13
Oct
“Mafi yawan mata masu yoyon fitsari Fulani ne” - Ramatu Daga UMAR AKILU MAJERI, a Dutse Hajiya Ramatu Muhammed tsohuwar malamar makaranta ce. Ta kasance bafilatana mai kishin yarenta, tare da son taimakon marasa galihu. Hajiya Ramatu na ɗaya daga cikin malamai da ake alfahari dasu a cikin makarantun ‘ya’ya Mata da suke taimaka wa wajan baiwa ɗalibai tarbiyar da ake alfahari dasu a Jahar Jigawa. Yanzu haka malama Ramatu itace babbar sakatariya mai cikakken iko a Hukumar Raya ilimin ‘yayan Fulani makiyaya a ma'aikatar ilimi ta Jahar Jigawa ,kafin takai ga wannan matsayin, ta tava riƙe muƙamin daraktan makarantun…
