Editor

9513 Posts
Sharhin littafin ‘Sin is a Puppy’ (Alhaki Kuikuiyo) daga Janine, Baturiyar Jamus

Sharhin littafin ‘Sin is a Puppy’ (Alhaki Kuikuiyo) daga Janine, Baturiyar Jamus

“A matsayina na Bajamushiya faɗan Rabi da Delu a littafin ya sani nishaɗi” Daga JANINE DRAEGER (TALATU) Taƙaitaccen bayanin littafin:Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ita ce marubuciyar littafin ‘Sin is a Puppy’, wanda asali a cikin harshen Hausa aka rubuta, mai suna 'Alhaki Kuikuiyo', kuma aka fassara zuwa harshen Ingilishi. Ramat General Enterprise ne suka wallafa a shekarar 1990. Farfesa Aliyu Kamal ne ya yi fassara zuwa harshen Ingilishi, kuma an wallafa wannan a Blaft Publications, cikin birnin Chennai a Ƙasar Indiya a shekarar 2012. Wannan ne fassarar da aka yi na wannan littafi a karon farko, zuwa harshen Ingilishi. Wannan…
Read More
Basir da yadda ya ke shafar zamantakewar ma’aurata

Basir da yadda ya ke shafar zamantakewar ma’aurata

Daga BILKISU YUSUF ALI TAMBAYA:Anti Bilki, Ina so a yi min bayani ne kan mene ne ciwon basir kuma ya ake yi ya ke shafar zamantakewar ma’aurata? AMSA:Ciwon Basir wani ciwo ne kuma marar daɗi da ya ke addabar al’umma duk da da dama mutane kan yi masa wani kallo na daban wataƙila don yadda ake jingina kowanne ciwo da basur ne don haka ake masa kallon shu’umi ko kuma kowacce cuta daga gare shi take oho? Kalmar basir asalinta Balarabiyar kalma ce inda da Larabci ake kiranta Bawasir ko Basuur da Turanci ana kiransa da ( Hemorrhoid /pile) Ciwo…
Read More
Maniyyata su shirya, akwai aikin Hajji bana, inji NAHCON

Maniyyata su shirya, akwai aikin Hajji bana, inji NAHCON

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinan tsare-tsare, bincike, ƙididdiga da kuma yaɗa labarai na hukumar aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Mamoh, ya bayyana cewa, bana ’yan Nijeriya za su samu damar sauke farali a ƙasa mai tsarki. Prince Mamoh ya bayyyana cewa, babu tantama suna da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata za su gudanar da aikin Hajji. Da yake fira da manema labarai, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata da ke faxin Nijeriya su fara shiri tun yanzu. Haka zalika, Kwamishinan, wanda ke jagorantar ɓangaren tsare-tsare, ya ƙara da cewa, hukumarsu na shirin kawo sauyi domin sauƙaƙa abubuwa…
Read More
Yadda kiran waya ya haifar da gobarar gas a Legas

Yadda kiran waya ya haifar da gobarar gas a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Talata a wani mummunar fashewar gas a kan titin Ojekunle, kusa da titin Ladipo, a unguwar Mushin da ke jihar Legas. Kamar yadda rahotanni suka ruwaito, bam ɗin ya lalata motoci aƙalla 15, tare da lalata gidaje da dama a yankin. Wurin da gobarar ta afku ya haɗa da makanikai, masu facin taya, dillalan iskar gas da sauran ’yan kasuwa. Shaidun gani da ido da suka zanta da kamfanin dillancin labarai, sun ce, lamarin ya faru ne a kusa da wata Mama Emma, mai soyan ƙosai da…
Read More
Bayyana da yaɗuwar harshen Hausa da Hausawa

