Editor

9513 Posts
An nemi ƙungiyoyi a Jihar Sakkwato su cire siyasa a tsakaninsu

An nemi ƙungiyoyi a Jihar Sakkwato su cire siyasa a tsakaninsu

Daga AMINU AMANAWA Sakkwato Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi na Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) shine ya bayyana hakan a lokacin da mambobin ƙungiyar masu kiran kafafen yaɗa labarai ta jihar suka kai ziyara a ofishin hukumar. Shugaban ya yaba wa 'ya'yan ƙungiyar akan jajircewar su da kuma gudanar da ayyukan cigaba a cikin al'umma. Shugaban ya yaba musu akan namijin ƙoƙarin da suka yi na bayar da Tallafin ga 'yan gudun hijira ta hannun hukumar Zakka da Waƙafi a 'yan kwanakin nan. Haka ma shugaban ya janyo hankalin mambobin ƙungiyar da su cire saka siyasa ga…
Read More
An buɗe rukunin Kamfanonin RUSBI a Kano

An buɗe rukunin Kamfanonin RUSBI a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An buɗe rukunin  kamfanonin sarrafa abubuwa daban-daban, Kamfanin mai suna Rufa'i Sule Bichi wato RUSBI wanda mai tallafa wa al'umman nan  Alhaji Rufa'i Sule Bichi ya buɗe, a ranar Talata da ta  gabata a ƙaramar hukumar Kumbotso cikin birnin Kano. Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Ibrahim Aminu Tsanyawa. Kwamishina Dakta Tsanyawa ya yi jinjina ga Alhaji Rufa'i Bichi dangane da irin wannan babban yunƙuri, sannan ya yi kira ga masu hali da su yi koyi da irin wannan aiki domin cigaban al'ummar Kano da ƙasa bakiɗaya. Rukunin…
Read More
Rashin ƙa’idojin rubutu na jirkita saƙon marubuci – Ibrahim Nayaya

Rashin ƙa’idojin rubutu na jirkita saƙon marubuci – Ibrahim Nayaya

“Akwai tasirin ƙa'idojin rubutu a litattafan Hausa” Daga AISHA ASAS Ɗaya daga cikin dalilan da masana su ka ce ya ciyar da rubutun Hausa ko a ce rubutun 'Adabin Kasuwar Kano' baya shine, kurakuren da su ka yawaita a cikin littattafan. A na ɗora alhakin wannan kan su marubutan litattafan, saboda kasancewar su ne masu wuƙa da nama a lamarin. Duk da haka, su kansu masanan na da na su kaso a wannan matsala, duba da cewa, da yawa daga cikin marubutan ba masu sani ne a kan Hausa ba. Ko da yake idan aka yi duba da ƙarancin sani kan…
Read More
Kashe Hanifa: Gwamnatin Kano ta janye shaidar gudanarwa ga makaratun kuɗi

Kashe Hanifa: Gwamnatin Kano ta janye shaidar gudanarwa ga makaratun kuɗi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ranar Litinin da ta gabata Gwamnatin jihar Kano ta janye duka shaidar gudanarwar da ta bai wa makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar domin sabunta su. Kwamishinan Ilimin jihar, Malam Muhammad Sanusi-Kiru ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano. Sanusi-Kiru ya nasabta ɗaukar wannan mataki da gwamnatin Kano ta yi da kashe Hanifa Abubakar, 'yar shekara 5 kuma ɗaliba a makarantar Noble Kids Comprehensive College, wanda aka zargi mai makarantar da aikatawa. Ya ci gaba da cewa, an janye shaidar gudanarwar ga makarantun ne don bayar da damar sabuntawa da kuma…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya dakatar da shirin cire tallafin fetur

Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya dakatar da shirin cire tallafin fetur

Gwmanatin Tarayya ta bayyana dakatar da shirinta na janye tallafin fetur har sai abin da Allah Ya yi. Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yau a Abuja. Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan sabbin kafofin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, dakatar da shirin ya biyo bayan rashin goyon baya da Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna ne kan cire tallafin na fetur.
Read More
WASIƘU: Zaɓin ’yan Nijeriya a 2023

