Editor

9513 Posts
Yadda ISWAP suka kashe Janar Dzarma Zirkusu a wani kwanton ɓauna

Yadda ISWAP suka kashe Janar Dzarma Zirkusu a wani kwanton ɓauna

Daga BASHIR ISAH A juma'ar da ta gabata sojojin Nijeriya suka far wa mayaƙan ISWAP jim kaɗan bayan sun idar da sallar Juma'a, inda sojojin suka yi wa 'yan ISWAP luguden wuta ta sama da ƙasa, lamarin da ya haifar da samun galabar sojojin a kan 'yan bindigar inda suka halaka da damansu tare da jikkata wasu. Bayanai sun nuna 'yan ISWAP na tsaka da tattaunawa ne tare da sabon kwamandansu, Sani Shuwaram a Sabon Tumbun da kuma Jibularam a yankin ƙaramar hukumar Marte, jihar Borno yayin da sojojin suka yi musu kwanton ɓauna. Majiya daga rundunar sojojin sun shaida…
Read More
An kashe kwamandojin ISWAP

An kashe kwamandojin ISWAP

Daga BASHIR ISAH Sojojin Nijeriya sun kashe wani babban kwamandan mayaƙan ISWAP tare da wasu mayaƙansa a wani harin ramuwar gayya da suka kai wa mayaƙan a yankin Askira-Uba na jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna mayaƙan na ISWAP sun kai wa so'joji hari don rama ragargazar da suka yi musu da jirgin yaƙi a Juma'ar da ta gabata tare da kashe musu mambobi da dama, wanda hakan ya yi ajalin Brigadier-General Dzarma Zirkushi a yankin Chibok tare da wasu sojoji su uku a ƙauyen Bungulwa kusa da Askira Uba a ranar Asabar. An ce…
Read More
Ya gwammace zama a kurkuku da zama da matarsa

Ya gwammace zama a kurkuku da zama da matarsa

Wani magidanci mai shekaru 30 a duniya ya bayyana cewa, ya gaji da rigimar matarsa, inda ya roƙi jami’an ’yan sanda da su tsare shi. A cewarsa, sam ba zai iya ci gaba da kasancewa tare da matar ta sa ba saboda irin tada masa da hankali da ta ke yi da fitinarta a kullum, inda ya ce, gara masa zaman gidan kurkuku. Ya ce, “Ina son tafiya gidan kurkuku, domin ba zan iya ci gaba da jure halin matata ba.” Mutumin ɗan ƙasar Albaniya wanda ya fito daga Guidonia, wani gari a wajen birnin Rome ya shafe tsawon watanni…
Read More
An ɗaure lauya bisa tafka ƙarya a gaban kotu

An ɗaure lauya bisa tafka ƙarya a gaban kotu

Mai shari’a Mojisola Dada ta kotun hukunta manyan laifuka da ke zama a Ikeja a Jihar Legas ta ɗaure wani lauya Kenneth Ajoku hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zaɓin biyan tara bisa laifukan ƙarya da kuma ƙirƙirar shaidar ƙarya. Alƙalin kotun ta kama shi da laifuka biyu a cikin wasu tuhume-tuhume biyun da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ke yi a kansa. Rahotanni sun bayyana cewa, an fara tuhumar Ajoku ne tun a shekarar 2017 lokacin da hukumar EFCC ta samu bayanan sirri game da gungun ’yan damfara da ke sayar…
Read More
Yadda aka fara haska fim ɗin Fanan a Sinima

Yadda aka fara haska fim ɗin Fanan a Sinima

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A yanzu haka dai an fara haska shahararren fim ɗin  'FANAN' a Cinimar Platinium da ke kan titin Zaria, kusa da Masallacin Umar Bin Khaddab da ke cikin garin Kano. An daɗe dai ana ta sanar da bayyanar fim ɗin wanda aka shirya shi tare da kammala aikin sa kusan shekaru biyu da suka gabata. Kuma an ƙiyasta fim ɗin ya laƙume miliyoyin Naira. Fim ɗin dai na tsohuwar jaruma Mansurah Isah ne, wanda aka shirya shi a ƙarkashin kamfanin 'Today's Life' tare da haɗin gwiwar wasu kamfanoni domin samun ingantuwar aikin. A lokacin da…
Read More
Yadda zaɓen ƙungiyar MOPPAN reshen Abuja ya gudana

