05
Oct
Daga BASHIR ISAH Gobe Laraba ake sa ran gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Nasarawa inda jama'a za su fito su zaɓi ciyamomi da kansilolin da za su ci gaba da jan ragamar ƙananan hukumomin nan da shekaru uku masu zuwa. Kafin wannan lokaci an ga 'yan takara daga jam'iyyu daban-daban sun ba da himma wajen yaƙin neman ƙuri'un jama'a yayin zaɓen na gobe. Ana sa ran gudanar da zaɓen ne a baki ɗayan ƙananan hukumomi 13 da ake da su a faɗin jihar. Gwamna Abdullahi Sule Da yake bayani a wajen wani taronsu na siyasa kwanan nan a…
