Editor

9513 Posts
Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (wato WHO) sun nuna cewa, aƙalla gurɓata muhalli ya na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan 10 a duniya a cikin kowace shekara. Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirika da wannan matsala ta yi ƙamari a cikinta, kuma ita ce ta huɗu a cikin jerin ƙasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurɓata muhalli. Domin kuwa ƙididdiga ta nuna cewa, duk cikin ’yan Nijeriya dubu ɗari, akwai mutum ɗari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shƙar gurɓatacciyar iska a kowace shekara. A ƙasar…
Read More
Idon Mikiya: Buhari ya tare wa Shugaban NIA faɗa da gidan rediyon Vision FM

Idon Mikiya: Buhari ya tare wa Shugaban NIA faɗa da gidan rediyon Vision FM

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Gwamnatin Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’, wanda wani shahararren shiri ne a gidan rediyon Vision FM da ke Abuja da wasu jihohin Arewa, saboda tattaunawa kan taƙaddamar tsawaita naɗin da aka yi wa Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Alhaji Rufa'i Abubakar, da kuma zargin rashin iya aikinsa, lamarin da wasu ke kallo a matsayin tare wa shugaban na NIA faɗa da gidan rediyon na Vision FM. A cikin wata wasiƙa da ta aike wa Manajan Daraktan Gidan Rediyon Vision FM, wacce Blueprint Manhaja ta samu kwafi a…
Read More
Mun wuce lokacin jiran gwamnati ta ba mu aiki – Aisha Musa

Mun wuce lokacin jiran gwamnati ta ba mu aiki – Aisha Musa

"Akwai sana'o'i da yawa da za mu iya zamanantar da su" Daga ABUBAKAR M. TAHIR  A'isha Musa Auyo, matashiya ce wadda take digirinta na uku, kuma mai sana'ar girke-girke, wanda ta zaɓi ta ɗauki wannan ɓangaren domin samun cigaban rayuwarta. Kasancewarta wadda ta yi zurfi a ilimi boko da kuma jajircewarta a neman na kai ta sa Manhaja ta nemi tattaunawa da ita, don jin yadda ta taki wannan matsayi. A sha karatu lafiya: MANHAJA: Za mu so jin tarihinki a taƙaice.A'ISHA: Sunana A’isha Musa Auyo, an haife ni ranar 22 ga Fabrairu, 1991. Na yi makarantar firamare da sakandare…
Read More
Amfanin zogale ga lafiyar iyali (2)

Amfanin zogale ga lafiyar iyali (2)

Daga BILKISU YUSUF ALI Ci gaba kan amfanin zogale daga makon da ya gabata. Kamar yadda muka faɗa Zogale yana da matuƙar amfani a jikin ɗan’adam don haka masana kiwon lafiya suke yawan ambatonsa a wurin magance ƙanana da manyan cutoci. Zogale yana da tasiri Allah Subhanahu wata’ala ya yi masa albarka kasancewar bincike –binciken kimiyya sun tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama. A kimiyance ana yi wa zogale laƙabi da Moringa oleifera wato Drumstick tree a Turance. Zogale yana da tasiri kwarai a jiki amma fa yana da ƙa’ida wajen shanya shi ba a son…
Read More
Gidan aure fagen yaƙi ne!

Gidan aure fagen yaƙi ne!

Daga AMINA YUSUF ALI Barkan mu da sake haɗuwa a wani sabon mako a shafinmu na zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja.  Kamar yadda Bahaushe yakan ce, wai 'aure yaƙin mata'. To a gaskiya aure yaƙi ne na sosai ba ga mata kaɗai ba. A taƙaice ma akwai masanan da suke ganin shi kansa gidan auren ma fagen yaƙi ne.  Na san masu karatu za su ce fagen yaƙi kuma? Ba wani abu zai kawo wannan tunani ba, sai don ganin shi aure yana samo asali ne daga soyayya. Wacce take wanzuwa tsakanin masoya biyu, kuma so…
Read More
Matsalar tsaro ba ta hana mu fita aiki ba – Shugaban Direbobin Tanka

