24
Jan
Daga BAKURA K. MUHAMMAD A Bauchi Mafi yawancin kuɗaɗe daga cikin nairori tiriliyan guda da biliyan ɗari biyar da Gwamnatin Tarayya ta keɓe domin tallafa wa ‘yan ƙasa marasa ƙarfi sun salwance cikin aljifan jami’an gwamnati da masu riƙon muƙaman siyasa da ke ƙarƙashin jagorancin gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari, a cewar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Gwamnan, ya kuma yi la’akari da cewar, shirin taimako na SIP wanda kututun sa ake shirin domin taimaka wa marasa ƙarfi su fice daga cikin ƙangin talauci, tare da inganta rayuwarsu, ana karkata su ne bisa rashawa da cin hanci domin…
