15
Nov
Jami'an tsaron Habasha sun kame ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya fiye da 12 dake aiki a ƙasar, kamar yadda jami'an agaji suka tabbatar. Bayanai sun ce an kame jami’an ne a birnin Addis Ababa, yayin wani samame da aka kaiwa 'yan ƙabilar Tigray a ƙarƙashin dokar ta-ɓaci. Ɗaya daga cikin majiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya da suka tsegunta labarin kamen, ta ce an ɗauke wasu daga cikin jami’an da aka kame ne a gidajensu. Tuni dai wata mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva ta sanar da mika buƙatar sakin jami’an nasu ga ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Habasha. A makon…
