16
Nov
Daga BASHIR ISAH Gobe Labara idan Allah Ya kai mu, ake sa ran gudanar da taron ƙaddamar da Ƙungiyar Haɓɓaka Harshen Hausa ta Ƙasa reshen Jihar Neja domin ci gaba da bunƙasa harshen Hausa yadda ya kamata. Taron wanda za a soma shi daga kan ƙarfe 10 na safe, zai gudana ne a Cibiyar Nazarin Harkokin Shari'a da Gudanarwa ta Fati Lami Abubakar (FLAILAS) da ke yankin Kpakungu a garin Minna, babban birnin jihar Neja. Manyan baƙin da ake sa ran su halarci taron sun haɗa da: Mai Martaba Sarkin Minna, Alh. (Dr.) Umaru Farouq Bahago da Farfesa Aliyu Muhammad…
