Editor

9513 Posts
Sai Yaushe miji da mata za su gane zaman aure taimakemeniya ne?

Sai Yaushe miji da mata za su gane zaman aure taimakemeniya ne?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkan mu da saduwa a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan mako muna tafe ne da bayani a kan yadda ma'aurata suka gaza fahimtar zaman aure, zaman taimakekeniya ne wato cuɗe ni, in cuɗe ka. Wato aikin gayya ko 'team work' da ingilisi kenan. A makon da ya gabata, mun bayyana yadda mata suke nuna damuwa da ƙorafi idan maza sun tafi sun bar su da wahalhalun gida. Wannan na nuna rashin uzuri ne domin ko dai sun tafi nema ko akwai dalili. Duk da dai akwai masu yawon mara amfani.…
Read More
Aikin albashin Naira 270,000 na ajiye na koma gyaran takalmi a zamance – Abubakar Sadik Umar

Aikin albashin Naira 270,000 na ajiye na koma gyaran takalmi a zamance – Abubakar Sadik Umar

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Malam Abubakar Sadik Umar wani haziƙin mtashi ne ɗan baiwa da ya ke gyaran takalmi a zamanance a cikin ƙwaryar Birnin Kano. A hirarsa da Wakilin Manhaja, Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji irin yadda tsohon ɗan takarar Gwamna na Jihar Kano ya bayyana irin yadda ya ke gyara wa manyan mutane a Nijeriya takalmansu da kuma yadda ya ke biyan ma'aikatansa albashin Naira 350,000 a wata. Ku biyo mu. Za mu so ka gabatar mana da kanka?Sunana Abubakar Sadik Umar. An haife ni a shekarar 1973, a ƙaramar hukumar Gwaram, ta jihar Jigawa. Na yi…
Read More
Ranar Malamai Ta Duniya: Malamai na cikin wani hali a Kebbi

Ranar Malamai Ta Duniya: Malamai na cikin wani hali a Kebbi

Daga Jamil Gulma a Kebbi Ranar ranar 5 ga Oktoba na kowacce shekara aka tsayar a matsayin Ranar Malamai ta Duniya, inda a wurare daban-daban na faɗin duniya ake gudanar da bukukuwa da taruka da kuma lakcoci dangane da abin da ya shafi aikin koyarwa, inda a waɗansu wuraren har ma akan karrama waɗansu haziƙan malamai da suka cancanta. Nijeriya ma ba a bar ta a baya ba wajen murnar zagayowar wannan ranar, sai dai ba wani abu na a-zo-a-gani da ake ganin an aiwatar bayan ranar ba a karatu illa malamai da ɗalibai suna zaune a gida. Wakilin Manhaja…
Read More
Yadda batun kama ɗan Shah Rukh Khan bisa zargin tu’ammalli da ƙwayoyi ya zama

Yadda batun kama ɗan Shah Rukh Khan bisa zargin tu’ammalli da ƙwayoyi ya zama

Daga AISHA ASAS A ranar 3 ga watan Oktobar wanann shekara ofishin kula da miyagun ƙwayoyi ta Ƙasar Indiya, wato NCB, ta damƙe ɗan shahararren ɗan wasan kwaikwayon Indiya Shah Rukh Khan da laifin tu’amalli da miyagun ƙwayoyi. Ofishin ya damqe shi ne a bakin taikon Mumbai, inda su ke gudanar da sharholiyarsu a cikin wani jirgin ruwa. Rahoton ya bayyana cewa, Ɗan na Shah Rukh ba shi kaɗai ne hukumar ta samu damar damqa ba, domin dai bikin na jin daɗi ne suke gabatarwa wanda ya ɗauki dubban matasa ‘yan'uwansa. Duk da cewa an tabbatar da cewa gayyatar Aryan…
Read More
Ko ka san sakin aure guda biyar mafi tsada a duniya?

Ko ka san sakin aure guda biyar mafi tsada a duniya?

