Editor

9513 Posts
Marigayi Yusuf Maitama Sule bai saci Kwabon al’umma ba – Jega

Marigayi Yusuf Maitama Sule bai saci Kwabon al’umma ba – Jega

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfasa Attahiru Jega, ya shaida cewa, Marigayi Ɗanmasanin Kano, AlhajiYusuf Maitama Sule bai yi almubazaranci ko satar kuɗaɗen jama’a ba a lokacin rayuwar sa da ya riƙe muƙaman gwamnati daba-daban, tun yana ƙuruciyar sa. Fitaccen malamin jami’a Jega, ya yi wannan furuci ne yayin gudanar da wata lakca kan shugabanci domin girmama Marigayi Ɗanmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule wadda gamayyar ɗaliban arewacin ƙasar nan ta shirya, wanda aka gudanar a cibiyar Umaru Musa Yar’adua da ke Jami’ar Katsina a ranar Litinin da ta…
Read More
Kunama ta buwayi mutane bayan tafka ruwan sama a Masar

Kunama ta buwayi mutane bayan tafka ruwan sama a Masar

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliya ya sauka a Aswan na ƙasar Masar, inda ya koro wasu irin nau’ukan kunamai masu haɗari zuwa neman mafaka a gidajen mutane. Mutane 3 ne AlJazeera ta ruwaito suka mutu inda sama da 400 ke kwance a asibiti a faɗin jihar domin karɓar maganin dafin kunama, a cewar kafafen yaɗa labarai na gwamnati. Sai dai kuma muƙaddashin ministan lafiya na ƙasar, Khalid Abdel-Ghafar, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, ba a samu rahoton mace-mace ko ɗaya ba. Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta tabbatar wa da jama’a cewa, tana…
Read More
An gano wanda ya sace Naira Miliyan 88.1 bayan shekaru 52

An gano wanda ya sace Naira Miliyan 88.1 bayan shekaru 52

Theodore John Conrad, wani mutum mai shekaru 20 a watan Yulin 1969, a lokacin ya fara aiki a wani banki da ke Amurka. Bayan fara aikin ne ya sace Dala 215,000, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 88,182,250 a kuɗin Nijeriya, daga nan babu wanda ya sake ganin sa. CNN ta ruwaito yadda darajar kuɗin da ya sata a yanzu ta kai $1.7m (N697,255,000) wanda shi ne mafi girman sata da aka taɓa yi wa banki a tarihin duniya. Ya koma wani garin fiye da shekaru 50 da suka shuɗe daga baya ’yan sanda su ka bayyana cewa ranar…
Read More
Ban ɗau fiye da mintuna uku ba kacal, inji mai fyaɗe

Ban ɗau fiye da mintuna uku ba kacal, inji mai fyaɗe

Wani mai fyaɗe, Sangokunle Akintola, wanda ya raka abokinsa Ismaila Raimi, domin koya wa wata budurwa darasin da ba za ta taɓa mantawa ba, ya shaida wa ’yan sandan jihar Osun cewa, bai wuce mintuna uku ba a lokacin da ya ke yi wa budurwar fyaɗe. Ismaila ya kasance yana abota da yarinyar tsawon wata shida, yana ba ta kuɗi masu yawa kuma yana fatan ya aure ta a gaba. Sai dai da yarinyar ta ce masa bai dace da damfara ba ‘Yahoo’, sai ya sha tabar wiwi, ya ɗauki sanda ya yi amfani da shi a matsayin bindiga ya…
Read More
Fim ɗin Gari Guda zai buɗe sabon shafin kallo a sinima – Darakta Sufyanu Kabo

Fim ɗin Gari Guda zai buɗe sabon shafin kallo a sinima – Darakta Sufyanu Kabo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A yanzu dai duk wani shiri ya kammala na fitowar sabon fim ɗin 'Gari Guda', wanda Kamfanin 'Islamic Film Empire' suka shirya, kuma Sufyanu Lawal Kabo ya bayar da Umarni.Ganin yadda fim ɗin ya bambanta da sauran fina-finan da aka saba shirya wa a masana'antar fina-finai ta kannywwod ne ya sa muka nemi jin ta bakin Daraktan fim ɗin Sufyanu Lawal Kabo don jin irin abubuwan da fim ɗin ya ƙunsa. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance: Akwai wani sabon fim da ka yi aikin sa, kuma ka ke…
Read More
Shekaru 21: Birnin Gwari ba kwanciyar hankali

