Editor

9513 Posts
Noma: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin tashin farashin abinci a Najeriya

Noma: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin tashin farashin abinci a Najeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa a kullum ake samun hauhawar farashin abinci a ƙasar Najeriya duk da yadda jama'a suka tsunduma ka'in da na'in wajen noma kayan abinci a ƙasar. Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin jawabin da Shugaban ya gabatar a ranar murnar zagayowar samun 'yancin Najeriya Karo na 61 wanda ya gudanar ranar 1 ga watan Oktoba l, 2021 wato Juma'ar da ta gabata, a Abuja. Inda shugaban ya bayyana cewa, ba wasu ne suke jawo wannan tsadar rayuwar ba illa dillalai. Domin a cewar sa, su ne…
Read More
Rashin tsayayyen farashin Dala na dagula harkar kasuwanci – Yusuf Maiwake

Rashin tsayayyen farashin Dala na dagula harkar kasuwanci – Yusuf Maiwake

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana ta'azzarar  farashin Dala da cewa yana dagula harkar kasuwancin 'yan kasuwar hatsi na Dawanau da ya sa suka ma rasa yaya za su yi. Alhaji Yusuf Barau Maiwake jigo a kayan amfanin gona na Dawanau shi ya bayyana haka. Ya ƙara da cewa, Dala ta zama abinda za ka ji yanzu an ɗaga farashinta, an jima  za ka ji farashin ya sake hawa, tun da su kayansu waje ake fitarwa kuma da Dalar ake amfani. Idan farashin bai tsaya ba, kowane ɗan kasuwa yana cikin ruɗani. Ya ce da a lokaci irin wannan,…
Read More

Ayyururui! An buɗe waya a Gusau

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Sai albishir da sambarka mutane ke yi wa juna biyo bayan buɗe na'urar sadarwar salula a Gusau, jihar Zamfara. Wannan na nuna aƙalla dai mazauna fadar gwamnatin jihar za su iya buga waya da hawa dandalin sadarwa. Sauran yankunan jihar dulum su ke ta wannan fuska don matakin gwamnati na datse sadarwa da zummar murƙushe ɓarayin daji. Irin wannan lamari ya na da riba kuma ya na da akasin haka. Don alamu na nuna yayin da a ke da ɓarayin daji akwai ɓarayin birni. Wannan ba zai zama abun mamaki ba don an nuna wani jami'in…
Read More
Jan kunnen da Sanusi ya yi kan tattalin arzikin Nijeriya

Jan kunnen da Sanusi ya yi kan tattalin arzikin Nijeriya

Hasashen da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Khalifa Muhammad Sanusi ya yi, cewa tattalin arzikin Nijeriya zai durƙushe nan ba da jimawa ba, kira ne ga manajojin tattalin arzikin ƙasa da masu tsara manufofi da su hanzarta cikin dabara don kaucewa faruwar hakan. Sanusi, ya kuma bayyana cewa, dogaro da ɗanyen man da aka ɗora kan tattalin arzikin ba shi da makoma kuma ba a nemansa a duniya baki ɗaya. Da yake jawabi a taron ƙoli na shida na masu saka hannun jari na Kaduna, bayan ƙaddamar da shirin ci gaban jihar daga 2021 zuwa 2023, don mayar da…
Read More
Kotu ta ɗaure ɗan Abdulrashid Maina, Fisal shekaru 14 a kurkuku

Kotu ta ɗaure ɗan Abdulrashid Maina, Fisal shekaru 14 a kurkuku

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ƙarƙashin Alƙali Abang Okon, ta yanke wa ɗan gidan Abdulrashid Maina, wato Faisal hukuncin ɗauri na shekara 14 a gidan yari. Tare kuma da umurtarsa da ya maido da kuɗi Naira miliyan 58 da dubu 100 ga Gwamnatin Tarayya. A wannan Alhamis ɗin Kotun ta yanke wannan hukuncin, inda ta tuhumi Faisal Maina da laifuka uku da suka haɗa da almundahana da safarar kuɗi ba bisa ƙa'ida ba, kuma an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar ne a kan ko wane laifi. Lauyan gwamnati da ke wakiltar hukumar EFCC da ta shigar da…
Read More
Rashin sha’awar iyali da dalilansu (3)

Rashin sha’awar iyali da dalilansu (3)

Daga BILKISU YUSUF ALI Cigaba daga makon jiya A sati biyun da suka gabata duk muna yin bayani ne kan abin da ke hana sha’awa ko ya katse ta bayan a baya ana zaune lafiya babu wannan damuwar, kuma ana ƙaunar juna da son kasancewa tare. Mun kawo abin da ke haifar da wannan matsaloli waɗanda muka haɗe su a ƙarƙashin matsaloli da zamantakewa ke haifarwa na yau da kullum. Sai dai kuma tun a farko mun ce matsalolin sun kasu ne gida biyu; wato matsalolin da yanayin rayuwa da zamantakewa ya haifar, sai kuma kashi na biyu wanda larura…
Read More
Zaratan marubuta biyar na duniya

Zaratan marubuta biyar na duniya

Daga AISHA ASAS Rubutu daɗaɗɗen abu ne da ya kwashe shekaru masu yawa ya na gudana, wanda hakan ya sanya ake samun saɓani a wurin ƙididdige shekarun sa, domin a duk lokacin da akayi matsaya ga shekarar da aka fara rubutu sai a samu wata hujja da ta tabbatar da rubutu kafin lokacin, don haka shekarun rubutu a duniya sun kasu da dama. Rubutu na ɗaya daga cikin ayyukan da ba su cika mutuwa ba, musamman idan an inganta shi. Marubuci na cikin hallitun da Allah ya bawa baiwar hasashen gaba, kamar wasu rubuce-rubuce, da waqe da aka rubutu shekaru…
Read More
Mijina ne ya dasa min sha’awar yin takara – Halima Amadu Jabiru

Mijina ne ya dasa min sha’awar yin takara – Halima Amadu Jabiru

“Ba zai yiwu a samu cigaba ba tare da gudunmawar mata ba” - Halima Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Hon. Halima Amadu Jabiru gogaggiyar ’yar siyasa ce da ta daɗe ta kuma ƙware a harkar siyasar Jihar Nasarawa da ƙasa bakiɗaya. Ta fito takarar kujerun siyasa da dama a jihar. Ta na daga cikin yan siyasa da su ka fara kafa jamiyyar PDP a jihar kafin daga baya ta canja sheka zuwa APC. A yanzu ita ce Kwamishiniyar Ma’aikatar mata da bunƙasa walwalar jama’a a Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu a ofishinta da ke ma’aikatar a Lafiya, ta…
Read More
Me ya sa mazan suke gudun zaman gidajensu?

Me ya sa mazan suke gudun zaman gidajensu?

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Sannunmu kuma da sake haɗuwa a wani makon mai albarka. A wannan mako, muna tafe da bayani a kan rashin zama a gida da wasu maza suke yi. Sanan kuma da irin ƙorafe-ƙorafe da kuma matsalolin da matan waɗancan marasa zama a gidan suke fuskanta. Kamar yadda mu ke iya gani a cikin zamantakewarmu, za mu ga akwai mazajen da ayyukansu da ma harkoki sukan ɗauke su daga gidajensu na yinin kowacce rana, wasu kuma ma aikin yakan ɗauke su daga garin kacokam ya…
Read More