Labarin rabuwar Bill Gates da Melinda ya mamaye kafofin watsa labarai a ranar 3 ga Mayu. Wannan ya ba mutane da yawa mamaki, musamman ma bayan auren shekaru 27. A yayin sanar da rabuwar tasu a shafin Manhajar Twitter, inda ma’auratan sun ce za su ci gaba da aikin haɗin gwiwar da su ke yi a gidauniyar Bill da Melinda Gates, wacce ke ɗaukar nauyin shirye-shiryen kiwon lafiya a duniya, daidaiton jinsi, ilimi, da sauran abubuwan. Wannan ba shine farkon babban saki da za a sanar ba, domin a qasa ga wasu saki 5 mafi tsada a duniya: Angelina Jolie…
Read More
Ɗan majalisa da gwamnatin Bauchi sun buɗe wa juna wuta kan ruguza gidansa

Ɗan majalisa da gwamnatin Bauchi sun buɗe wa juna wuta kan ruguza gidansa

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazavar ƙaramar Hukumar Bauchi, Hon. Yakubu Shehu Abdullahi, ya bayyana cewar, fashi ne ƙuru-ƙuru da jami’an gwamnatin jihar suka yi na ruguza masa gida mai lamba 7 da ke titin Buba Yero cikin rukunin gidajen gwamnati da ke Bauchi. A cewar ɗan majalisar, yana da takardar mallaka ta gidan (Certificate of Occupancy) mai lamba BA/39705 da gwamnatin jiha ta amince a ba shi, haɗi da biyan dukkanin kuɗaɗen da ya wajaba ya biya. Hon. Abdullahi a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar ranar Talata da ta…
Read More
Shauƙin zama likita gado ne na gidanmu, Inji Saraki

Shauƙin zama likita gado ne na gidanmu, Inji Saraki

Daga NASIR S. GWANGWAZO Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya bayyana dalilin da ya sa ya zama likita.  Saraki ya yi wannan bayani ne yau a wurin taron ƙasa na Kungiyar Ɗalibai Likitoci ta Nijeriya wanda aka gudanar a Jami'ar Baze dake Abuja. Dr. Abubakar Bukola Saraki shi ne Uban Taron na, wanda bayan buɗe taro da ya yi Kungiyar ta girmama shi da lambar yabo. A cikin jawabinsa ya ce: "A al'adar gidanmu, mun mayar da zama likita wata kafa ta taimakawa masu buƙatar taimako. Ina ɗan shekara 12 na…
Read More
2022: Buhari ya gabatar da kasafi mafi tsada a tarihi

2022: Buhari ya gabatar da kasafi mafi tsada a tarihi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja A jiya Alhamis ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jimillar kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 16.39 na shekarar 2022 ga babban zauren Majalisar Tarayya, wanda shine kasafi mafi tsada da aka gabatarwa a tarihin Nijeriya. A jawabinsa na gabatar da daftarin kasafin na Naira tiriliyan 16.39, Buhari ya shaida wa zauren majalisar cewa kasafin 2021 ya samu matsala, saboda Nijeriya ta samu durƙushewar tattalin arziki sau biyu, amma ta yi nasarar fitowa daga matsalar. Ya ƙara da cewa, a 2021 an samu kuɗaɗen shiga daga vangaren da ba na mai, kuma sun…
Read More
Sarkin Sasa ne ya naɗa ni Ƙauran jihohin Kudu – Aminu Kuceri

Sarkin Sasa ne ya naɗa ni Ƙauran jihohin Kudu – Aminu Kuceri

Daga DAUDA USMAN a Legas  Ƙauran jihohin kudu da yammacin Nijeriya, Alhaji Aminu Bature Kuceri, ya bayyana cewar Sarkin Sasa a Ibadan, Alhaji Malam Haruna mai Yasin Katsina ne ya naɗa shi a matsayin sarautar Ƙauran jihohin kudu da yammacin Nijeriya a Legas. Alhaji Aminu Kuceri ya faɗi hakan ne a gidansa na kallon wasan damben gargajiya da ke unguwar  Alabar Rago a lokacin da ƙungiyar ta su ta gudanar da wani ɗan ƙwarya-kwaryar taro kuma yake bayyana kaɗan daga cikin tarihin rayuwarsa. Kuceri ya cigaba da cewar baya ga wannan sarautar ma da Sarkin Sasa Ibadan ya ba shi…
Read More
An cafke matashin da ke lalata da ƙaramin yaro a Jigawa

An cafke matashin da ke lalata da ƙaramin yaro a Jigawa

Daga UMAR  AKILU MAJERI a Dutse Dubun wani matashi mai  kimanin shekaru talatin a duniya ta cika adaidai lokacin da malaman makaranta suka gano ɗaya daga cikin ɗaliban su yana wadaƙa da kuɗi, inda bincike ya yi zurfi aka samu labarin wannan matashi mai suna Abdullahi, mazaunin unguwar Maranjuwa da ke lalata da shi a gidansa idan matarsa ba ta nan. Lamarin da ya sa hukumar makarantar ta samar da iyayen yaron halin da ɗansu yake ciki, kuma suka sanar da jami'an Civil Defense aka cafke wanda ake tuhumar, yayin da bai musa ba ya tabbatar da abinda ake tuhumarsa…
Read More