Editor

9513 Posts
HOTUNA: Yadda taron maulidin Sheikh Ahmad Tijjani karo na 6 ya gudana a Lafiya

HOTUNA: Yadda taron maulidin Sheikh Ahmad Tijjani karo na 6 ya gudana a Lafiya

Daga ISAH BASHIR A ranar Lahadin da ta gabata dubban mabiya Ɗariƙar Tijjaniya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, suka gudanar da babban taron maulidi da suka saba shiryawa duk shekara karo na shida a garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa. Taron wanda aka gudanar a dandalin Lafia Squre, ya samu mahalarta daga ciki da wajen Nijeriya. Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, da Sarkin Lafiya, Mai Martaba Jastis Sidi Bage, da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da sauransu, na daga cikin waɗanda suka halarci taron. Yayin da Gwamna Sule ke gaisawa da Sheikh Ɗahiru Bauchi a wajen taron Yayin…
Read More
WASIƘU: Batun aikin wutar lantarki a Mambila

WASIƘU: Batun aikin wutar lantarki a Mambila

Assslam alaikum! Kirana ga Gwamnatin Tarayya shi ne su ƙara himma, domin wani bincike da BBC Hausa ta gudanar ya bankaɗo cewa ba a yi komai ba a wurin da aka ware domin aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ke jihar Taraba a Arewa-maso-gabashin Nijeriya ba shekara arba'in da fara maganar aikin. Tun a shekarar 1982 ne lokacin mulkin tsohon shugaban Nijeriya, Shehu Shagari aka fara maganar tashar wutar wacce a lokacin aka tsara za ta samar da wuta megawat 2,600. Gwamnatoci da suka shuɗe sun sake fasalta aikin wutar inda a shekarar 2012 ƙarƙashin shugaba Goodluck…
Read More
Ƙungiyar matasan Afirka ta faɗakar da matasa illolin tayar da hankali

Ƙungiyar matasan Afirka ta faɗakar da matasa illolin tayar da hankali

Daga UMAR AƘILU MAJERI, a Dutse Ƙungiyar majalisar matasan Afirka reshen jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Malam Muhammad Ado Yusif, ta gudanar da taronta a Jihar Jigawa da nufin faɗakar da matasa muhimmancin zaman lafiya a Nijeriya. Muhammed Ado ya ce, maƙasudin taron shi ne a faɗakar da matasa illolin tada hankalin al’umma da kuma illar shaye-shaye da matsalolin da rayuwar matasa take a halin yanzu a faɗin Nijeriya. Ado ya buƙaci matasa su zage dantse wajen neman ilimi, kana su tashi tsaye wajen koyon sana’a domin matasa su ne ƙashin bayan kowacce al’umma. Shi ma hakimin Chamo, Alhaji Salihi Suleiman…
Read More
Ba mu gamsu da rawar kafafen yaɗa labarai ba – Tsohon minista Shamsudden

Ba mu gamsu da rawar kafafen yaɗa labarai ba – Tsohon minista Shamsudden

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Ƙungiyar ƙwararru ta Kano da Jigawa, wato Kano Jigawa Professional Forum (KJPF), ta gudanar da taron tattauna musayar Ilimi da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, da ya gudana a ɗakin taro na Makarantar Nazarin Harkokin Kasuwanci ta Dangote da ke Jami'ar Bayero a Kano ranar Asabar da ta gabata. Taron ƙungiyar da Kuliya A. Zubair ke a matsayin Daraktanta, taken taron dai shi ne "Zuba Jari da Bunƙasa Kafafen Yaɗa Labarai", ya samu halartar mamallaka kafafen yaɗa labarai da dama da ke cikin jahohi. Tun da farko a jawabinsa, tsohon ministan tsare-tsare,…
Read More
SHAROBA ta tallafa wa marayu a ɓangaren karatu

