10
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da naɗin sabon Sarkin Sudan na Kontagora, kwanaki bayan rasuwar sarkin masarautar na shida, Alhaji Sa'idu Namaska. Kwamishinan qananan hukumomi da ci gaban al'ummomi da masarautun gargajiya, Emmanuel Umar ne ya sanar da naɗin Mohammed Barau a matsayin sabon Sarkin Kontagoran, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da daddare. Ya ce, an zaɓi sabon Sarkin Sudan na Kontagoran ne a ranar Lahadi 19 ga watan Satumban 2021, kuma manyan masu zavar sarki na masarautar ne suka yi hakan. Kwamishinan ya ce "Masu zavar sarkin sun tabbatar wa…
