Editor

9513 Posts
Gidan rediyon Vision ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna

Gidan rediyon Vision ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Kamfanin yaɗa labarai na ‘Vision Media Service’, masu gidajen rediyon Vision FM ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna ta hanyar yaɗa jita-jitar ƙarya a kafafen sadarwa na zamani. A cikin wata sanarwa da babban jami’in gudanarwar kamfanin, Malam Shuaibu Mungadi, ya sanya wa hannun kuma ya raba wa manema labarai, ya ce, “abubuwan da ke faruwa a kafafen sadarwa na zamani dangane da kamfaninmu mai daraja, ya sa hukumar kamfanin ta fitar da wannan sanarwa da nufin gyara kura-kuren da wasu tsirarun mutane da wasu abokan aikin kamfanin suka yi.” Sanarwar…
Read More
Yadda aka kashe mutum 64 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Yadda aka kashe mutum 64 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Aƙalla mutum 64 ne aka kashe a cikin kwanaki biyu a jihar Sokoto yayin da ’yan bindiga suka kai farmaki. Adadin waɗanda suka mutu a hare-haren na ranar Lahadi da Litinin a ƙaramar hukumar Goronyo da ke jihar ya ƙaru zuwa 43 daga 15, yayin da wasu 14 suka mutu a ranar Talata a hare-haren da aka kai a ƙauyukan ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar. Harin na baya-bayan nan wanda aka kashe mutane 14 ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tura ƙarin kayan aikin soji…
Read More
Gwamnatin Kano ta biya Ja’afar Ja’afar diyyar ɓata sunansa

Gwamnatin Kano ta biya Ja’afar Ja’afar diyyar ɓata sunansa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta baiwa shahararren Dan jaridar nan Ja'afar Ja'afar Naira 800,000 saboda ɓata masa suna da ta yi, Jiya Juma'a ne dai Ja'afar Ja'afar ya sanarwa Freedom Radio Kano cewa, an biya shi kudin, kamar yadda kotu ta bada umarni da a biya shi Naira dubu 800, Tun a watan Yulin wannan shekarar ne dai babbar kotun Kano mai lambar 9 da ke zaman ta a Bampai ƙarƙashin mai Shari'a Baba na Malam ta umarci gwamnatin Kano ta biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa ƙudin, saboda ɓata masu…
Read More
Zaɓen Anambara: Ba lallai a rantsar da Soludo a matsayin gwamna ba

Zaɓen Anambara: Ba lallai a rantsar da Soludo a matsayin gwamna ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bincike a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Nijeriya, inda aka gudanar da zaɓe kwanan nan, kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya zama wanda ya lashe zaɓen, ya bankaɗo wani babban batu, wanda fitaccen masanin tattalin arziki kuma ma'aikacin banki ya aikata. Wani bincike ya nuna cewa, ɗan takarar jam'iyyar PDP, Valentine Ozigbo wanda ya zo na biyu a zaɓen gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga Nuwamba, 2021, ana iya rantsar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Anambra na gaba. Ta kuma bayyana cewa, Farfesa Charles Soludo, na…
Read More
Tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi zanga-zanga kan rashin cin nama

Tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi zanga-zanga kan rashin cin nama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗaruruwan 'yan Boko Haram da ke a sansanin da aka killace su bayan da suka miƙa wuya ga sojojin Nijeriya sun tayar da tarzoma a ranar Laraba da nufin gwamnatin ta dinga yanka musu shanun da ake kawo musu. Tarzoma ta tayar da hankalun mazauna garin Maiduguri da ke kusa da sansanin tubabbun mayaƙan na Boko Haram, inda mazauna garin suka ɗauko adduna, takobi da kuma gariyo suna barazarar kashe duk ɗan Boko Haram ɗin da ya yi yunƙurin barin sansanin, a cewar majiyar da ta shaida wa kafar AFP. Lamarin ya nuna yadda…
Read More
Tattalin arziki da tsaro: Nijeriya ta samu tagomashi da koma-baya

Tattalin arziki da tsaro: Nijeriya ta samu tagomashi da koma-baya

*Hauhawar farashi zai jefa ’yan Nijeriya miliyan shida cikin talauci – Bankin duniya *Fyaɗe 11,200 aka yi a Nijeriya daga bara zuwa bana – Amnesty International *Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.03 a 2021 – NBS *Yanzu babu tursasawar addini a Nijeriya – Amurka Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Daga dukkan alamu al’amuran Nijeriya su na yin kwangaba-kwanbaya ko kuma a ce tafiyar kura, inda yayin da a wani fannin ta samu cigaba, a wani fannin kuma ci-baya ta samu. Ga yadda Manhaja ta haɗo muku rahotanni kan halin da ƙasar ke ciki, musamman ma a wannan…
Read More
Yadda kyakkyawar zamantakewa ke kawo zaman lafiya

Yadda kyakkyawar zamantakewa ke kawo zaman lafiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu'amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama'a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra'ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama'a, daga ɓangarori daban-daban. Babu shakka zaman lafiya da jama'a, tausayawa, tallafawa, da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama'a ke…
Read More
Wa ke da laifin lalacewar yaranmu mata?

Wa ke da laifin lalacewar yaranmu mata?

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Assalamu Alaikum, kamar kullum, ga mu yau ma a cikin filin mu na tarbiyya. Za mu ɗauko batu mai matuƙar mahimmanci da amfani da ya kamata kowaɗanne iyaye su sa ido su kuma cire soyayya su ajiye gaskiya a kan yara. Ƙila wasu iyayen sun san me yaransu suke aikatawa a bayan idanunsu, ƙila kuma ba su sani ba. Ban gaskanta hakan na faruwa ba sai da na ji daga bakin yara matasa mata da maza kusan mutum shida sai abun ke ɗaure min kai, da gaske ne ko da wasa? Na ɗan bincika na tarar…
Read More
Ko Gaddafi zai dawo Libya?

Ko Gaddafi zai dawo Libya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wani faifan bidiyo da editan jaridar Manhaja, Nasir S. Gwangwazo, ya saka a shafinsa na yanar gizo ya ja hankalina kan mulki da yadda ya ke da kuma yadda zai iya kasancewa idan ba a kai ba ko idan ya kuvuce. A cikin bidiyon, Kakakin tsohon Shugaban Nijeriya Jonathan, wato Reuben Abati, ke bayani kan kwanakin ƙarshe na mulkin maigidansa a 2015, inda ya zama mutane da a baya ke tururuwa zuwa fadar Aso Rock su ka yanke cak kamar an ɗauke ruwan sama. Kafin lokacin Abati ya ce, mutane ke jerin gwanon neman ganin Jonathan…
Read More
Yawaitar asarar rayuka sakamakon ruftawar gini

Yawaitar asarar rayuka sakamakon ruftawar gini

A wani rahoto daga wani bincike da aka buga a makon da ya gabata an nuna cewa, aƙalla mutane 305 ne suka mutu yayin da mutane 449 suka samu munanan raunuka ta hanyar ruftawar benaye 83 a Nijeriya tun daga shekarar 2013, wanda ya kasance ba wai kawai abin damuwa ba ne amma kuma abin takaici ne. Binciken da wata jarida ta ƙasa ta gudanar ya bayyana cewa, alƙaluman sun nuna ƙarara ga kafafen yaɗa labarai, domin da yawa ba a taɓa jin labarinsu ba. Ya ce, har yanzu Legas ce cibiyar rugujewar gine-gine a Nijeriya inda aka samu rahoton…
Read More