Editor

9513 Posts
Fasinjojin AZMAN sun yi zanga-zanga kan soke tafiya a Kano

Fasinjojin AZMAN sun yi zanga-zanga kan soke tafiya a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗaruruwan fasinjojin jirgin Azman ne a safiyar ranar Talata da ta gabata suka mamaye hedikwatar kamfanin domin nuna rashin amincewarsu da soke jirginsu. Da farko an shirya jirgin Kano zuwa Legas da ƙarfe 7:30 na safe. Manhaja ta kalato cewa fasinjojin da suka yi zanga-zangar sun koka da rashin jin daɗin sokewar da aka yi musu ba zato ba tsammani, inda suka nuna rashin amincewarsu da lamarin saboda babu wata sanarwa kafin ɗaukar matakin. Fasinjoji biyu, mata da miji da za su bi jirgin a kan hanyarsu ta zuwa Landan sun nuna takaicinsu kan abun…
Read More
Everton ta kori Rafael Benitez kwanaki 200 bayan ba shi aikin horarwa

Everton ta kori Rafael Benitez kwanaki 200 bayan ba shi aikin horarwa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta kori Manajanta Rafael Benitez kwanaki 200 cif bayan ba shi aikin horarwa daidai lokacin da ƙungiyar ke ci gaba da fuskantar tarin rashin nasara a wasanninta na Firimiya. Benitez wanda ya yi aiki tsawon lokaci da Liverpool da ke matsayin babbar abokiyar dabin Everton ya karɓi ragamar ƙungiyar ne a watan Yunin 2021. Sanarwar da ƙungiyar ta wallafa a shafinta ta tabbatar da raba gari da kocin nata bayan shan kaye a wasanni 9 cikin wasanni 13 da ƙungiyar ta doka a baya-bayan nan ƙarƙashin gasar firimiyar Ingila. Rashin nasara ta baya-bayan nan da…
Read More
Shugaba Buhari ya aika da saƙo ga kocin Super Eagles

Shugaba Buhari ya aika da saƙo ga kocin Super Eagles

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci kocin Super Eagles, Austin Eguavoen da ya ci gaba da kuma zarce yadda ya kai ga nasara a gasar cin kofin Afrika (AFCON) da ake yi a Kamaru. A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Larabar da ta gabata ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina, Buhari ya bayyana cewa ƙasar na fatan samun nasara guda bakwai a gasar. Shugaba Buhari ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na lashe dukkan wasanninta na rukuni wanda ya sa ta tsallake zuwa zagaye na biyu a…
Read More
An kama fitaccen kwamandan ’yan fashin daji a Zamfara da bindigogi 200

An kama fitaccen kwamandan ’yan fashin daji a Zamfara da bindigogi 200

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce an kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Katare a ranar Asabar da ta gabata. Shinkafi ya bayyana hakan ne ga manema labarai, inda ya ƙara da cewa Katare yakan gudanar da hare-haren sa ne a kusa da Lambar Bakura-Tureta da dajin Raba a jihar Sakkwato. A cewarsa, abubuwan da aka samu daga hannunsa akwai bindigogin AK-47 guda 200 a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa zuwa wani dajin da ke jihar. Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya ce kwamandan ‘yan fashin bai wuce shekara…
Read More
Bankin Standard Chartered zai rufe rassansa a Nijeriya

Bankin Standard Chartered zai rufe rassansa a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai ana tsammanin rassa goma sha uku ne daga rassan Bankin Standard Chartered ne za su cigaba da aiki a ƙasar Nijeriya. Hakan ta faru a dalilin yunƙurin bankin na ganin ya rage wasu sassansa da ke ƙasar nan.  Shi dai wannan Rukunin Bankunan na Standard Chartered na Nijeriya yana da Shalkwatarsa ne a birnin Landan ta ƙasar Ingila. Babban banki ne wanda  yake tafiyar da harkokin kasuwancin kuɗi iri daban-daban.  Jaridar Bloomberg ita ta yi wannan rahoto a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata. Inda ta bayyana cewa, bankin zai dakatar…
Read More
Shekaru ma fi hatsari a tarbiyyar ’ya mace

