Editor

9513 Posts
Yan sanda sun kama masu garkuwa 14 a Jihar Jigawa

Yan sanda sun kama masu garkuwa 14 a Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse ’Yan sanda sun kama mutane 14 da ake zargi da garkuwa da mutane tare bindigogi ƙirar AK47 guda uku da kuɗi sama da Naira miliyan biyu.  Jawabin hakan ya fito ne daga bakin kakakin rundunar 'yan sanda Lawan Shisu Adam, inda ya ce sun samu narasa wajen kama su bayan sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargin.'Yan sandan sun fatattake su a yayin musayar wutar har sun harbi ɗaya a ƙafa. Lawan Shisu ya ci gaba da cewar sun gano maɓoyar 'yan ta'addar ne a dajin Ɗangwanki da kuma ƙauyen 'yan damo dukkansu…
Read More
Kifin ƙanƙara: Gwamnati ta ba mu lambar yabo kan tsaftar sana’armu – Sani Lawan Sani

Kifin ƙanƙara: Gwamnati ta ba mu lambar yabo kan tsaftar sana’armu – Sani Lawan Sani

Daga BABANGIDA GORA a Kano Sana'ar kifi mai ƙanƙara sana'a ce da ma fi akasari ba Hausawa ne suke gudanar da ita ba a da, amma a yanzu Hausawa sun yi mata kaka-gida. Wakilin Blueprint Manhaja, Babangida Gora, ya samu zantawa da shugaban ƙungiyar masu sayar da kifi mai ƙanƙara na Jihar Kano, Alhaji Sani Lawan Sani. Ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance. MANHAJA: Da farko, masu karatu za su so su san waye Alhaji Sani Lawan?SANI: To kamar dai yadda ka faɗa, sunana Alhaji Sani Lawal Sani, kuma ni ne shugaban masu sana'ar sayar da kifi mai kankara…
Read More
An fara samun bayanai kan halin da tsohon shugaba Kabore ke ciki

An fara samun bayanai kan halin da tsohon shugaba Kabore ke ciki

Hamɓararren shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, yana cikin ƙoshin lafiya kuma sojoji suna tsare da shi a wani gida da ke fadar shugabancin ƙasar, kamar yadda wata majiya ta jam'iyyarsa ta bayyana. Halin da Kabore da kuma inda yake ya zama muhimmin batu tun bayan da wasu sojoji suka hamɓarar da shi daga mulki a ranar Litinin, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagorantar kiran da a sake shi. A baya bayan nan ne kuma, wata majiya a jam’iyyar tsohon shugaba Kabore ta 'People's Movement for Progress' MPP, ta tabbatar yana cikin ƙoshin lafiya, amma babu ƙarin bayani kan…
Read More
’Yan sanda sun damƙe soja yana fashi da makami a Yobe

’Yan sanda sun damƙe soja yana fashi da makami a Yobe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dubun wani soja ta cika inda aka kama shi tare wa wasu mutum biyu bayan sun aikata fashi da makami a garin Damaturu, Jihar Yobe. ’Yan Sanda sun cafke sojan da abokan fashin nasa ne bayan sun kutsa gida wata mata a unguwar Sabon Pegi da tsakar dare ɗauke da bindiga ƙirar AK 47 da sauran muggan makamai suka yi mata fashi. An kama sojan da abokan fashinsa ne bayan sun yi wa matar awon gaba da mota ƙirar Peugeot 307 da tsabar kuɗi N250,000 da kuma wayar hannu ƙirar Nokia. “Bayan an kama su, sun…
Read More
An farmaki ofishin Jaridar This Day bayan shekaru 10 da harin Boko Haram

An farmaki ofishin Jaridar This Day bayan shekaru 10 da harin Boko Haram

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Wasu gungun mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a ofishin kamfanin Jaridar This Day da ke Abuja, inda suka yi barazanar sheƙe dukkan ma’aikatan kamfanin. Kafar Labarai ta Arise News, mallakin Kamfanin Jaridar This Day, ta ruwaito cewa, maharan da suke ɗauke da muggan makamai sun kutsa cikin harabar kamfanin ne da misalin ƙarfe uku na asuba. Harin na daren Alhamis na zuwa ne shekara 10 bayan harin bom da aka kai wa ofisoshin kamfanin na This Day da ke Abuja da Kaduna. Bayan shigar maharan cikin…
Read More
Aubameyang ya buƙaci ninkin albashin Ibrahimovic a AC Milan