Shekaru 21: Birnin Gwari ba kwanciyar hankali

Idan na ce Birnin Gwari ina nufin ƙasar Birnin Gwari, saƙo da lungunta, ba wai cikin ƙwaryar garin ba cibiyar mulki da hada-hadar kasuwanci. Ƙasar Birnin Gwari mai faɗin murabba'i sama da Dubu Shida, ƙasa ce ta manoma. Zaman lafiya da kwanciyar hankali da son jama'a musamman baƙi, su ne halayen nagarta da aka san ƙasar Birnin Gwari tun kafin Jihadin Mujaddadi Shehu Ɗan Fodiyo. Tarihi ya tabbatar da cewa, akwai Musulunci a ƙasar Birnin Gwari mai inganci kuma mai ƙarfi tun kafin Mujaddadi Shehu Ɗan Fodiyo ya tsaida jihadi a kan ƙasar Hausa. Wannan ne ma yasa Shehu Ɗan…
Read More
Da kuɗi na maganin mutuwa da mun kashe ko nawa ne don kuɓutar da Sani Ɗangote – Tinubu

Da kuɗi na maganin mutuwa da mun kashe ko nawa ne don kuɓutar da Sani Ɗangote – Tinubu

Daga BASHIR ISAH Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana rasuwar Marigayi Sani Dangote a matsayin al'amari da Allah Ya nuna ikonSa, yana mai cewa, da kuɗi na maganin mutuwa da sun haɗa ko nawa ne don kuɓutar da Sani daga hannun mutuwa. Tinubu ya bayyana haka ne sa'ilin da ya ziyarci Alhaji Aminu Alhassan Dantata a Juma'ar da ta gabata dangane da rasuwar Sani Ɗangote. Tinubu wanda ya kai ziyarar a bisa rakiyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce da kuɗi na sayen rai da ko nawa ne za su kashe don tsawaita ran Marigayi Sani.…
Read More
Gwamnan Adamawa ya fifita cigaban ilimi a jiharsa – Sakataren Ƙungiyar Malamai

Gwamnan Adamawa ya fifita cigaban ilimi a jiharsa – Sakataren Ƙungiyar Malamai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD Duk da matsaloli da barazanar tsaron da ake fuskanta a arewacin Nijeriya, ba a taɓa daina zuwa makarantu a Jihar Adamawa ba, saboda yadda gwamnan jihar, Ahmad Fintiri, ya fifita harkokin ilimi a jihar. Sakataren ƙungiyar malamai ta ƙasa reshen jihar ta Adamawa, Kwamared  Wakili Kyari ne ya bayyana haka a Kano a yayin taron shekara-shekara na ƙasa da ƙungiyar shugabannin makarantun firamare suka gudanar. Ya ce Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Fintiri yana bada kulawa sosai ga ci gaban ilimi fiye da gwamnoni da suka gabata, duk da matsalolin da ba za a rasa ba. Domin kafin zuwansa malamai…
Read More
Yari da Marafa ’yan bindigar siyasa ne a Zamfara, cewar Sani Shinkafi

Yari da Marafa ’yan bindigar siyasa ne a Zamfara, cewar Sani Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan takarar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya caccaki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa kan gudummawar da suka bayar na taɓarɓarewar jam’iyyar APC a jihar Zamfara, yana mai bayyana su a matsayin ‘yan bangar siyasa. Shinkafi ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Gusau ranar Lahadi, a lokacin da yake mayar da martani ga ɓangaren Yari da Sanata Kabiru Marafa kan taron mazaɓun jam’iyyar APC da aka kammala a mazavu 147 na jihar. A cewar sa, ƙaurace wa taron da ɓangaren Yari…
Read More
An nemi manoma su daina sarrafa amfanin da ke sanya cuta

An nemi manoma su daina sarrafa amfanin da ke sanya cuta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An buƙaci manoma da su kiyaye da yadda za a sarrafa kayan amfanin gona bayan sun yi girbi domin kawo ƙarshen yadda a wani lokaci abincin ya kan zama sanadiyyar jawo cututtaka ga al’umma, matuƙar ba su yi amfani da shawarwarin masana harkar noma ba. Farfesa Sani Miko, Shugaban Hukumar Sasakawa ta Nijeriya ne ya yi wannan kiran a yayin da ma’aikatar sa ta Sasakawa ta shirya wata bita mai taken 'hada-hada kan kayan noma bayan girbi da kuma yadda za a ajiye shi.' Ma’aikatar ta shirya bitar ne ga manoman jihar Kano da…
Read More