Shekaru ma fi hatsari a tarbiyyar ’ya mace

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Yau za mu yi magana a kan shekarun da dukkan mace baliga take jin kanta, daga shekara goma sha huɗu zuwa Shekara Ashirin. A lokacin ne da maƙerin halitta na 'yanmatantaka ya nuna a jikin mace. Wato komai nata ya fito na budurci, ta ƙosa kenan. To lokacin ne uwa kuma za ta shiga yanayi na damuwa da rayuwar hatsari ga yaranta mata da suka shiga wannan shekarun sai ta ɗauki kyakkyawan  mataki, da sa ido sosai a kan yaranta mata. Wannan su ne shekarun da iyaye ke cewa ma fi hatsari a kan iyalinsu don…
Read More
Imo: Magidanci ya faɗa a komar ‘yan sanda bayan da ya yi yunƙurin halaka ɗan maƙwabcinsa don tsafi

Imo: Magidanci ya faɗa a komar ‘yan sanda bayan da ya yi yunƙurin halaka ɗan maƙwabcinsa don tsafi

Daga BASHIR ISAH Wani magidanci mai suna Mr Francis Chukwura, ya faɗa a komar yan sandan jihar Imo bisa zargin yunƙurin halaka ɗan maƙwabcinsa don neman cika muradinsa na tsafi. Tuni dai wannan al'amari ya yi silar Chukwura ya rasa aikinsa a inda yake aiki, wato FMC Owerri. Cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Alhamis da ta gabata dangane da kamun wanda ake zargin, mai magana da yawun 'yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam, ya ce wanda ake zargin ya yaudari Henry Ekwos, ɗan shekara 14, zuwa ɗakinsa inda ya yi yunƙurin kashe shi bayan kuma…
Read More
Abin da ya sa na keta maƙogoron abokin karatuna, cewar ɗalibin sakandare a Maiduguri

Abin da ya sa na keta maƙogoron abokin karatuna, cewar ɗalibin sakandare a Maiduguri

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta cafke wani matashi mai suna Umar Goni ɗan shekara 16, kuma ɗalibi a makarantar 'Elkanemi College of Islamic Theology Maiduguri', bisa yunƙurin halaka wani ɗalibi abokin karatunsa mai suna Jubril Mato. Tun farko, jaridar Neptune Prime ta rawaito labarin yadda Umar Goni ya keta maƙogoron abokin karatunsa Jubril Mato, dan shekara 12, da makami a nan makarantar tasu. Daga bayanan da ya yi wa 'yan sanda, Goni ya yi iƙirarin cewa ya aikata wannan ɗanyen aiki ba don komai ba, sai don neman iyayensa su cire shi daga tsarin kwana…
Read More
Buhari bai taɓa ba da umarnin cire tallafin fetur ba – Shugaban Majalisar Dattawa

Buhari bai taɓa ba da umarnin cire tallafin fetur ba – Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa, ba za a cire tallafin man fetur ba a yanzu haka ba, saɓanin yadda wasu kafafen sada zumunta da na zamani suka ruwaito. Sanata Lawan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ranar Talata a Abuja. A cewarsa, Buhari bai taɓa bai wa kowa izinin a cire tallafin man fetur ba kamar yadda ake ta cece-kuce a wasu sassan…
Read More
Tufka da warwara kan cire tallafin fetur

Tufka da warwara kan cire tallafin fetur

•Rahoton Majalisar Zartarwa ya ci karo da kalaman Shugaban Majalisar Dattawa •Tallafin wata shidan farko mu ka saka a kasafin 2022 – Ministar Kuɗi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatoci da dama da suka shuɗe a Nijeriya sun ci alwashi da ɗauka wa talakawan ƙasar alƙawarin za su sayi man fetur cikin rahusa ta hanyar ware wasu maqudan kuɗaɗe, domin bayar da tallafi.    Sai dai wasu alƙaluma da gwamnati ke fitarwa sun nuna cewa, a na kashe kusan Naira biliyan 250 duk wata a matsayin kuɗin tallafin, wanda gwamnati a yanzu ke cewa ya yi yawa, kuma ta…
Read More