan jama'a kimanin mutum sama da miliyan 20, akwai buƙatar a samu sauyin jam'iyyu guda biyu daga lokacin da aka fara dimukuraɗiyya ba a samu canji ba na jam'iyyun PDP da APC. Ayyukan mazaɓu: Yadda wasu sanatoci suka yi sama-da-faɗi…
Read More