Editor

9513 Posts
Hare-haren Boko Haram/ISWAP sun yi ajalin jami’an tsaro 11 a Neja

Hare-haren Boko Haram/ISWAP sun yi ajalin jami’an tsaro 11 a Neja

*Sanata Sani Musa ya roƙi agajin Gwamnatin Tarayya Daga BASHIR ISAH Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas a Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa na jam'iyyar APC, ya yi tir da mabambantan hare-haren da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai a yankunan ƙaramar hukumar Paikoro da Shiroro tsakanin ranakun Juma'a da Asabar da suka gabata. Bayanai sun nuna sabbin hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro 11 tare da jikkata manoma da dama haɗa da lalata dukiya mai tarin yawa a yankuna da lamarin ya shafa. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba a Abuja, Sanata Sani ya bayyana kashe-kashen da…
Read More
Tarbiyyar yara a ƙasar Hausa: Da sauran rina a kaba!

Tarbiyyar yara a ƙasar Hausa: Da sauran rina a kaba!

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Da fatan na same ku lafiya, Allah ya ba mu wuce wannan sanyi lafiya. Ga mu yau ma kamar kullum cikin filinmu mai albarka, filin koya tarbiyya. Yau za mu tavo yadda muka yi sakaci da rayuwa, muka sa son zuciya da bushewarta, har shaiɗan ya yi galaba cikin rayuwarmu. Mutane mun zamo marasa imani, da rashin tsoron Allah. Da yawa mun fifita kuɗi a kan neman Lahira.Tarbiya ta daɗa nisa da mu, yara ƙanana mun koya musu son abun duniya da neman kuɗi ta kowacce hanya. Yara sun ƙeƙashe zuciya da muguwar rayuwar da suka…
Read More
Sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda a Katsina

Sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda a Katsina

Daga WAKILINMU A ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi shiyyar Arewa-maso-yammacin Nijeriya, sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda wanda hakan ya yi ajalin wasu manyan 'yan ta'addan a jihar Katsina. Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna cewa, luguden wutar da jirgin yaƙin sojojin sama (NAF) ya yi a Lahadin da ta gabata a yankin Ilela na jihar Katsina, ya haifar da galaba a kan 'yan ta'addan yankin tare da yi ajalin da damansu a sansanonin Gwaska Dankarami da Alhaji Abdulkarami, wanda duka su biyun gawurtattu ne. An gano cewa, 'yan ta'addan da aka halaka su ke…
Read More
Na kashe mutane sama da 20, cewar matashin ɗan ta’adda Naziru Sani

Na kashe mutane sama da 20, cewar matashin ɗan ta’adda Naziru Sani

*Ana biya na tsakanin N20000 zuwa N30000 bayan kowane hari da muka kai - Sani Daga BASHIR ISAH Matashin nan ɗan shekara 21 da ake zargin ɗan ta'adda ne, wato Naziru Sani, wanda ke aiki a ƙarƙashin gawurtaccen ɗan ta'adda Bello Turji, ya yi iƙirarin cewa ya kashe sama da mutum 20 a hare-hare da dama a faɗin Nijeriya. Matashin ɗan ta'addan ya bayyana hakan ne a lokacin da jami'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Gambo Isah, ya gabatar da shi a gaban manema labarai a babbar hedikwatar rundunar a ranar Talata. An cafke Sani…
Read More
Kundin Miftahul Futuhat ya zo da sabon salo a bege

Kundin Miftahul Futuhat ya zo da sabon salo a bege

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Cika da bunƙasar mawaƙi ita ce ya zamo ya shahara a dukkan salon waƙar da ya sa a gaba zai yi ta. Sarkin waƙar Masarautar Dutse, kuma Ɗan Buran na Masarautar Gobir, Aminu Ladan Abubakar Ala, yana ɗaya daga cikin mawaƙan wannan zamani a ƙasar Hausa da Allah ya yi wa wannan baiwa. Domin kuwa yana da baiwar shirya waƙa a kowanne ɓangarori na rayuwa wanda idan ya yi za ka ji kamar a nan fasahar sa ta ƙare, amma daga ya zo da wani salon sai kuma a ji a nan ma ya zama…
Read More
WASIƘU: ‘Babu alamar kasafin kuɗin 2022 zai taimaki talaka’