SHAROBA ta tallafa wa marayu a ɓangaren karatu

Daga MUHAMMADU MUJITABA, a Kano Ƙungiyar tsofffin ɗalibai ta Sharaɗa ‘Old Boys Association’ (SHAROBA) Aji na 1991 ƙarƙashin shugabancin Malam Rabiu Hamisu Danjidda ta bada tallafin kayan karatu ga makarantar da suka kammala shekaru 30 da suka wuce. Wannan jawabin ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin ɗaliban, Auwalu S Mu’azu, ya bayyana a lokacin taron da ƙungiyar ta gabatar a ɗakin taro na ɗakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano a ranar Asabar da ta gabata. Har ila yau, ya qara da cewa, baya ga tallafi ga makarantar haka kuma ƙungiyar tsoffin ɗaliban ta SHAROBA ta ga…
Read More
Taƙaddamar fili: yadda ta kaya tsakanin EFCC da maiɗakin Ganduje

Taƙaddamar fili: yadda ta kaya tsakanin EFCC da maiɗakin Ganduje

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar nan mai yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annnati ta gayyaci Hafsa Abdullahi Ganduje, maiɗakin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje domin amsa tambayoyi. Majiyarmu wacce take da alaƙa da gwamnatin Kano, ta rawaito cewa, hukumar EFCC ɗin ta gayyaci maiɗakin gwamnan ne a kan zargin cin hanci da rashawa da suke da alaƙa da wata badaƙalar filaye wadda ɗanta, Abdul-Azeez Ganduje ya shigar a kanta. Majiyarmu ta ƙara da cewa, EFCC sun sallami Hafsa Ganduje bayan sun shafe awanni suna yi mata tambayoyi. Wato tun safiyar Litinin tana…
Read More
An zargi Gwamnan Ribas da nuna wariya ga cigaban kasuwancin ‘yan Arewa

An zargi Gwamnan Ribas da nuna wariya ga cigaban kasuwancin ‘yan Arewa

Daga HABU ƊAN SARKI Ƙungiyar haɗin kan marubuta a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya, ta Arewa Media Writers ta bayyana damuwa game da ƙalubalen da Hausawa mazauna Jihar Ribas ke fuskanta na rusa harkokinsu na kasuwanci da ƙuntata wa rayuwarsu da suke zargin Gwamnan jihar Nyeson Wike da sa hannun a ciki. A cikin saƙon da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Abba Sani Pantami ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta koka da irin ƙuntatawar da ta ce Gwamnan Jihar na yi wa ‘yan Arewa mazauna jihar, musamman biyo bayan rushe kasuwar da ‘yan Arewan suke harkokinsu fiye da shekaru…
Read More
Shafukan Facebook, WhatsApp da Instagram sun yi kusufi na tsawon awanni

Shafukan Facebook, WhatsApp da Instagram sun yi kusufi na tsawon awanni

Daga AMINA YUSUF ALI A yammacin ranar Litinin ɗin da ta gabata ne, al'ummar Najeriya da wasu wuraren suka tsinci kansu a halin ɗaukewar shafukan fesbuk da wasaf da instagiram ɗif! Har na tsawon awanni. Al'amarin ya faru ne tun daga ƙarfe biyar na yammacin ranar Litinin din. Inda al'umma suka kasa sarrafa shafukan a tsakanin waɗancan lokutan. Bincike ya nuna cewa, wannan al'amari da ya faru, ya jawo wa mawallafin shafukan, Mark Zuckerberg ya tafka mummunar asara har ta Dalar Amurka Biliyan Bakwai. Wannan asara da shi Zuckerberg ya tafka, ta komar da shi baya a matsayinsa na ɗaya…
Read More
Likitoci sun tsagaita yajin aiki don lura da gudun ruwan gwamnati

Likitoci sun tsagaita yajin aiki don lura da gudun ruwan gwamnati

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar likitoci da aka fi sani da NARD a taƙaice, ta tsagaita yajin aikin gama garin da take yi na tsawon makonni shida domin bai wa Gwamnatin Tarayya damar biya mata buƙatunta. A jiya Litinin NARD ta ba da sanarwar tsagaita yajin aikin da ta shafe kwanaki 64 ta na yi, kamar yadda shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr Godiya Ishaya, ya bayyana a tattaunawar da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya yi da shi a Abuja. Ishaya ya ce ƙungiyar ta ɗauki matakin tsaigaita yajin aikin ne duba da ƙoƙarin da ta ga gwamnati na yi…
Read More