Aubameyang ya buƙaci ninkin albashin Ibrahimovic a AC Milan

Ɗan wasan gaba na Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, yana neman sau biyu abin da Zlatan Ibrahimovic yake samu a AC Milan don komawa qungiyar ta qasar Italiya. AC Milan ita ce kulob na baya-bayan nan da ake alaƙanta ta da ɗan wasan mai shekaru 32, wanda a yanzu ba a san makomar shi ba a Emirates. Tun a ranar 6 ga watan Disamba, Aubameyang bai taka leda a Gunners ba, lokacin da Arsenal ta sha kashi da ci 2-1 a Goodison Park. An cire ɗan wasan na Gabon ne daga muƙamin kyaftin ɗin ƙungiyar bayan mako guda bayan wani sabon ladabtarwa…
Read More
Ban naɗa Babban Magatakardan Kotu don kasanewar sa Kirista ba – Alƙalin Alƙalan Bauchi

Ban naɗa Babban Magatakardan Kotu don kasanewar sa Kirista ba – Alƙalin Alƙalan Bauchi

*Ta gargaɗi sabbin kwamishinonin kotuna kan cin hanci Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Alƙalin Alƙalai a Jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar, ta nuna takaicin ta bisa yadda wasu ma’aikatan shari’a suke buga takardun bogi, rasitai, har ma da tambarin hukuma na kan su suna yin almundahanar karkata kuɗaɗen shiga ga gwamnati, domin arzurta kan su. Babbar Mai Shari’ar ta jiha ta bayyana cewar, bisa ƙoƙarin kawar da wancan mummunar ɗabi’a ce na karkata kuɗaɗen shigowa wa gwamnati, a yanzu aka buga wasu sabbin makamantan waɗancan takardu da sauran kayayyakin aiki masu alamun tsaro da zummar daƙile duk…
Read More
Cire tallafin mai: Dalilin Buhari na bar wa magajinsa damar hukunci

Cire tallafin mai: Dalilin Buhari na bar wa magajinsa damar hukunci

*NNPC na buƙatar Naira tiriliyan uku a 2022 Daga MAHDI M. MUHAMMAD da SANI AHMAD GIWA a Abuja A ƙarshe dai Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ta yi watsi da cece-kucen da ake yi na buƙatar ko akasin haka wajen cire tallafin man fetur, inda ta ce, ta bar zaɓin aiwatar da hakan ga wanda zai gaji ofishin Shugaban Ƙasa a 2023, saboda yanayin halin da tattalin arzikin Nijeriya da ma na ’yan Nijeriya ke ciki a halin yanzu. Kana kuma, idan shawarar ta wuce gaban Majalisar Dokoki ta ƙasa da ake sa ran za ta ba ta wasu…
Read More
Hukumar Kwastam: CBN ya kawo ƙarshen cajin masu safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba

Hukumar Kwastam: CBN ya kawo ƙarshen cajin masu safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya, CBN ya gabatar da wani sabon tsarin da zai hana hukumar Kwastan cajar masu shigowa ko fita da kaya a ciki da wajen Nijeriya ba bisa ƙa'ida ba. CBN ɗin ya ƙaddamar da sabon tsarinsa na 'evaluator' da 'e-Invoice' waɗanda da su ne tsari na yanar gizo da 'yan kasuwa za su dinga amfani da su  don biyan kuɗin shige da fice da kaya ba tare da an yi musu lissafin awon igiya kamar yadda yake faruwa a baya.  Wannan bayani dai ya fito ne daga wata sanarwa da Babban Bankin ya wallafa…
Read More
Matakan da gwamnati ke ɗauka kan tsaro ya taimaka wajen haɓaka kasuwancin kayan gwari – Shugaba

Matakan da gwamnati ke ɗauka kan tsaro ya taimaka wajen haɓaka kasuwancin kayan gwari – Shugaba

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Shugaban kasuwar kayan gwari ta ƙasa da ƙasa ta Mile 12 da ke Legas, Alh Shehu Usman Jibril, ya bayyana cewa matakan da gwamnati ke ɗauka na inganta lamurran tsaro a Nijeriya ya taimaka wa lamurran kasuwancin kayan gwari, musamman na iya safarar su daga jihohin Arewa dake fama da matsalar tasaro zuwa kasuwar kayan gwari ta Mile 12. Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara da jagororin kasuwar ke gudanarwa a duk shekara domin tattauna nasarori da irin ƙalubalen da masu noma da kasuwancin kayan gwarin ke fuskanta, taron da a wannan…
Read More