WASIƘU: ‘Babu alamar kasafin kuɗin 2022 zai taimaki talaka’

*Ya kamata talaka ya san cewa Allah kaɗai ne gatansa*Shan miyagun ƙwayoyi: Babbar barazanar da ke neman kassara matasan Nijeriya Assalamu alaikum, jarudar Blueprint Manhaja. Haƙiƙa mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da su ke yi mana ƙaiƙayi a rai tare da isar da saƙon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar ƙasa. Muna muku addu’ar Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasar wannan jarida mai farin jini baki ɗaya. Abin kunya ne kwarai da gaske a irin halin da wannan ƙasa tamu da ma al’umma musamman ma’aikata…
Read More
Mutane 36,000 sun ƙi amsar rigakafin Korona a Birnin Kudu

Mutane 36,000 sun ƙi amsar rigakafin Korona a Birnin Kudu

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Lissafi ya nuna kimanin mutane  36,000 ne suka ƙi amsar allurar rigakafin cutar Korona a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa.  Jawabin hakan ya biyo bayan wata ziyara da kwamatin kiwon lafiya mai karfin gaske ya kai ziyara ƙaramar hukumar domin ganin an yi gangami wajen nuna wa jama'a muhimmancin rigakafin Korona. Kwamitin a ƙarƙashin jagorancin babban Sakataren Hukumar Lafiya kuma muƙaddashin kwamashinan lafiya na Jihar Jigawa Dr Sambo Ibrahim tare da manyan muƙarrabansa a hukumar lafiya matakin farko sun je ƙaramar hukumar ta Birnin Kudu domin gano kura-kuran dake ƙaramar…
Read More
Ƙalubalen rayuwar ɗalibai a makarantu abin dubawa ne

Ƙalubalen rayuwar ɗalibai a makarantu abin dubawa ne

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani labari da ya ɗauki hankalin ’yan Nijeriya sosai cikin makon da ya gabata shi ne labarin kisan gillar da wani malamin makaranta a Jihar Kano ya yi wa wata ƙaramar ɗaliba mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar, bayan tsawon wata guda da ya yi yana garkuwa da ita, don jiran kuɗin fansa har Naira Miliyan 6 daga iyayenta. Wannan yana zuwa ne ba da jimawa ba, bayan wani kisan gillar da aka yi wa wani ɗalibi ɗan makarantar sakandire a Jihar Legas mai shekaru 12 mai suna Sylvester Oromoni, wanda wasu abokan karatun sa suka azabtar…
Read More
Ɓatagari sun halaka gyatuma bayan sun yi mata fyaɗe a Ondo

Ɓatagari sun halaka gyatuma bayan sun yi mata fyaɗe a Ondo

Wasu ɓatagari da ake zargin Fulani makiyaye ne, sun yi taron dangi wajen yi wa wata mata mai suna Mrs Roseline Joguntan fyaɗe sannan suka halaka ta bayan haka a ƙauyen Igbokoda da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Ilaje, jihar Ondo. Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa, an aikata wa matar wannan ɗanyen aiki ne a gonarta sa'ilin da ta je ɗibar 'yan'yan itatuwa kamar yadda ta saba tare da ɗaya daga cikin 'ya'yanta. Majiyar jaridar ta ce, "Bayan da marigayiyar ta ɗibi kwandon farko na 'ya'yan itatuwan ne sai ta buƙaci 'yarta ta ɗauka ta kai gida, ko da…
Read More
2023: Tambuwal ya bi sahun masu kwaɗayin mulkin Nijeriya

2023: Tambuwal ya bi sahun masu kwaɗayin mulkin Nijeriya

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya fito fili ya bayyana ƙudiransa na neman takarar shugabancin Nijeriya ya zuwa 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na PDP a jiharsa wanda ya gudana a jiya Litinin. Gwamnan ya ce, ya yanke shawarar takarar shugabancin ƙasa ne duba da irin nasarorin da ya samu a tarihin siyasarsa. A cewarsa, “A lokacin da 'yan Majalisar Wakilai zubi na bakwai suka buƙace ni da in nemi kujerar Shugaban Majalisa na gindaya musu sharuɗɗa. "Cewa a matsayina na ɗan Sakkwato mai biyayya, sai sun je…
Read More