21
Apr
"Rubutu a kafafen sadarwa na zamani cigaba ne" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Duniyar marubutan adabi ba za ta taɓa mantawa da sunan Malam Kabiru Yusuf Fagge ba, wanda aka fi sani da ANKA, da irin gudunmawar da ya bayar kuma har yanzu yake kan bayarwa a harkar rubutun adabi, kama daga rubutun zube, wasan kwaikwayo har zuwa rubutun littattafan ýan makaranta, don bunƙasa ilimin yara manyan gobe. Marubuci, mawallafi, malamin makaranta, kuma ɗan kasuwa. Wakilin Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi kaciɓis da shi a Kano, bayan yayen ɗalibai zangon farko na Kwalejin Marubutan Hausa da aka gudanar, bayan kammala…
