Editor

9513 Posts
Ziyarar Buhari a Sakkwato

Ziyarar Buhari a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato A yau ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jihar Sakkwato inda ya ƙaddamar da katafaren kamfanin siminti mallakar kamfanin BUA da kuma jajanta wa al'ummar jihar dangane da rasehe-rashen da aka samu a jihar sakamakon matsalar tsaro. Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal tare da muƙarrabansa ne suka tarbi Buhari da tawagarsa bayan da suka sauka a filin jirgin sama. Sa'ilin da Buhari ya ziyarci Fadar Sarkin Musulmi Ana sa ran kamfanin Simintin BUA da Shugaba Buhari ya ƙaddamar ya riƙa samar da siminti har ton milyan 3 don amfanin al'umma. Yayin…
Read More
Nijeriya ta kwaso ‘ya’yanta 167 da suka maƙale a Libiya

Nijeriya ta kwaso ‘ya’yanta 167 da suka maƙale a Libiya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Sha'anin Masu Hijira ta Ƙasa-da-ƙasa (IOM) sun dawo da ƙarin 'yan Nijeriya su 167 daga ƙasar Libiya waɗanda suka maƙale a ƙasa bayan da aka yi safararsu don ayyukan aikatau. Malam Kabiru Musa wanda shi ne mai sanya ido kan shirin Nijeriya a Libiya, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata a Abuja. Musa ya ce 'yan Nijeriyar su 167, sun baro babban filin jirgin saman Mitiga da ke Tripoli ran Talata da daddare inda suka iso babban filin jirgin saman Murtala Muhammed…
Read More
2023: Okorocha ya ɗauri niyyar takarar shugaban ƙasa

2023: Okorocha ya ɗauri niyyar takarar shugaban ƙasa

Daga BASHIR ISAH Sanata Rochas Okorocha na jam'iyyar APC daga jihar Imo, shi ma ya bi sahun masu kwaɗayin mulkin Nijeriya ya zuwa 2023. Okorocha wanda shi ne sanata mai wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Tarayya, ya bayyana muradinsa na takarar shugaban ƙasa ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan inda shi kuma ya karanto wasiƙar yayin zaman majalisar a jiya Laraba. Sanatan ya ce yana da shirin da zai yi hira da 'yan jarida ran 31 ga Janairu a Babban Zauren Taro da ke Abuja don bayyana wa duniya ƙudirin nasa. Da…
Read More
‘Yan bindiga sun sace malami da wasu mutum huɗu a Yobe

‘Yan bindiga sun sace malami da wasu mutum huɗu a Yobe

Daga WAKILINMU Rahotanni daga jihar Yobe na nuni da cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin makarantar firamare tare da wasu mutum huɗu. Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar ta fito ta tabbatar da aukuwar lamarin a yau Laraba, inda ta ce 'yan bindiga sun sace Babagana Kachalla wanda malami ne a makarantar Central Primary School, Buni Yadi, tare da wasu mutum huɗu a ƙauyen Madiya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Gujba a jihar. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, shi ne ya bada tabbacin hakan a Damaturu, babban birnin jihar. Abdulkarim ya lissafo…
Read More
Sojoji sun lalata maɓuya da kasuwar Boko Haram/ISWAP a Borno

Sojoji sun lalata maɓuya da kasuwar Boko Haram/ISWAP a Borno

Daga BASHIR ISAH Hedikwatar Runduhar Sojojin Nijeriya ta ce, dakarunta na '401 Special Force Brigade' tare da haɗin gwiwar '19 Brigade' a Baga sun yi nasarar lalata maɓuyar Boko Haram/ISWAP sa'ilin da suke sintiri a yankunan Kauwa da Gudumbali a jihar Borno a ranar Talatar da ta gabata. Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na facebook a ranar Laraba. Ta ce dakarunta sun samu lalata maɓuyar mayaƙan ne yayin da suke aikin tsaftace yankunan da lamarin ya shafafa daga harkokin 'yan ta'adda, tare da cewa za ta yi ƙarin bayani kan lamarin…
Read More
Tattaunawa ta musamman da Sheikh Ibrahim Mansoor