Matsalar tsaro ba ta hana mu fita aiki ba – Shugaban Direbobin Tanka

Daga MUHAMMADU MUJITABA BIN USMAN Shugaban ƙungiyar direbobin dakon man fetur na ƙasa, wato ‘Petroleum Tankers Drivers’ (PTD), shiyyar Kano, Katsina, Jigawa da Yobe, Alhaji Sani Malam Garba ya ce kansancewar wannan sana’a ita suka iya Allah kuma ya sa suka dogara da ita, ya ce suna yi wa Ubangiji godiya duk da matsalilin lalacewar hanya da kuma matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar, ya ce hakan bai hana su gudanar da aikin su ba. Sani ya kuma janyo hankalin gwamnati kan gyara hanyoyin ƙasar nan baki ɗaya da kuma shawara kan dakatar da janye tallafin man fetir da gwamnatin…
Read More
Hisbah ta ƙwace kwalaben giya 1,906 da kama mutum 92 a Jigawa

Hisbah ta ƙwace kwalaben giya 1,906 da kama mutum 92 a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ce ta ƙwace kwalaben giya 1,906 a sumamen da ta kai a lokuta daban-daban a faɗin jihar a shekarar da ta gabata, 2021. Kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Dahiru, shi ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN, a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Talatar makon jiya. Mallam Ibrahim ya ce sun yi nasarar ƙwace giyar ne a otal-otal da wuraren shan barasa daban-daban a faɗin jihar. Shugaban Hisbar ya kuma ce sun kama mutum 92 da suke zargi da aikata laifuka na baɗala daban-daban, waɗanda suka…
Read More
Yadda Farfesa Wakawa ya tsere wa tsara wajen kula da rayuwar al’umma

Yadda Farfesa Wakawa ya tsere wa tsara wajen kula da rayuwar al’umma

Daga ABDULLAHI GAMBO Farfesa Ibrahim Abdu Wakawa, ƙwararren likita ne da ya yi shura wajen cigaban rayuwar al'umma, mutum ne mai tsananin kishi da nuna jinƙai ga gajiyayyu da masu ƙaramin ƙarfi; shi ne Babban Darakta (CMD) kuma babban jami'in kula da lafiya a asibitin kula da masu matsalar ƙwaƙwalwa ta tarayyar Nijeriya da ke Maiduguri.  Wakawa ya yi ilimi mai zurfi a ɓangaren sanin ƙwayoyin cututtuka da kuma ilimin sanin gaɓoɓin ɗan Adam a Maiduguri, cikin shekarar 2001. Sanan ya samu horo na musamman a kan ilimin matsalar ƙwaƙwalwa a Kwalejin Sanin Gaɓoɓin ɗan Adam ta Afirka a shekarar…
Read More
2023: IBB ya yi wa Saraki mubaya’a

2023: IBB ya yi wa Saraki mubaya’a

Daga BASHIR ISAH Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana goyon bayansa ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki, kan ƙudirinsa na takarar kujerar shugaban Nijeriya don zama magajin Shugaba Buhari ya zuwa 2023. IBB ya bayyana goyon bayan nasa ga Saraki ne a lokacin da yake amsa buƙatar tawagar kamfen ɗin Saraki sa'ilin da suka ziyarce shi a gidansa da ke Minna, jihar Neja, ƙarƙashin jagorancin shugaban tawagar, Farfesa Hagher Iorwuese da Darakta-Janar ɗinsa, Chief Osaro Onaiwu. Tawagar yaƙin nema wa Saraki zaɓe ta ziyarci tsohon shugaban ƙasar ne musamman don nema wa…
Read More
Rashin fansho da giratuti ya mayar da tsaffin ma’aikata tamkar mabarata

Rashin fansho da giratuti ya mayar da tsaffin ma’aikata tamkar mabarata

Daga ZAHRADDEEN IBRAHIM KALLAH Wata babbar masifa da take neman zama ruwan dare a ƙasar nan shi ne, yadda gwamnatoci ke wulaƙanta ma’aikata tare da danne musu haƙƙoƙinsu. Abin takaicin da ya fi fitowa ƙarara shi ne yadda ma’aikata da suka gama aiki suke zama tamkar mabarata.  A yayin da suka ƙarar da ƙarfinsu wajen bauta wa ƙasarsu, tare da tunanin samun haƙƙoƙinsu don shirya rayuwa kafin ta Allah ta kasance, a lokacin ne wasu a can gefe za su yi babakere da kasafta waɗannan kuɗaɗe ko haƙƙoƙi.  Ire-iren waɗannan tsofaffin ma’aikata suna cikin matsananciyar buƙatun rayuwa, amma sun kwashe…
Read More