Bayyana da yaɗuwar harshen Hausa da Hausawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamar yadda mu ka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu riqa kawo wa masu karatu tarihin manyan ƙabilun Nijeriya, a yau za mu bayyana taƙaitaccen tarihin asalin Hausawa da harshen Hausa a Nijeriya. Ƙabilar Hausa dai ƙabilace da ke zaune a Arewa maso Yammacin Tarayyyar Nijeriya da Kudu maso Yammacin Jamhuriyyar Nijar. Ƙabilace mai ɗimbin al’umma, amma kuma a al'adance mai mutuƙar haɗaka, aƙalla akwai sama da mutane miliyan 50 da harshen yake asali gare su. A tarihi an ce, ƙabilar Hausawa na tattare a salsalar manyan birane. Hausawa dai sun sami kafa…
Read More
An shirya gudanar da babban taron KILAF na bana

An shirya gudanar da babban taron KILAF na bana

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Moving Image Limited tare da haɗin gwiwar Tsangayar Nazarin Sadarwa ta Jami'ar Bayero, Kano, sun shirya gudanar da babban taronsu na shekara-shekara na tallata harsunan gida na Kano a kasuwar fina-finai ta Afirka, wato Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival ko kuma KILAF a taƙaice. Taron KILAF na 2021 zai gudana ne a ranakun Litinin 22 da Talata 23 ga watan Nuwamban da ake ciki. Wannan shi ne karo na huɗu da ake shirya taron. Sanarwar manema labarai da ta sami sa hannun mu'assasin KILAF, Abdulkareem Mohammed da shugaban tsangayar nazarin sadarwa na…
Read More
Numfashin mutum (2)

Numfashin mutum (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI 'Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkanmu mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan Adam, domin ku fa’idantu, ku san yadda jikin ku ke aiki. Satin da ya wuce, na fara bayanin yadda jini taimakawa wajen musayar iska tsakanin duniyar da muke ciki, da kuma duniyar jikin ɗan adam. Mun tsaya a inda nake cewa: Huhun mutum na dama da na hagu, sun sanya zuciya a tsakiya. Saboda hikima da fikra ta Sarkin halitta, hakan na da wani sirri da…
Read More
‘Mijina ke ƙarfafa ni kan aikina duk lokacin da gwiwata ta yi sanyi – Halima Hassan Ibrahim

‘Mijina ke ƙarfafa ni kan aikina duk lokacin da gwiwata ta yi sanyi – Halima Hassan Ibrahim

“A dalilin aikin jarida na zama mai tallafa wa marayu” Daga ABUBAKAR M. TAHIR Masu karatu, wannan tattaunawa ce ta musamman da Wakilin Manhaja, Abubakar M. Tahir, ya yi da wata matashiyar 'yar jarida kuma mai fafutukar tallafa wa marasa gata da gajiyayyu, wato Halima Hassan Ibrahim. A cikin tattaunawar da matashiyar ’yar jaridar mai shekaru 33, za ku ji yadda ta fara wannan aikin na tallafawa marayu da gajiyayyu, gwagwamayar rayuwa, nasarori da dai sauran batutuwa: Mu fara da tarihinki a taƙaice.Assalamu alaikum warahamatullah, ni dai Halima Hassan Ibrahim Shi ne sunana, kuma an haifeni a Kano, a Shekarar…
Read More
Dalilin da ya sa Coca-cola ya maka Pop-cola a kotu

Dalilin da ya sa Coca-cola ya maka Pop-cola a kotu

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Coca-cola ya maka takwaransa na Mamuda Beverages Nigeria limited mai sarrafa lemon kwalbar nan na Pop-cola, a Babbar Kotun Kano kan zargin satar alamar kasuwancinsa. Kano Focus ta ruwaito cewa, kamfanin Mamuda Beverages Nigeria limited ya ƙaddamar da lemon kwalba na Pop-cola ne a watan Yunin da ya gabata. Coca-cola na zargin kamfanin Mamuda Beverages da kwaikwayon zane wajen tsara alamarsa ta kasuwanci a jikin kwalba wanda ya ce zanen sak yake da nasa wanda hakan na haifar da ruɗani ga kwastomominsa inda wasunsu kan ɗauki Pop-cola a matsayin Coca-cola. Bayan sauraren lauyoyin duka ɓangarorin biyu,…
Read More