Tattaunawa ta musamman da Sheikh Ibrahim Mansoor

Daga BILKISU YUSUF ALI Sheikh Ibrahim Mansoor Malami ne matashi kuma mabiyin ɗariƙar Tijjaniya, amma kuma wanda a kullum fatansa shine a haɗa kai a zauna lafiya tsakanin dukkan Musulmi ko kuwa masu bambancin aƙida ne, inda Sheikh Mansoor ya kasance bai yarda da rarrabuwa ba, don aƙida. Ga dai yadda Wakiliyar Blueprint Manhaja, BILKISU YUSUF ALI, ta gana da shi: Za mu so mu ji taƙaitaccen tarihinkaSunana Ibrahim amma mahaifina yana kirana Inyas kakana yana kira na Barhama ‘yan’uwana suna kirana Shehu. Sunan mahaifina malam Mansur. An haifeni a cikin garin Kaduna a wata unguwa da ake kirantaTudun Nufawa…
Read More
Amfanin zogale ga lafiyar iyali

Amfanin zogale ga lafiyar iyali

Daga BILKISU YUSUF ALI Tambaya:Salam. Anti Bilkisu, Ina da tambaya kan muhimmancin zogale ga lafiya, musamman lafiyar iyali. Amsa:Zogale yana da matuƙar amfani a jikin ɗan’adam don haka masana kiwon lafiya suke yawan ambatonsa a wurin magance ƙanana da manyan cutoci. Zogale yana da tasiri Allah Subhanahu wata’ala Ya yi masa albarka kasancewar bincike-binciken kimiyya sun tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama. A kimiyance ana yi wa zogale laƙabi da Moringa oleifera wato Drumstick tree a Turance. Zogale yana da tasiri kwarai a jiki amma fa yana da ƙa’ida wajen shanya shi ba a son a…
Read More
Martabar sarakunan gargajiya da ƙalubalen tsaro

Martabar sarakunan gargajiya da ƙalubalen tsaro

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshen makon da ya gabata ne aka gudanar da taron tunawa da Marigayi Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato a wani gagarumin taro da aka gudanar a birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gidauniyar Tunawa Da Sardauna, wanda aka yi wa taken 'Farfaɗo da Masarautun Gargajiya Don Inganta Tsaro Da Zaman Lafiya A Arewa'. Wannan babban taro ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa, ministoci, ’yan majalisu, sarakuna, malamai, malaman jami'o'i da sauran su. An kuma gabatar da jawabai masu kama hankali sosai, dangane da…
Read More
Yadda aka yi wa basarake da abokansa kisan gila a Ogun

Yadda aka yi wa basarake da abokansa kisan gila a Ogun

Daga BASHIR ISAH Al'ummar Agodo da ke yankin ƙaramar hukumar Ewekoro a jihar Ogun sun faɗa cikin yanayi na alhini da firgirci a ranar Litinin ɗin da ta gabata sakamakon kisan gilan da wasu da ba a kai ga sanin ko su wane ne ba suka yi wa sarkin yankin, Oba Ayinde Odetola. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, aika-aikar ta rutsa da wasu abokan sarkin su uku wanda aka ƙona su har lahira. Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa kisan na da nasaba da rikicin sarautar Alagodo. An ce da ma tun farko akwai kwantacciya kan ko…
Read More
Nijeriya da Sao Tome za su yi haɗin gwiwa wajen yaƙi da matsalar tsaro

Nijeriya da Sao Tome za su yi haɗin gwiwa wajen yaƙi da matsalar tsaro

Daga AISHA ASAS Nijeriya ta bayyana cewa za ta yi aiki tare da ƙasar Sao Tome wajen yaƙi da matsalolin tsaron don amfanin ƙasashen biyu Babban Hafsan hafsoshin rundunar tsaro na Nijeriya, Janaral Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a lokacin ya karɓi banƙuncin takwaransa na ƙasar Sao Tome, Janar Idalecio Pachire, a ofishinsa da ke Abuja. Irabor ya ce had'ɗin kai tsakanin mayaƙan ƙasashen biyu na da matuƙar amfani, musamman wajen tunkarar matsalar tsaro da ake fama da ita a wannan zamani. Tattaunawar jagororin biyu ta taɓo batun ƙalubalen tsaro a gabar tekun Guinea da irin rawar da ƙasashen…
Read More