Yadda zaɓen ƙungiyar MOPPAN reshen Abuja ya gudana

Daga IBRAHIM HAMISU a Abuja Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya Fina-finai ta Nijeriya, Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) reshen Abuja ta gudanar da zaɓen shugabanni a ranar Asabar 30 ga Oktoba, 2021, a harabar ɗakin taro na kamfanin Kufaina Films da ke Abuja. Malaman zaɓen dai sun fara tantance 'yan takara da misalin ƙarfe 10:30 na safe. An kuma kammala tantance su ne zuwa ƙarfe 11:30, inda aka tantance 'yan takara guda 10. An fara kaɗa ƙuri'a ne da misalin 11:30 na safiyar a ƙarƙashin kulawar Babban Ma'ajin ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa, Alhaji Bala Mu'azu Kufaina. Bayan ƙirga ƙuri'un…
Read More
Mun kama ɗan sanda bogi, ɗan jarida da malamin addini bisa afka wa gidan alƙali – ’Yan Sanda

Mun kama ɗan sanda bogi, ɗan jarida da malamin addini bisa afka wa gidan alƙali – ’Yan Sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar `yan sandan Nijeriya ta yi nasarar kama wasu mutane 14 da ake zargi da shiga gidan Mai Shari'a Mary Odili kwanakin baya. Daga cikin waɗanda ake zargin har da wani ɗan sandan bogi mai suna Lawrence Ajodo da wani ɗan jarida da kuma malamin addinin Musulunci. Da ya ke gabatar da mutanen ga manema labarai a Abuja jiya Alhamis, Kakakin 'Yan Sanda na Ƙasa, Mista Frank Mba, ya ce, an kama mutanen ne bayan ƙaddamar da bincike. “Har yanzu akwai aƙalla mutum 10 da 'yan sanda ke alaƙantawa da lamarin da suka tsere,”…
Read More
Zafin kishi ya sa uwa kashe ’ya’yanta biyar

Zafin kishi ya sa uwa kashe ’ya’yanta biyar

Wata kotu ta yanke wa wata mata a birnin Solingen na yammacin ƙasar Jamus hukuncin ɗaurin shekaru 15 bayan samunta da laifin kashe biyar daga cikin ’ya’yanta na cikinta guda shida. Yaran da ta halaka ƙanana ne, domin bas u ma wuce shekara ɗaya zuwa takwas ba. Kotun wacce ke da zama a birnin Wuppertal ta ƙasa gano wani dalili da zai sa a yi wa matar mai shekaru 28 a duniya uzuri, saboda haka ta soke batun sakinta bayan kammala wa'adin shekaru 15 a gidan yari. A yayin shari'ar, mai shigar da ƙarar ya yi zargin cewa ta fara…
Read More
Buhari ga Bankin Musulunci: ’Yan Nijeriya za su samar wa kansu aikin yi idan kun raya ƙasar

Buhari ga Bankin Musulunci: ’Yan Nijeriya za su samar wa kansu aikin yi idan kun raya ƙasar

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya gana da Shugaban Bankin Cigaban Musulunci (IDB), Dakta Mohammed Al-Jasser, a gefen taron Paris kan Zama Lafiya, inda ya bayyana cewa, matuqar bankin ya taimaka wajen raya Nijeriya ta fuskar gudanar da manyan ayyuka, to ’yan ƙasar za su iya samar da kansu ayyukan yi. Don haka ne ya ce, wannan ne dalilin da ya sa gwamnatinsa ta duƙufa wajen farfao da manyan ayyukan cigaba a Najeriya. Bayanin hakan na ƙunshe ne a sanarwar da Mai Taimaka Wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labari, Mista Femi…
Read More
Mahara sun kashe mutane kimanin 10 a Ƙaramar Hukumar Batsari

Mahara sun kashe mutane kimanin 10 a Ƙaramar Hukumar Batsari

Daga BABANGIDA GORA a Katsina Kimanin mahara sama da ɗari ne su kai dirar mikiya a wata unguwa da ke cikin garin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina. Maharan da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne, da su kai ƙaurin suna a yankin na Batsari da ke makwabtaka da jihar Zamfara da ta daɗe tana fama da  masu garkuwa da mutane da satar shanu tsawon lokuta, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Haka zalika maharan sun kai wannan farmaki ne a ranar Talatar da ta gabata da misalin ƙarfe 8:00 na dare, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane…
Read More