28
Jan
Daga AISHA ASAS a Abuja Jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya, kuma shugaban ƙungiyar yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, wato Movement of North East Organization Forum, Hon. Alhaji Abdulrahman Buba Kwacam, ya bayyana cewa babban kuskure ne ga 'yan arewa su zaɓi mutumin da wata jam'iyya ta tsayar daga kudancin ƙasar nan da nufin zamewa shugaban ƙasar Nijeriya a zaɓe mai zuwa na 2023. Kwacam ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya kira a gidan sa da ke Abuja ranar Alhamis ɗin makon jiya, inda ya nuna tsananin damuwar sa dangane da yanayin da arewacin ƙasar…