WASIƘU: Zaɓin ’yan Nijeriya a 2023

*Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin ’ya’yanku*Kira ga matasa su guji faɗa wa cikin hatsarin sha’awa Duk da cewa ba matsayi guda ne kaɗai ake zaɓe ba amma wanda aka fi magana a kai guda ne. Magajin kujerar shugabancin ƙasa. Amma kafin akwai ta gwamnonin jihohi da ta ’yan majalissun jihohi zuwa na tarayya don haka mu dubi hasashen makomar kujera ta ɗaya bayan zaɓen 2023. Tun a karon farko an ji wasu ’yan siyasa daga ɓangarorin kudanci sun bayyana muradin su. Tsohon gwamnan Legas Chief Bola Ahmed Tinubu kuma jigo a Jam'iyya mai mulki APC…
Read More
Amnesty ta bayyana damuwa kan makomar aikin Jarida a Nijar

Amnesty ta bayyana damuwa kan makomar aikin Jarida a Nijar

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta bayyana fargaba a game da makomar ‘yancin aikin jarida a Jamhuriyar Nijar, bayan da kotu ta yanke hukuncin ɗaurin talala a kan wasu ‘yan jaridu biyu saboda sake wallafa labarin da wata jarida ta wallafa dangane da matsalar fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar. A ranar 3 ga wannan wata na Janairu ne kotu a Yamai ta yanke hukuncin ɗaurin talala a kan Samira Sabou da Moussa Aksar saboda sun sake wallafa labaran da wata Cibiya da ke Geneva mai suna Global Initiative Against Transnational Organized Crime (GITOC) ta buga, da ke…
Read More
Bala Chamo ya zama Shugaban ALGON na Arewa

Bala Chamo ya zama Shugaban ALGON na Arewa

Daga BILKISU YUSUF ALI An zaɓi Shugaban ƙaramar hukumar Dutse da ke Jihar Jigawa, Hon. Bala Usman Chamo, a matsayin Shugaban Ƙungiyar Ciyamomin Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) mai kula da yankin arewacin Nijeriya. Hon. Chamo, wanda kuma shi ne Shugaban ALGON na Jihar Jigawa, an zaɓe shi shugaban ƙungiyar na Arewa ne a ranar 15 ga Janairu, 2022, inda shugabannin ƙananan hukumomin suka nuna masa yaƙininsu na kawo cigaba ga yankin Arewa bisa la’akari da ƙwazonsa wajen sauke nauyin da ke kansa. Wata majiyar ƙungiyar ta ce, “Hon. Chamo ya yi ayyuka na raya garin Dutse da kuma…
Read More
Gwamnatin Katsina ta raba wa ƙungiyoyi kayayyakin aikin gayya

Gwamnatin Katsina ta raba wa ƙungiyoyi kayayyakin aikin gayya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sama da buhunan siminti dubu uku da banduran kwanan rufin gidaje saba’in ne Gwamnatin Jihar Katsina ta sayo domin raba wa ƙungiyoyin aikin gayya a ƙananan hukumomi 18 da ke faɗin jihar. Mai bai wa gwamnan Jihar Katsina shawara a kan ci gaban al’umma da ƙungiyoyin aikin gayya, Alhaji Bishir Abdullahi Dangote ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamar da rabon kayan kashi na farko wanda ya gudana a harabar ma’aikatar da ke kusa da gidan gwamnatin jihar. Kamar yadda ya bayyana, kashin na farko da aka ƙaddamar za a tallafa wa ƙungiyoyi 30 ne…
Read More
Abinda ya sa NLNG hana sayar da gas ga ƙasashen waje

Abinda ya sa NLNG hana sayar da gas ga ƙasashen waje

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai hukumar hada-hadar Gas ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya (NLNG) ta ba da odar hana fita da gas zuwa wasu ƙasashen sai dai a sayar da shi ga dilolin cikin gida. Abinda ya jawo ruguzowar farashin gas ɗin girki ga al'ummar ƙasar.  Wannan umarni na NLNG ya zo ne a dai-dai lokacin da jama'a suke kokawa da yadda farashin gas ɗin ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar tun daga watanni biyar da suka wuce.  Hukumar Rarraba gas ɗin ta Nijeriya ta bayyana cewa, ana sa ran nan gaba kaɗan za ta sauko da…
Read More